Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza da kuma Aisha Shariff Baffa

  1. Kadarar da na mallaka tun kafin na hau mulki ita ce har yanzu - Buhari

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kadarar da ya mallaka tun kafin ya hau mulki ba ta ƙaru ba har bayan saukarsa daga mulki a watan Mayun 2023.

    Cikin wata sanarwa da kakakin tsohon shugaban, Mallam Garba Shehu ya fitar ya ce Buhari ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da gwamnonin APC da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Kaduna.

    Tsohon shugaban ya shawarci gwamnonin na APC su rungumi aniyar hidimta wa al'umma, yana mai cewa shugabanci cike yake da tarin ƙalubale da kuma dama, kuma haɗa abubuwan biyu ne zai ciyar da ƙasa gaba.

    Haka Muhammadu Buhari ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan gwamnonin na APC da irin nasarar da ya ce an samu samu a jihohinsu.

    Tsohon shugaban ya kuma gode wa gwamnatin Tinubu saboda gyara masa gidansa na Kaduna.

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce ƙungiyar tasu ta kai wa tsohon shugaban ziyarar barka da sallah, tare da bayyana godiyarsu da girmamawa ga tsohon shugaban kan gudunmowar da ya bayar ga dimokradiyya.

    Tsohon shugaban ya gode wa gwamnonin kan ziyarar, yana mai cewa yayin da ya yi aiki da wasu wasun kuma sabbi ne a gare shi.

  2. Kotun Duniya za ta saurari ƙarar Sudan kan zargin UAE a kisan kiyashin ƙasar

    A yau Alhamis ne Kotun Duniya ta ICJ za ta saurari ƙarar da Sudan ta shigar kan zargin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da hannu a kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar Masalit na yammacin Darfur.

    A ƙarar an zargin dakarun RSF da aikata laifuka da suka shafi kisa da fyaɗe da tilasta wa fararen hula gudun hijira.

    Gwamnatin Khartoum ta ce an aikata laifukan ne saboda taimakon UAE na makamai da kuma ɗaukar sojojin haya.

    Hadaddiyar Daular Larabawa dai ta sha yin watsi da zargin.

    Tun ɓarkewar yaƙin basasa a watan Afrilun 2023, dakarun RSF da sojojin Sudan ke zargin juna da aikata ta'asa.

  3. Cinikayya tsakanin Amurka da China za ta ragu saboda munin dangantaka - WTO

    Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya WTO ta yi hasashen cewa cinikayya tsakanin Amurka da China za ta ragu da kashi 80 sakamakon taɓarɓarewar danganta tsakaninsu.

    WTO ta ce hakan zai kai ga hasarar dala biliyan 400 na cinikayya bisa la'akari da alƙalumman shekarar da ta gabata.

    Ƙungiyar ta ce barazanar da ƙasashen ke yi wa juna - babbar barazana ce ga tattalin arzikin duniya - kuma ƙasashe matalauta ne za su fi shan wahala.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Barkanmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci da za mu kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Abdullahi Bello Diginza ke zai ja ragamar shafin a daidai wannan lokaci bisa kulawar Usman Minjibir.