Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/04/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza da kuma Aisha Shariff Baffa

  1. Harajin Trump ba zai sa mu mika wuya ba - China

    China ta dage cewa ba za ta mika wuya ba, duk da matsin da take fuskanta daga shugaba Trump na lafta mata haraji, amma ta ce idan an nemi ayi sulhu a shirye take.

    Ma'aikatar kasuwancin kasar ta ce kofar tattaunawa a buɗe take.

    Rahotanni sun ce dama sun jima cikin shiri, sannin cewa irin wannan yanayi zai taso, kuma suna ganin Amurka ita tafi bukatar China.

    Akwai rahotanni da ke cewa manyan masana tattalin arziki a jam'iyyar kasar ta kwaminisanci na tattauna hanyoyin taimakawa 'yan kasar a wannan gaba da ake ciki na yakin kasuwanci.

    Amurka ta lafta harajin kashi 125 kan kayayyakin China.

    Yayin da ita kuma China ta mayar da martani da harajin kashi 84 kan kayayyakin Amurka.

  2. Gwamnatin Kano ta miƙa wa Edo bayanan mafarautan da aka kashe

    Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kammala tattara bayanan iyalan mutanen da aka kashe a Uromi da ke jihar Edo inda ta mika wa gwamnatin Edon sunayensu.

    Tun da farko gwamnatin jihar ta Kano ta kafa kwamiti da zai gudanar da bincike tare da tattara bayanan iyalan mafarautan da aka kashe.

    Mataimakin gwamnan jihar ta Kano ne ya jagoranci wata tawaga da suka je Edon inda suka mika rahoton da ke kunshe da bayanan.

    Yayin mika rahoton, mataimakin gwamnan na Kano kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya fadawa gwamnan jihar Edo cewa," Dama can mai girma gwamna na Edo kun mana alkawarin cewa za a yi wa mutanen da aka kashen adalci kuma mun yarda a kan hakan shi ya sa muka tattara bayanan iyalansu.Muna so ayi komai a bayyane cikin adalci wajen tabbatar da cewa an hukunta dukkan wadanda ke da hannu a kisan da aka yi wa mafarautanmu."

    A nasa bangaren, gwamnan jihar ta Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Edo sun kafa kwamitin da zai binciko gaskiyar abin da ya faru a kan kisan da aka yi mafarauta a Uromi.

    Gwamnan na Edo ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu, bai ji dadin abin da ya faru ba a Uromi sannan kuma ya kuduri aniyar tabbatar da cewa jihar da ma kasa baki daya za su zamo wurare masu aminci da kowa zai iya rayuwa da ma gudanar da kasuwanci.

    Daga bisani gwamna Okpebholo da kuma tawagar Kano da ta je Edo sun ziyarci Uromi in da suka gana da al'ummar Hausawa da ke wajen.

  3. Gwamnatin Nijar ta rusa ƙungiyoyin ƙwadago

    Gwamnatin mulkin soji a jamhuriyar Nijar ta rusa ƙungiyoyin ƙwadago guda uku da ke wakiltar jami'an tsaro da suka haɗa da na ma’aikatan kwastam da na ma’aikatar kula da ruwa da gandun daji.

    Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar.

    Hukumomin sun ɗauki wannan mataki ne kamar yadda kundin tsarin mulkin na 26 ga watan Maris ɗin shekarar nan ya tanada.

  4. Ƴan China 155 na taimakon Rasha a yaƙinta da Ukraine - Zelensky

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce akwai aƙalla ƴan China guda 155 da suke taimakon Rasha a yaƙin da ake gwabzawa a ƙasarsa Ukraine.

    Zelensky ya yi wannan jawabin ne bayan ya sanar da kama wasu ƴan China guda biyu da suke fafata yaƙin a makon jiya - wanda shi ne karon farko da Ukraine ke tabbatar da zarginta na China na taimakon Rasha a yaƙin.

    Da yake zantawa da menama labarai a ranar Laraba, Zelensky ya yi ikirarin cewa akwai "wasu ƙarin" ƴan China ɗin da suke cikin yaƙin dumu-dumu.

    Sai dai gwamnatin China ta mayar da martani a wani saƙo da gwamnatin ya fitar cewa, "yana da kyau kowane ɓangare ya fahimci rawar da China ke takawa a yaƙin, sannan a guji yaɗa zargi mara tushe."

    "China ba ta da hannu ko kaɗan a yaƙin da ake yi a Ukraine. Mu masu neman sulhu ne da zaman lafiya," in ji kakakin ma'aikatar wajen China, Lin Jian.

  5. An bayyana jihohin da za a iya ambaliyar ruwa a Najeriya

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a fuskanci mamakon ruwan sama da zai haddasa ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma Abuja babban birnin tarayyar kasar a daminar bana ta 2025.

    Ministan albarkatun ruwa, Joseph Utsev, ne bayyana haka a ranar Alhamis a yayin gabatar da hasashen kan ambaliyar ruwa wanda hukumar da ke kula da rafuka ta kasar NIHSA ta yi.

    Jihohin da za su iya fuskantar ambaliyar ruwan sun hadar da Legas da Ogun da Abia da Ondo da Adamawa da Akwa Ibom da Anambra da Bauchi da Benue da Borno da Bayelsa da Cross-River.

    Sauran su ne Delta da Ebonyi da Edo da Gombe da Imo da Jigawa da Kebbi da Kogi da Kwara da Nasarawa da Neja da Osun da Oyo da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe da Zamfara da kuma birnin tarayya Abuja.

    Ministan ya ce wasu bangarori na yankin kudu maso kudancin kasar za su fuskanci ambaliya ta gabar tafkuna da rafuka.

    Jihohin sun hadar da Bayelsa da Cross-River da Delta da Rivers, yayin da Akwai-Ibom da kuma Edo za su kasance cikin mummunan hadarin ambaliyar ruwa.

    A cewar ministan, ambaliyar ruwa ita ce babbar masifar yanayin da ke daidaita mutane da albarkatun kasa a Najeriya sannan kuma sauyin yanayi ne ke kara hadarin afkuwa ambaliyar.

    Joseph Utsev, ya ce jihohin da suka hadar da Abia da Benue da Legas da Bayelsa da Rivers da kuma na daga cikin jihohin da ke cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwa.

  6. Adadin mutanen da aka kashe a watan Maris a Najeriya ya karu da kashi 28 - Beacon Consultancy

    Rahotanni a bangaren tsaro a Najeriya daga kamfanin Beacon Security na cewa mutum dubu daya da dari uku ne aka kashe a cikin hare-haren da su ka wakana cikin kasar a watan Maris .

    Wannan ya nuna cewa lamarin hare-hare a watan na Maris ya karu da kashi 28 cikin dari idan aka kwatanta da abin da ya faru a watan Fabrairu.

    Dakta Kabiru Adamu shi ne shugaban kamfanin Beacon Security mai gudanar da bincike kan lamarin tsaro a yankin Sahel da Sahara ya shaida wa BBC cewa a wurare biyu aka samu karin hare-haren da aka kashe mutane, wato akwai yankin arewa maso gabas inda kungiyoyin masu kaifin kishin Islama suka kai hare-hare ciki har da manya shida daya daga cikinsu wanda aka kai wa sansanin jami'an tsaro.

    Ya ce," Sai kuma yankin arewa maso yamma musamman jihohin Sokoto da Kebbi, inda 'yan kungiyar Lakurawa ke kai hare-hare, da kuma masu satar mutane da ke hari a jihar Katsina."

    Dakta Kabiru Adamu, ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta karfafa tsarin da ta ke bi tsakaninta da jihohi da kuma al'umma, domin matsalar tsaro karfin soja ba zai iya magance shi ba.

    " Dole sai gwamnatin tarayya ta hada kai da gwamnatocin jihohi da ma al'umma, da kuma inganta tsaron al'umma musamman a yankunan karkara."

  7. Ana hasashen farashin man fetur zai sauka a Najeriya

    A Najeriya, ana hasashen farashin man fetur a ƙasar zai sauka a kwanaki masu zuwa.

    Ana wannan hasashen ne sakamakon matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar sayar wa matatun man cikin gida da ɗanyen mai a kuɗin Naira.

    A watan Maris ɗin da ya gabata ne yarjejeniyar ta wata 6 ta ƙare, wanda hakan ya sa matatar mai ta Dangota dakatar da sayar da mai da naira, matakin da ya sa farashin mai a ƙasar ya tashi.

    Masana tattalin arziki da masu ruwa da tsaki a fanni man fetur na maraba da matakin na gwamnatin, kuma sun ce nan ba da jimawa ba za a soma ganin tasirinsa.

  8. MDD ta ce an fara kama wanzamai da matasan da ke askin zamani a Afghanistan

    Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce ma'aikatan hukumar Hisbah na ƙungiyar Taliban a Afghanistan na tsare wanzamai da matasan da ke askin da ta ce ya saɓa wa ƙa'ida da kuma tsawaita gemu.

    Kamen na zuwa ne bayan da a watan Agustan bara ma'aikatar ɗa'a da yaƙi da miyagun ɗabi'a ta aiwatar da dokokin da za su riƙa lura da yanayin askin matasa tare da haramta wa mata magana a bainar jama'a.

    Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce dokokin na haifar da mummunar makoma ga ƙasar.

    Sai dai tuni ƙungiyar Taliban ta yi watsi da sukar.

  9. Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu ya yi watsi da batun sauya shi

    Mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, kuma tsohon ɗan tawaye, Riek Machar, ya yi watsi da wani yunƙuri daga wani ɓangare na jam'iyyarsu ta adawa da suka nemi a maye gurbinsa.

    Yanzu haka dai Mista Machar yana fuskantar ɗaurin talala ne.

    Gwamnati ta zarge shi da mara baya ga mayaƙa da suka kai hare-hare kwana nan kan sojoji.

    Rikicin ya ɗaga hankula da haifar da fargabar sake tsunduma ƙasar cikin yaƙin basasa.

  10. Jari matasan Afirka suke bukata, ba kyautar kuɗin kashewa ba - Shugaban bankin Afirka

    Shugaban bankin raya yankin Afirka, Akinwumi Adesina ya ce matasan Afirka tallafin jari suke buƙata domin inganta harkokin kasuwancinsu, ba kyautar kuɗaɗe kamar naira dubu 10 ko dubu 50 ko makamancin haka ba.

    Adesina, wanda tsohon ministan noma ne a Najeriya, ya ce matasan Najeriya da wasu ƙasashen na Afirka guda 51 ba tallafin kuɗaɗen kashewa da sunan tallafi suke buƙata ba.

    Ya ce matasan suna buƙatar tallafi ne da za su yi amfani da shi domin inganta harkokinsu na kasuwanci, domin su samu arziki mai yalwa.

    "Yadda matasanmu suke ficewa suna tafiya ƙasashen waje babbar asara ce a gare mu," in ji Adesina a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Alhamis.

    "Matasa ba sa buƙatar a yi ta faɗi da baki cewa 'zan ba ku tallafi.' Suna da sana'o'i da harkokin da suka ƙware, kuma suna da ilimi da gogewa, babban burinsu shi ne yadda za su mayar da tunaninsu ya zama kasuwanci domin samar da kuɗi.

    "Don haka babban abin da suke buƙata a yanzu shi ne jari, ba wai shirye-shiryen tallafi ba."

    Ya ƙara da cewa akwai matasa sama da miliyan 465 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 35 a nahiyar, inda ya yi gargaɗin cewa kada shugabannin yankin su yi sakacin mayar da yawan matasa, wanda ya kamata ya zama kadara, ya koma tamkar baraza.

  11. Wakilan gwamnatin Kano sun tafi Edo kan kisan matafiya a Uromi

    Wakilan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashi jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo sun tafi jihar Edo domin faɗaɗe bincike tare da tattauna batun kisan matafiya ƴan arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar wadda ke kudancin Najeriya.

    Tawagar ta ƙunshi shi mataimakin gwamnan, da Sarkin Rano Ambasada Mohammad Isa Umar da kwamishinonin addini da na ƙananan hukumomi da na ayyuka na musamman da ta harkokin mata da shugaban ƙaramar hukumar Bunkure da sauransu, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar, Ibrahim Garba Shuaibu ya nuna a wata sanarwa da ya fitar.

    Da yake jawabi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano kafin tafiyarsu, Gwarzo ya ce za su tafi Edo ne domin su yi bincike, "ta hanyar tattaunawa domin gano haƙiƙanin yadda lamarin ya auku domin samar da matsaya mai inganci."

    Ya ce ba wai za su je bincike ba ne kawai, "zuwan zai taimaka wajen ƙara sulhunta tsakanin al'ummomi domin kare sake aukuwar lamarin."

    A baya dai gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya ziyarci Kano domin jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe a jiharsa, inda a lokacin ziyarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci a biya diyyar waɗanda aka kashe ɗin, sannan a yi holen waɗanda aka kama da zargin kisan.

  12. Gwamnati ta ci tarar kamfanonin wuta da ke tsawwala wa al'umma kuɗin wuta

    Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, NERC ta ci tarar kamfanonin rarraba wutar lantarki guda takwas saboda bijirewa tsarin farashin lantarki ga waɗanda ba su da mita a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2024.

    Kamfanonin da aka ci tarar sun haɗa da na Abuja da Eko da Enugu da Ikeja da Jos da Kaduna da Kano da Yola.

    An ci kamfanonin tarar sama da naira miliyan 6287, sannan ana so su rage farashin lantarkin ga kwastomomin da abin ya shafa zuwa 15 ga watan Mayun 2025.

    NERC ta ce wannan matakin da ta ɗauka yana cikin ƙudurinta ta tabbatar da ana bin doka da oda, tare da kare haƙƙin kwastomomi.

  13. Matatar Dangote ta rage farashin man fetur

    Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin litar man fetur da take sayar wa ƴan kasuwa masu gidajen mai zuwa naira 865 daga naira 880.

    Tashar Channels ce ta ruwaito hakan, inda ta ce wata majiya ce daga matatar ta tabbatar mata da rage farashin a ranar Alhamis.

    Ragin farashin ya zo ne bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin matatar Dangote da ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun a ranar Talata.

    Bayan taron ne gwamnatin Najeriya ta ce yarjejeniyar sayar wa Dangote ɗanyen mai da naira na nan, kuma za a cigaba da amfani da ita bayan a baya kamfanin NNPCL ya sanar da kawo ƙarshen yarjejeniyar.

    Da wannan matakin ne ake sa ran gidajen man fetur da suke da yarjejeniya da matatar Dangote irin su MRS da Ardova da Heyden da sauransu za su rage farashin litar man fetur ɗinsu.

  14. Ƴansandan Kenya sun tarwatsa masu zanga-zanga a wata makaranta

    Ƴansandan Kenya sun harba hayaƙi mai sa ƙwalla a lokacin wata zanga-zangar da ta ɓarke a wata makaranta a Nukuru, lokacin gabatar da wata dirama da jami'an gwamnatin ƙasar suka ɗauka a matsayin sukar gwamnati.

    Wani tsohon Sanata ne da aka kama ya rubuta diramar mai suna, Echoes Of War.

    An tsara diramar kan wata ƙirƙirariyar masarauta da matasanta suka yanke ƙauna da samun adalci daga shugabanninsu.

    Gwamnatin ƙasar ta musanta haramta wa makarantun mata shiga bukukuwan makarantu a Nukuru.

    Bayan hana mutane shiga inda ake diramar, taurarin da suka taka rawa a diramar sun karanta taken ƙasar kafin ficewa daga wurin.

  15. Gwamnan riƙo na Rivers na shan suka kan sauke shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi

    Gwamnan riƙo na jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya na shan suka bayan da ya kori shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 23 da kuma sauke shugaban hukumar zaɓen jihar.

    Ibas ya bayyana matakin ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibibia Worika ya fitar ranar Laraba.

    Sanarwar ta ce tuni aka maye gurbin shugabannin riƙon ƙananan hukumomin, yayin da Dakta Michael Odey ya maye gurbin Adolphus Enebeli a matsayin shugaban hukumar zaɓen jihar.

    Dakta Odey zai yi aiki da wasu mambobi shida ciki har da farfesoshi huɗu.

    Yayin da yake mayar da martani kan matakin tsohon mai taimaka wa gwamnan jihar da aka dakatar, Jerry Omatsogunwa, ya ce matakin bai dace ba.

    Haka shi ma shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Naija Delta, Amb Godknows Igali ya soki Mista Ibas kan matakin, yana mai cewa matakin rusa tsarin dimokraɗiyya ne a jihar.

  16. Rundunar sojin Isra'ila ta yi barazanar korar dakarun ƙasar da ba sa fifita yaƙar Hamas

    Babban hafsan sojin sama na Isra'ila, Manjo Janar Tomer Bar ya ce zai kori sojojinsa da ke cikin rundunar ko-ta-kwana da suka buƙaci a fifita karɓo Isra'ilawan da ake garkuwa da su maimakon yaƙar Hamas.

    Fiye da sojojin saman Isra'ila 1,000 da ke cikin dakarun ko-ta-kwana ciki har da waɗanda suka yi ritaya ne suka sanya hannu kan wata wasiƙa da ke kiran hakan.

    Rundunar sojin Isra'ilar ta ce ba za ta bari sojojin da ke rundunar ko-ta-kwana su riƙa shiga zanga-zangar siyasa ba.

    Wani tsohon babban hafsan sojin ƙasar na daga cikin wadanda suka sanya hannu a takardar.

  17. Peter Obi ya yi kira ga ƴan hamayya su riƙa magana kan halin da Najeriya ke ciki

    Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya yi kira ga ƴan hamayya su riƙa magana kan abin da ya kira shugabanci maras kyau da ƙasar ke fuskanta, yayin da ya ce ta kama hanyar durƙushewa.

    Yayin da yake jawabi a taron kwamitin zartaswa na jam'iyyar a Abuja ranar Laraba, Mista Obi ya koka kan yawan talaucin da halin matsi da ake fama da shi a ƙasar.

    Ya ce abubuwa na ƙara lalacewa a ƙasar, kuma lokaci ya yi da za a haɗa kai wajen yin abin da ya dace, farawa daga jam'iyyarsa ta LP.

    “Dole mu yi magana idan abubuwa suka lalace, Najeriya na kan hanyar durƙushewa, alƙaluma a bayyane suke, mutane da yawa na ƙara talaucewa, mutanen da a baya ke cin abinci mai kyau, yanzu sun koma mabarata...''.

    “A baya idan na zo nan, mutane kan riƙa tambayata abin da nake son ci ko sha domin su kawo min, amma yanzu babu wanda yake tambayata, wannan na nuna halin talaucin da ƙasar nan ke ciki, don haka ya kamata mu tashi tsaye mu hada kai don yin gyara,'' in ji Mista Obi.

  18. Yaya girman kasuwancin da ke tsakanin Amurka da China?

    Darajar kasuwancin kayyakin da ke tsakanin manyan ƙasashen biyu ya kai kusan dala biliyan 585 a shekarar da ta gabata.

    A yanzu haka Amurka na fuskantar giɓin China, a shekarar da ta gabata, Amurka ta shigar da kayyakin China da suka kai na dala biliyan 440, yayin da China ta shigar da kayan Amurka da suka kai na dala biliyan 145.

    A wa'adinsa na farko a matsayin shugaban ƙasa, Trump ya ƙaƙaba haraji kan China, yayin da Joe Biden ya ƙara shi.

    Lamarin da ya sa kayayyakin da China ke shigarwa Amurka ya ragu daga kashi 21 a 2016 zuwa 13 a shekarar da ta gabata.

    Hakan na nufin dogara da kayan China da Amurka ke yi ya ragu cikin shekara 10, wani abu da masana suka ce China na karkatar da akalarta zuwa ƙasashen kudu maso gabashin Asiya.

  19. Rasha da Amurka sun sake musayar fursunoni tsakaninsu

    Rasha da Amurka sun sake gudanar da musayar fursunonin tsakanin ƙasashen biyu.

    Rasha ta saki Ksenia Karelina --Ba'amurkiya ƴar asalin Rasha, ƴar rawa - wadda wata kotun Moscow ta ɗaure saboda bayar da tallafi ga wata gidauniyar Ukraine.

    Yayin da ita kuma Amurka ta saki Arthur Petrov, ɗan Rasha asalin Jamus.

    Ko a watannin da suka gabata ma ƙasashen biyu sun gudanar da musayar fursunoni tsakaninsu.

  20. Kasuwannin hannayen jari sun soma farfaɗowa a Asiya bayan Trump ya dakatar da haraji

    Kasuwannin hada-hadar hannayen jari na yankin Asiya sun ɗan farfaɗo bayan farfaɗowar da aka samu a kasuwannin Amurka.

    Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Trump ya sanar da dakatar da harajinsa mai tsanani ga wasu ƙasashen da dama da ke cinikayya da Amurka har tsawon wata uku.

    Kasuwar hannun jarin Japan ta farfao da sama da kashi takwas, bayan kwanaki tana faɗuwa.

    Haka ma kasuwar Taiwan ta farfaɗo da kashi 10.