Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Shugabannin Turai za su taru kan yaƙin Ukraine

    A yau Litinin shugabannin kasasshn Turai za su taru a birnin Paris na Faransa domin tattauna yakin Ukraine a matsayin martani ga shirin Shugaba Donald Trump na tattaunawa kai-tsaye da Rasha da nufin kawo karshen yakin.

    Rahoton rashin gayyatar kasahsen Turai ko Ukraine kan a tattaunawar da za a yi a cikin makon nan a kasar Saudiyya ya jefa Turai cikin mamaki da bacin rai.

    Wakilin BBC ya ce jami'ai a Faransa na son mayar da wannan taron gaggawar tamkar wanda aka saba yin sa,

    Sannan taron wata dama ce ga shugabannin Turai domin tattaunawa da daukar matakin bai-daya wajen yin martani ga Mista Trump kan batun Rasha da Ukraine.

  2. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Litinin.

    Ni ne Umar Mikail zan jagoranci kawo rahotonnin bisa kulawar Usman Minjibir.

    Ku biyo mu.