Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Gwamna jihar Katsina ya raba wa mata awaki domin yaƙi da talauci

    Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa mata 3,610 da ke gundumomi 361 tallafin awaki wanda ya laƙume kuɗi naira biliyan 5.4 a matsayin tallafi.

    Gwamnan Jihar Dikko Radda ya faɗi hakan ne a yayin da ya ke rabon awakin karkashin shirin kiwon awaki da aka ƙaddamar a garin Dan-Nakolo da ke karamar hukumar Daura.

    Ya ce shirin wani babban mataki ne na cimma burinsu na ganin jihar Katsina ta zama kan gaba wajen yin kiwo a arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.

    Gwamnan jihar ya kuma ce karkashin shirin za a horar da matan kan matakan kiwo da suka dace da su, kamar abincin da ya kamata su ci, kula da lafiyarsu, da ma dabarun noma.

    ''Akalla awaki 40,000 aka ware domin rabawa waɗanda za su ci gajiyar shirin daga matakan gunduma inda duk gunduma aka zabo mata goma da babban manomi ɗaya, kuma duk mace daya za a ba ta awaki huɗu babban manomin kuwa awaki 50.''

    Ya kuma ce a wannan shekarar za a kafa gonar kiwon awaki a karamar hukumar Rimi domin inganta kiwo, samun madara da kuma taki, kuma zai kasance cibiyar horaswa.

  2. Atiku ya soki 'samamen' da jam'ian tsaro suka kai majalisar dokokin Jihar Legas

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yi tir da kutsen da jami'an tsaro suka yi wa majalisar dokokin jihar Legas.

    A shafinsa na X, Atiku ya bayyana alamarin a matsayin abin ƙi, ya kuma ce wajibi ne a gudanar da cikakken bincike.

    A cewar sa, ''abin takaici ne jami'an tsaron suka kai samamen da niyyar tilasta sauya shugabancin majalisar.''

    Ya ce zargin gayyatar jami'an tsaron wajen sasanta rikicin majalisa lamari ne da bai kamata a lamunta ba kuma a yi bincike kansa da gaggawa inda ya ce hakan wani mataki ne na cutar da dimokraɗiyya.

    Atiku ya kuma yi kira ga shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan fito da Najeriya daga matsalar da ya jefa ta maimakon ya rika katsalandan cikin alamuran jihohi.

    A yau Litinin ne aka wayi gari da wani sabon ruɗani a majalisar dokokin jihar ta Legas, lamarin da ya kai ga cewa jami'an tsaro sun yi wa harabar majalisar ƙwanya bayan raɗe-raɗin da ake yi kan cewa shugaban majalisar da aka tsige zai shiga majalisar a gobe Talata.

    Hakan na zuwa ne bayan matakin da ƴan majalisar suka ɗauka a kwanakin baya na tsige shugaban majalisar, Mudashiru Obasa, tare da zaɓen Mojisola Meranda a matsayin sabuwar shugabar Majalisar.

    Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jami'an tsaro suka toshe hanyar shiga harabar majalisar, inda ƴan majalisa suka yi cincirindo a wajen.

    Wannan ya tursasa wa ƴan majalisar yin zama a wani lambu da ke kusa.

  3. Shugaban Argentina na fuskantar barazanar tsigewa saboda kuɗin Kirifto

    Shugaban ƙasar Argentina, Javier Milei na fuskantar barazanar tsigewa da kuma gurfanar da shi a kotu bisa zargin shi da zamba da yaudara bayan ya tallata wani kuɗin kirifto a shafinsa na sada zumunta.

    Milei ya tallata kuɗin kirifto na $LIBRA a shafinsa na X a ranar Juma'a, wanda ya ce zai taimaka wa ƙananan ƴan kasuwa da masu tasowa samun kuɗaɗe.

    Ya kuma wallafa inda za a shiga a shafin intanet domin a sayi kuɗin wanda ya sa farashinsa ya tashi sosai.

    Sai dai bayan wasu sa'oi, ya goge rubutun da ya wallafa wanda ya sa kuɗin kirifton ya faɗi, wanda ya kai masu zuba jari sun tafka asara.

    Wasu abokan hamayya a majalisa sun ce su na shirin fara matakan tsige Milei. Hakazalika lauyoyi sun shigar da kara bisa zamba a kotun laifuka ta Argentina a ranar Lahadi.

    Sai dai ofishin shugaban ƙasa a ranar Asabar ya ce an goge rubutun a shafin shugaban ƙasar ne saboda kauce wa 'hasashe' sakamakon maganganun da alumma ke yi bayan ƙaddamar da kuɗin kirifton.

  4. An ƙaddamar da bincike kan zargin kashe mutum shida 'bisa kuskure' a Katsina

    Rundunar tsaron sojin saman Najeriya, ta ce za ta yi bincike kan zargin cewa jirgin yaƙin soji ya kashe mutum shida bisa 'kuskure' a lokacin da sojojin ke bin wani gungun ƴan bindiga a jihar Katsina.

    A cikin wata sanarwa da daraktan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na shelkwatar rundunar, Air Vice Marshal Olusola F Akinboyewa ya fitar, ya ce Rundunar ta yi matuƙar damuwa da rahotannin, kuma babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ya bayar da umurnin gudanar da cikkaken bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace.

    A ƙarshen mako ne rahotanni daga jihar Katsina, mai fama da matsalar ƴan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya, suka bayyana cewa wani jirgin sojin saman Najeriya ya kai hari kan fararen hula, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

    Sojojin Najeriya sun yi ƙaurin suna wajen kai harin kuskure kan fararen hula a ƴakin da suke yi da matsalar tsaro a yankunan Najeriya.

    Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar a yau Litinin, rundunar ta ce sojojin sama da ke aiki ƙarakshin dakarun Fansar Yamma sun yi nasara a harin da suka kai a tsaunin Yauni a gundumar Zakka da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina inda suka yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama kuma suka taimaka wajen daƙile harin da aka kai wa ƴansanda da kuma ƴan sinitirin jihar Katsina.

    Ya kuma ce sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai da ke nuna cewa an kai wa yankin da ƴansandan suke hari inda aka kashe jami'ai biyu da ƴan sintiri huɗu, kuma an samu tabbacin cewa ƴan bindigar na boye a tsaunin Yauni da ke kusa da yankin kafin kai harin.

  5. An mayar da Jagoran adawa na Uganda gidan yari daga asibiti

    An mayar da Jagoran adawa a Uganda, Kizza Besigye gidan yari bayan kwanciyarsa a asibiti sakamakon kamuwa da cuta bayan yajin cin abinci.

    Dr Besigye, wanda ya jima ya na adawa da shugaba Yoweri Museveni, na tsare a gidan yarin birnin Kampala tun watan Nuwamban bara bayan zargin sato shi daga Kenya da tilasta masa komawa Uganda don ya fuskanci hukunci.

    Shugabannin adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙkin bil'adam sun nemi a sake shi saboda rashin lafiya bayan bayyanarsa a kotu cikin mawuyacin hali.

  6. Mutane 50 sun mutu bayan shan barasa a Turkiyya

    Aƙalla mutane 50 sun mutu yayin da wasu 40 ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali bayan shan barasa da aka haramta haɗawa da sayarwa a Ankara, babban birnin Turkiyya.

    Hukumomi sun ce fiye da mutane 120 sun mutu a birnin Ankara da Istanbul a wannan shekarar sakamakon shan barasa mai guba.

    Ana samun ƙaruwar irin waɗannan mace-macen a Turkiyya saboda samun karuwar haɗa haramtacciyar barasar a ɓoye.

    Haraje-haraje sun ƙaru sosai a ƙarƙashin shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ake ganin hakan ya bunƙasa kasuwar haranmtaciyyar barasar.

  7. Rasha na ƙokarin maido da cikakkiyar hulda da Amurka

    Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya ce Rasha na taɓo batun yiwuwar maido da cikakkiyar hulɗa da Amurka a wata tattaunawa da za a fara a Saudiyya ranar Talata.

    Mista Peskov ya ce ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov tare da wani mataimakin shugaban kasar na kan hanyarsu ta zuwa Saudiyya.

    Ya ce za su tattauna batun yakin Ukraine tare da shirya yadda za a shige gaba tsakanin shugaba Putin da Trump.

    Sergei Lavrov ya kuma ce a tattaunawar shugaba Putin da Trump ta wayar tarho, sun amince su za su yi watsi da bambancin da ke tsakanisu, sun kuma amince a koma teburin sulhu.

    Ƙasashen Yamma sun yiwa Rasha dabaibayi da takunkumin tattalin arziƙi sakamakon mamayar da ta yi a Ukraine.

  8. An kwantar da Fafaroma a asibiti

    Likitocin da ke kula da lafiyar Fafaroma Francis wanda ke fama da cutar numfashi zasu sauya masa magani saboda abin da fadar Vatican ta bayyana a matsayin "yanayi mai wahala na asibiti".

    An kwantar da Fafaroma mai shekaru tamanin da takwas a asibiti kwanaki huɗu da suka gabata.

    Fadar Vatican ta ce zai ci gaba da zama a asibitin don kulawa da lafiyarsa.

    Wani mai magana da yawun Vatican ya bayyana cewar nan gaba kaɗan a yau za a fitar da ƙarin bayani game da yanayin da Francis ke ciki.

  9. Jami'an tsaro sun auka wa majalisar dokokin jihar Legas

    Rikicin shugabanci a majalisar dokokin jihar Legas da ke kudancin Najeriya ya ɗauki sabon salo, inda yanzu haka jami’an tsaro suka mamaye harabar ginin ‘yanmajalisar na tsaka da yin zama a yau Litinin.

    Lamarin shi ne na baya-bayan nan a rikicin da ya dabaibaye majalisar tun bayan tsige Mudashiru Obasa a matsayin kakaki.

    Kawo yanzu dai tsohon kakakin majalisar na ikirari cewa shi ne halastaccen kakakin majalisar bayan tsige shi, duk da maye gurbinsa da Meranda Mojisola.

    Rahotonni sun nuna cewa jami'an tsaron sun rufe ofishin Meranda, da na mataimakinta.

    Kazalika, an shafe lokaci kafin fara zaman na yau.

  10. Tsaron nahiyar Turai na fuskantar sauyi - Von der Leyen

    Shugabar hukumar Tarayyar Turai ta ce tsaron nahiyar na fuskatar sauyi.

    Ursula von der Leyen ta ce za ta je birnin Paris don halartar muhimmin taro bayan damuwar da tattaunawar Donald Trump da Putin don kawo karshen yaki a Ukraine ta haifar.

    Miss von der Leyen ta nemi hadin kai tare da ɗaukar matakan tsaro.

    Shugabannin ƙasashen Yamma za su tattauna yadda za su mayar da martani game da matakin da Trump ya dauka kan Ukraine, abin da ya hada da jibge dakarun 'kasashen Turai idan bukatar hakan ta taso lokacin tattaunawar sulhu.

    Wakilin BBC ya ce Burtaniya a shirye take ta aike da dakaru, mun san Faransa ta jima tana batun, amma Jamus da wasu ƙsashen na bukatar a jawo hankalinsu.

  11. Birtaniya a shiye take ta tura dakaru Ukraine don kiyaye zaman lafiya - Starmer

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce ƙasarsa a shirye take domin aikawa da dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa Ukraine idan aka cim ma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ƙasar da Rasha.

    A yammacin yau Litinin firaministan zai gana da sauran shugabannin Turai, waɗanda ke fargabar an ware su a tattaunawar zaman lafiya tsakanin Rasha da Amurka.

    Shugaban Amurkar Donald Trump ya ce zai iya ganawa da Shugaban Rasha Vladmir Putin "nan gaba kaɗan".

    Ƙasashen Turan na yin ganawar gaggawar ne a birnin Paris na Faransa a matsayin martani ga ganawar da jami'an Rasha da Amurka za su yi a Saudiyya gobe Talata game da yaƙin na Ukraine.

  12. Amurka na shirin korar 'yan Najeriya 201 zuwa gida

    Hukumomi a Amurka sun rattaba sunayen 'yan Najeriya 201 da za su kora zuwa gida yayin da Shugaba Donald Trump ke ci gaba da aiwatar da shirin korar baƙin haure daga ƙasar.

    Daga cikin waɗanda aka tsara mayarwa gidan har da fursunoni, da waɗanda suka aikata laifuka, kamar yadda Ƙaramar Ministar Harkokin Waje ta Najeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana a shafinta na X.

    Ta ce ta bayyana wa jakadan Amurka Richard Mills Jr damuwar gwamnatin Najeriya game da mutanen lokacin da ya kai mata ziyara a Abuja.

    "Zuwa yanzu, an faɗa mana cewa akwai 'yan Najeriya kusan 201 a sansanonin jami'an shige da fice na Amurka, kuma an tantance 85 da za a dawo da su," in ji ta.

    "Wannan ba mazauna Amurka kawai ya shafa ba, har da 'yan'uwansu a Najeriya da suka dogara da su, da yaran da suke biya wa kuɗin makaranta.

    "A matsayinmu na ƙasa, muna so mu ji ko za a ba su isasshen lokaci wajen tattaro dukiyoyinsu. Ko kuma kawai zuba su za a yi a jirgi a dawo da su? Abin zai zama mai ɗimautarwa sosai musamman ga waɗanda ba su aikata wani laifi ba."

  13. 'Daular Larabawa za ta shiga tsakanin musayar fursunonin Rasha da Ukraine'

    Shugaban Ukraine Zelensky ya ce ya tattauna da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) game da shirinta na shiga tsakani a musayar fursunoni tsakanin Ukraine ɗin da Rasha.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Telegram, Zelensky ya ce: "Tawagar shiga tsakani ta UAE ta ceto rayukan mutane da dama. Muna murna da irin wannan haɗin gwiwar, kuma mun tattauna a yau kan yadda za mu ci gaba da hakan."

    Ya kuma ce ya saka hannu kan yarjejeniyar kasuwanci da Shugaban Ƙasa Mohamed bin Zayed Al Nahyan.

    UAE ta ce an yi musayar fursuna 2,883 cikin musaya 12 da aka gudanar tsakanin Ukraine da Rasha, wadda ta shiga tsakani zuwa yanzu.

  14. Labarai da dumi-dumi, Manyan jami'an Rasha na kan hanyar Saudiyya don haɗuwa da jami'an Amurka

    Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov, da mataimaki na musamman ga Shugaba Vladmir Putin, Yury Ushakov na kan hanyarsu ta zuwa Saudiyya domin ganawa da jami'an Amurka kan yaƙin Ukraine.

    Kafofin yaɗa labarai ta gwamnatin Rasha da dama sun ruwaito labarin.

    Tun da farko an bayar da rahoton cewa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ma na kan hanyar zuwa Riyadh babban birnin Saudiyya domin haɗuwa da jami'an gwamnatin Rasha don tattauna kawo ƙarshern yaƙinta da Ukraine.

    Sakataren Tsaron Amurka Mike Waltz, da Jakadan Amuerka a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff za su yi wa Rubio rakiy zuwa Saudiyya.

  15. Gwamnatin Najeriya za ta ɗauki ma'aikatan lafiya 28,000 aiki saboda janye tallafin USAID

    Ministan Lafiya na Najeriya Ali Pate ya ce gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara aiki da mutum 28,000, waɗanda a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Development (USAID).

    Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Juma'a, ministan ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.

    Bayan hawansa mulki ne Shugaban Amurka Donald Truymp ya umarci a dakatar da bayar da tallafi wajen samar da magunguna da ayyuka kamar na cutar HIV a ƙasashe masu tasowa har sai an kammala bincike kan lamarin.

    Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ba ta zuba kuɗaɗe masu yawa ba a ɓangaren lafiyar, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu "a shirye yake wajen sauya alƙiblar tsarin".

    Ya ƙara da cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeirya daga waje ake shiga da su ƙasar.

  16. Guguwa da ambaliya sun kashe aƙalla mutum tara a Amurka

    Aƙalla mutum tara ne suka mutu a ƙarshen mako sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da kuma guguwa da suka auka wa gabashin Amurka, inda suka ɗaiɗaita tituna da gidaje.

    Gwamnan jihar Kentucky Andy Beshear ya ce mutum takwas sun mutu a jiharsa kuma ya nuna cewa akwai yiwuwar adadin zai ƙaru.

    An ceto ɗaruruwan mutane ne da suka maƙale a wuraren da ruwa ya mamaye. wasu a cikin mota.

    A jihar Georgia ma, an samu mutum na tara da lamarin ya halaka bayan wata bishiya da iska ta tuge ta auka wa wani mutum yana tsaka da barci a kan gadonsa.

    Jihohin Kentucky, Georgia, Alabama, Mississippi, Tennessee, Virginia, West Virginia, North Carolina na cikin yanayin gargaɗi na guguwa a ƙarshen mako.

  17. Habasha ta kama mutane da dama kan zargin yunƙurin kashe shugabannin Afirka

    Jami'an tsaron Habasha sun ce sun kama sama da mutum 12 da ake zargi da tsara kai hari kan shugabanni da 'yanjaridar da ke halartar taron ƙungiyar hadin kan ƙasashen Afirka ta African Union a ƙasar.

    Gidan talabijin na Ethio Forum ya ruwaito cewa "ana yunƙurin kai wa wasu shugabannin Afirka hari domin kashe su a Addis Ababa, amma har an kai ƙara gaban kotu".

    Jerin sunayen da aka kai gaban kotun ya nuna mutum 15 da ake zargi, ciki har da wani jami'i a ɓangaren 'yan'adawar ƙasar da ake zargi da karɓar aiki daga wata ƙungiya mai suna Fano domin kashe mahalarta taron.

    "An kama mutanen da sunayensu ke sama ne a ranar 13 ga watan Fabraoiru yayin da suke yunƙurin kai harin ta'addanci yayin taron AU," kamar yadda takardun na 'yansanda suka bayyana.

  18. Jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa 'kuskure' a Katsina

    Rahotanni daga jihar Katsina na cewa jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa 'kuskure' a lokacin da sojojin ke bin wani gungun masu garkuwa da mutane.

    Mazauna ƙauyen Zakka a Katsina sun ce jirgin sojin sun jefa bama-bamai a kan rukunun bukkoki, abin da ya janyo sanadiyyar kisan mutum shida.

    Luguden wutar kamar yadda wani rahoto ya ce na zuwa ne bayan da wasu ƴanbindiga suka kai wa wani sansanin ƴansanda hari inda suka kashe jami'an guda biyu da ɗan sinitiri guda ɗaya.

    Sai dai ƙungiyar Amnestiy International ta nemi da a gudanar da bincike.

    Har kawo yanzu sojojin Najeriya ba su uffan ba dangane da harin na 'kuskure'.

    A baya dai sun sha bayyana cewa hare-hare irin waɗannan na kuskure ne kuma za a ɗauki matakan kawo ƙarshen abkuwar hakan a gaba.

    Wannan ne dai karo na 10 da ake samun irin waɗannan hare-hare na kuskure a shekaru biyu sannan na 11 a tsawon shekaru takwas.

    Ko a watan Janairun 2025 ma sai da aka samu irin wannan harin na kuskure a a jihar Zamfara inda fafaren hula 16 suka mutu.

    A watan Disamban 2024 ma an samu irin wannan hari a jihar Sokoto wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10.

  19. 'Yantakarar shugabancin Jamus sun tafka muhawara kan baƙin haure

    Hudu daga cikin 'yantakarar da ke sahun gaba a neman kujerar shugaban gwamnatin Jamus sun fafata a zazzafar muhawarar farko da aka yaɗa kai-tsaye a gidan talbijin.

    Musayar yawun ta fi karfi kan manufofinsu kan baƙin haure, da kuma tattalin arziki.

    Wakilin BBC ya ce muhawara ce mai zafi tsakanin 'yantakarar hudu, wadda ta fi tsanani tsakanin shugaba mai ci Olaf Sholz da babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar Conservetive.

    A karon farko, an samu 'yartakara ta jam'iyyar AfD mai sassaucin ra'ayi Alice Weidel, wadda ta sha suka kan kin goyon bayan Ukraine kan mamayar da Rasha ta yi mata a 2022.

  20. 'Yansandan Najeriya sun ce sun kashe 'yan ESN biyar a jihar Imo

    Rundunar 'yansandan Najeriya ta ce gamayyar jami'an tsaron ƙasar ta kashe mambobin ƙungiyar Eastern Security Network (ESN) biyar a jihar Imo da ke kudancin ƙasar.

    ESN ɓangaren soji ne na ƙungiyar 'yan'aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) da gwamnatin Najeriya ta haramta, wadda ke neman kafa ƙasar Biafra a kudu maso gabashin ƙasar.

    Mai magana da yawun rundunar, Muyiwa Adejobi, ya faɗa ranar Lahadi cikin wata sanarwa cewa dakarun sun kashe jagororin mayaƙan biyu yayin wani samame a ranar 8 ga watan Fabarairu nan.

    Sai kuma a ranar 9 ga watan dakaru suka tare wani rukunin mayaƙan dajin Nkwukwo da ke ƙaramar hukumar Mbaitoli, inda suka sake kashe wasu shugabannin uku yayin musayar wuta, a cewarsa.

    Mista Adejobi ya ƙara da cewa jami'ansu sun ƙwace bindiga ƙirar AK-47 bakwai daga hannun 'yan ƙungiyar, da bindiga harba-ruga 13, da ɗaruruwan harsasai iri-iri