Wani
rahoton asusun kula da kananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya
bayyana cewa kashi 16 ne kaɗai cikin yara ke zuwa makaranta a jihar Jigawa.
Gwamnatin
jihar da ɓangaren majalisa da kuma UNICEF sun amince da wani tsari da zai
taimaka wajen tabbatar da cewa yaran da suka isa zuwa makarantar firamare da
sakandare sun shiga.
Matsalar
rashin zuwa makaranta wani al’amari ne da ke ci wa al’ummomin nahiyar Afrika
ciki har da Najeriya tuwo a kwarya, duk kuwa da irin hobɓasa da gwamnatoci a
matakai daban-daban ke cewa suna yi wajen magance matsalar da ke yi wa yara
tarnakin zuwa makarantar.
Rahoton wanda aka fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa kashi 44 huɗu na yaran da suka isa zuwa makarantun firamare da kuma
kashi 52 na waɗanda suka isa zuwa
sakandire ne ba sa zuwa, inda wasu daga cikinsu ke gararamba da kuma tallace-tallace.
Dr Lawan Yunusa Danzomo, kwamishinan ma’aikatar ilimi a matakin farko na jihar, ya ce sun ɓullo da matakai daban-daban na magance matsalar.
"Mun ƙara sabunta makarantu a karkara. Muna tattara shugabanni don sanar da su muhimmancin ilimi a wjaen da yara ba sa zuwa makaranta. Muna kuma ci gaba da aikin gina ƙarin makarantu da gyara wasu da suka lalace," in ji Dr Lawan.
Dr. Danzomo ya kara da cewa sun lura akwai wasu matsaloli da suke hana yaran
zuwa makaranta ciki har wasu al’adu.
Ya ce cikin abubuwan da suka janyo wasu yaran ba sa zuwa makaranta sun haɗa da talauci da rashin wadata da zai sa wasu sai sun yi tallace-tallace domin samun na kai wa baka, da kuma matsin tattalin arziki da ƙasa ke ciki.
Gwamnati da tallafin asusun na UNICEF sun yi wa shugabannin jihar kaimi, inda
yayin wani zama da ɓangaren majalisa suka amince su rika tallafawa yara masa
galihu.
Kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Haruna Aliyu ya ce bayan ganawa da UNICEF, ya raba wa yara 8,000 littafai da kuma abin rubutu.
Gwamnatin jihar ta kafa hukumar kula da makarantun tsangaya, inda za a
tattaro yara al’majirai da marasa galihu a mayar da su makaranta su ci gaba da
karatu, sannan kuma an samar da wani tsari mai taken "mathers association" wanda
zai rika jawo hankalin iyaye mata su rika tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna zuwa
makarnta a kan lokaci.