Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaranmu na kai-tsaye na yau Asabar.
Sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya nuna mana.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 23/08/2025.
Umar Mikail
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaranmu na kai-tsaye na yau Asabar.
Sai kuma gobe Lahadi idan Allah ya nuna mana.

Asalin hoton, Reuters
Kafofin yaɗa labaran Falasɗinawa sun ruwaito cewa hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 19 a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke birnin Khan Younis, a kudancin Gaza.
An kuma ce akwai wani iyali da dukansu suka mutu lokacin da hari ya faɗa kan sansaninsu.
Har ila yau, an bayar da rahoton kai hare-hare a tsakiya da kuma arewacin Gaza - yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da farmakin da suke yi a birnin Gaza.
An ruwaito cewa wasu ƙarin Falasɗinawa takwas sun mutu a yankin sakamakon yunwa, ciki har da yara ƙanana biyu.
A ranar Juma'a, wata hukumar lura da abinci da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya, ta tabbatar da cewa fari ya samu gindin zama a birnin Gaza - kuma zai ci gaba da yaɗuwa a faɗin yankin ciki wata mai zuwa.

Asalin hoton, AFP
Ƴan tawayen M23 waɗanda ke iko a gabashin Kongo, sun zargi sojojin Kongo da haɗa kai da mayaƙan kabilar Hutu waɗanda ba sa ga maciji da juna.
Wani mai magana da yawun ƴan tawayen Delion Kimbulungu ya faɗa wa taron manema labarai a birnin Goma - wanda ke ikon M23 - cewa shugaba Felix Tshisekedi ya amince da samarwa mayaƙan na FDLR da ke arewacin Kivu makamai.
Kalaman na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Humans Right Watch ta wallafa wani rahoto inda take zargin M23 da kashe fararen hula 140 a yankin Rutshuru a watan Yuli.

Asalin hoton, PDP
Jam'iyyar PDP ta Najeriya ta ce babu gudu ba ja da baya kan shirye-shiryenta na gudanar da babban taronta wanda aka shirya yi a ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar nan ta 2025 a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.
PDP ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnoninta ta fitar bayan taron gwamnonin da aka yir a jihar Zamfara a ranar Asabar 23 ga Agusta.
Gwamnonin sun yi kira ga mambobin jam'iyyar da su jajirce domin tabbatar da yiwuwar babban taron, domin a cewarsu PDP ce kaɗai jam'iyyar da za ta iya mayar da Najeriya turba mai kyau.
"Muna kira ga mambobinmu da su dage wajen yaƙi da masu shirya mana tuggu da zagon ƙasa domin hana faruwar babban taronmu mai zuwa."
"Jam'iyyar ta yaba da ƙoƙarin jagororinta bisa jajircewar da suka nuna a lokacin da ake guguwar ficewa daga cikinta," in ji sanarwar wadda gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad ya sanya wa hannu, sannan ta ƙara da cewa tsaiko ne da ba zai dakushe karɓuwar jam'iyyar ba a wajen masu zaɓe.
Ƙungiyar ta kuma nanata ƙudurin da ta ce jam'iyyar na da shi na ceto ƴan Najeriya da ma ƙasar daga APC, "wadda matakanta suka jefa ƴan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa."

A duk lokacin da damuna ta fara zuwa nisa, manoma sukan shiga farin ciki tare da shig harkar noma gadan-gadan, inda har wasu ma'aikata suke ɗaukar hutu domin zuwa kula da gonakinsu.
Amma a wani lamari da Hausawa ke kira 'duniya juyi-juyi' a daidai lokacin da wasu suke murnar, wasu kuma fargaba suke shiga na abubuwan da za su fuskanta.
Daga cikin abubuwan da ake fargabar fuskanta akwai ambaliyar ruwan sama da kusan duk shekara ke zuwa ta ɗaiɗaita wasu garuruwa a Najeriya da ma wasu ƙasashen duniya.

Asalin hoton, Umar Dikko Radda
Gwamnatin jihar Katsina ta ce sojojin Najeriya sun kai samame, inda suka samu nasarar tarwatsa maɓoyar ɗanbindiga Babaro tare da ceto mutum 76 da aka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Nasir Mu'azu ya fitar, ya ce Babaro da yaransa ne suka kai hari a Gidan Mantau da ke ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Ya ce, "sojojin saman Najeriya ne suka kai harin ta sama a tsaunin Pauwa da ke ƙaramar hukumar Kankara, inda suka samu nasarar ceto mutum 76 ciki har da mata da ƙananan yara."
Kwamishinan ya ce tsaunin ne babban sansani kuma maɓoyar ɗanbindigar, inda ya ke shirya kai hare-hare zuwa garuruwa.
Sai dai kwamishinann ya ce an wani ƙaramin yaro ya rasu, sannan ya ƙara da cewa nasarar da suka samu na cikin yunƙurin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.
A ƙarshe ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewar da ya ce suna yi wajen gudanar da aiki ba tare da gajiyawa ba.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Wani ƙarin mutum ɗaya ya mutu a Portugal sakamakon ɓarkewar gobar daji a arewa da kuma tsakiyar ƙasar.
Mutumin na ƙoƙarin kashe gobara ne lokacin da ya gamu da ajalinsa.
Zuwa yanzu mutum huɗu ne suka mutu a lamarin.
Haka ma, wasu mutum huɗu sun mutu a wata gobarar a ƙasar Sifaniya - biyu daga ciki sun kasance jami'an ba da agajin gaggawa.
An fuskanci gobarar daji da dama a wasu sassan Turai a wannan shekara, inda lamarin ya fi shafar Girka da Faransa da kuma Balkans.

Asalin hoton, PDP
Gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun hallara a birnin Gusau na jihar Zamfara domin yin wani taron tattaunawa.
Suna gudanar da taron ne a matsayin sharar fage kafin taron kwamatin gudanarwa mai muhimmanci da za su yi ranar Litinin mai zuwa.
Ministan Abuja Nyesom Wike - wanda har yanzu yake iƙirarin zama ɗan jam'iyyar duk da kasancewarsa a gwamnatin APC mai mulki - ya soki taron da za a yi a jihar Oyo, inda ya ci alwashin hana gudanar da shi.
Gwamna Dauda Lawal ne ke karɓar baƙuncin gwamnonin tara daga sassan Najeriya a yau Asabar.

Asalin hoton, PDP

Asalin hoton, Nema
Hukumar bayar da agaji ta gaggawa a Najeriya Nema ta ce mutum huɗu ne ta tabbatar sun rasu sakamakon kifewar kwale-kwale da ta auku a jihar Sokoto a farkon makon nan.
Cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, Nema ta ce ta gano ƙarin gawar mutum ɗaya. Jimillar mutanen da aka ceto sun kai 41, a cear Nema.
Ta ƙara da cewa hakan ya sa ta kawo ƙarshen aikin neman waɗanda suka tsira da kuma neman gawarwaki, wanda ta gudanar tare da sauran hukumomin da lamarin ya shafa.
Ziyarar bincike da jami'an hukumar suka kai ranar Alhamis a ƙauyukan Takuske, Kwakwazu, Bari, da Gamiha - wuraren da fasinjojin suka fito - ta sa sun gano cewa akwai ƙarin mutum 16 da suka tsira daga hatsarin.
Hatsarinya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata bayan kwale-kwalen ya kife a madatsar ruwa ta Goronyo da ke garin Kojiyo.

Asalin hoton, Nema
Hukumar ba da agajin gaggawa a Najeriya, Nema, ta gargaɗi mazauna kusa da Kogin Neja da su tashi saboda ƙaruwar yawan ruwan kogin.
Shugabar hukumar, Zainab Umar, ta umarci ofisoshinta da ke kusa da kogin da su ɗaura ɗamarar wayar da kan mazauna jihohin Kebbi da Neja da Kwara, waɗanda ke maƙwabtaka da ƙasar Benin.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta nemi mazauna jihohin da su koma wurare masu tudu domin guje wa ambaliyar da ka antayowa.
Sai dai Nema ba ta faɗi wani takamaiman lokaci da take hasashen faruwar hakan ba.

Asalin hoton, EPA
Koriya ta Kudu ta tabbatar cewa ta yi harbin gargaɗi kan sojojin Koriya ta Arewa da suka tsallaka cikin iyakarta na ɗan lokaci.
Gidan talabijin na Arewa ya bayyana harbin da "tsokana da gangan" kuma gwamnatin ƙasar ta zargi Kudu da jawo "fitina".
A kwanan nan Arewa ta ɗan tsananta adawa, inda 'yar'uwar Shugaba Kim Jong Un ta ƙi amincewa da shirin sasanci da gwamnatin Kudu ta nema.
Lamarin ya faru ne yayin da Koriya ta Arewan take ta aikin toshe iyakarta da maƙociyar tata baki ɗaya.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani matashi mai suna Umar Adamu-Umar ɗauke da tabar wiwi mai nauyin 9kg da ta kai darajar naira miliyan 10.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Asabar ta ce dakarunta sun kama matashin mai shekara 27 a jihar Kano ranar 6 ga watan Agusta.
Ta ƙara da cewa na kama shi ne a kan babbar hanyar Kano zuwa Zariya yana shirin safarar ƙunshi 19 na tabar daga Legas zuwa Kano.
"Matashin ya amsa cewa yana safarar miyagun ƙwayoyin, kuma da ma hukumar ta kwana biyu tana saka masa ido," mai magana da yawun NDLEA Sadiq Muhammad-Maigatari.

Asalin hoton, EPA
Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp ya yi murabus daga gwamnatin riƙon ƙwarya saboda rashin ɗaukar ƙarin matakai kan Isra'ila game da hare-haren da take kaiwa a Gaza.
Mista Veldkamp ya faɗa wa manema labarai ranar Juma'a cewa yana so a ƙara matsa wa Isra'ila game da yaƙin da take yi a Zirin Gaza, da kuma faɗaɗa mamaye a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
"Na ga alamun majalisar ministoci na ƙin amincewa da ƙarin matakai," in ji shi.
A ranar 3 ga watan Yuni gwamnatin ƙasar ta rushe, inda aka kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da za ta ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kafa gwamnatin haɗaka.

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yanfashin daji bakwai a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar, kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.
Kwamashinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Nasir Mu’azu ya faɗa wa manema labarai ranar Juma'a cewa sojojin sun kuma yi nasarar ƙwace babura huɗu a ƙaramar hukumar Kankara.
Ya ƙara da cewa samamen da dakarun suka kai ya ɗauki sama da awa biyu a ranar Alhamis bayan samun bayanan sirri cewa maharan sun far wa ƙauyen Baba.
Sanarwar tasa na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wasu 'yanfashi sun kashe mutum kusan 30 a wani hari kan masallata, wanda yanzu rahotonni ke cewa mutanen da suka mutu sun kai kusan 50.

Asalin hoton, Nigerian Army
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe kwamandojin ƙungiyar Boko Haram biyu tare da mayaƙa 11 yayin wani artabu na tsawon awanni a jihar Borno.
Kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito kwamandan rundunar Operation Hadin Kai, Manjo Janar Abdulsallam Abubakar yana bayyana Abu Nazir da Abu Fatima a matsayin jagororin da suka yi nasarar kashewa.
Ya ce mayaƙan ne suka yi yunƙurin kai hari a yankuna biyu na Bitta da Wulgo da ke ƙaramar hukumar Gwoza ranar Juma'a, inda suka daƙile su kuma suka kashe 13 daga cikinsu.
Ya ƙara da cewa fafatawar da suka yi ta ɗauki tsawon awanni, tun daga ranar Alhamis da dare har zuwa safiyar Juma'a.
A cewarsa, daga cikin kayayyakin da suka ƙwace a hannun 'yanbindigar akwai babura shida, da bindigogi ƙirar AK-47 da yawa, da kuma ƙunshin harsasai.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyoyin agaji sun ce Falasɗinawan da ke fuskantar matsananciyar yunwa a birnin Gaza sun yi galabaitar da ba za su iya tsere wa lugudan wutar da Isra'ila ke yi a birnin ba.
Mai magana da yawun asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta ce ba su da karfin da za su iya matsawa daga inda suke duk da an umarce su su bar wuraren.
Wani rahoto da kungiyar IPC mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce mutum 500,000 na fama da yunwa matsananciya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da rahoton yana mai cewa karya ce tsagwaronta.
Barkanmu da hantsin Asabar.
Ku biyo mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.
Umar Mikal ne ke tare da ku har zuwa ƙarfe 4:00.