Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Nabeela Mukhtar da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. Kwalara ta kashe mutum 672 a Sudan

    Kwalara ta kashe aƙalla mutum 672 daga cikin 24,00 da suka kamu da cutar a Sudan.

    Wata jaridar birnin Paris, Sudan Tribune, ta ce an samu ɓarkewar kwalarar ne a jihohin Sennar da Gezira da kuma White Nile da ke tsakiyar ƙasar.

    Maikatar lafiyar Sudan ta sanar da halin da ake ciki game da yaduwar cutar ne mako guda bayan ta karɓi tallafin rigakafin cutar kwalarar miliyan 1.4.

    Jihohi 10 daga cikin 18 na ƙasar suna fama da yaɗuwar kwalara a ƙasar tun daga tsakiyar watan Agusta saboda mamakon ruwan sama da aka yi fama da shi.

    Yaƙin basasar Sudan ya shafi ma'aikatar lafiyar ƙasar, inda hukumar lafiya ta duniya ta ce aƙalla kashi 80 na asibitocin ƙasar sun samu matsala.

  2. Jagoran Azbinawan Nijar ya yi tir da ƙwace 'yancinsa na zama ɗan ƙasa

    Jagoran ƴan tawayen Azbinawa a Nijar kuma tsohon minista a gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, Rhissa Ag Boula, ya yi watsi da matakin da shugaban gwamnatin sojin ƙasar na ƙwace ƴancinsa na zama ɗan ƙasa tare da wasu mutum takwas.

    Ag Boula, wanda makusancin Bazoum ne ya bayyana a wani bidiyo, inda ya sha alwashin ci gaba da fafutukar mayar da Nijar bisa turbar dimokuradiyya.

    Kafar yaɗa labaran Faransa ta RFI ta ruwaito Ag Boula na cewa: "Kada ku wargaza ƙasarmu. A 1991 na ɗauki makamai na tsawon shekara shida domin yaƙi da tsare-tsaren gwamnatin wancan lokaci, amma ban taɓa yin iƙirari ko kiran a ɓalle daga Nijar ba. Ni ɗan Nijar ne kuma zan ci gaba da zama ɗan Nijar duk halin da aka shiga... Mu ƴan Nijar ne kuma babu wanda ya isa ya canza hakan.''

    Bayan juyin mulkin 2023 ne Ag Boula ya ƙaddamar da ƙungiyar Resistance Council of the Republic (CRR) mai rajin mayar da tsohon shugaban ƙasar kan mulki, wanda har yanzu yake tsare a hannun sojojin da ke mulkin ƙasar.

  3. APC ta gargaɗi Ndume kan sukar Tinubu

    Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shawarci tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan ƙasar, Sanata Ali Ndume kan ya riƙa gabatar da ƙorafin sa kai tsaye ga shugaba Bola Tinubu, a madadin fita fili yana sukar tsare-tsaren gwamnati.

    A wata hira da jaridar The PUNCH darakatan yaɗa labaran jam'iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim ya ce kowanne ɗan ƙasa yana da ƴancin bayyana ra'ayin sa a tsarin dimokuraɗiyya, amma akwai buƙatar manyan ƴan siyasa irin su Ndume su riƙa kiyaye irin bayanan da zasu yi a bainar jama'a.

    Sanata Ndume mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya bayyana a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa, inda ya buƙaci gwamnatin shugaba Tinubu ta ɗauki matakan kawo sauƙin halin matsi da ƴan Najeriya ke ciki, ya yi kiran a dakatar da ƙarin farashin mai a ƙasar.

    Sanata Ndume ya kuma fitar da wata sanarwa ga manema labarai domin jaddada matsayar sa a kan halin da ake ciki, inda ya yi iƙirarin cewa akwai wasu da ke tunzura gwamnati tana aiwatar da tsare-tsare masu tsauri.

    A watannin baya ma jam'iyyar APC ta nemi majalisar dattawa ta ladabtar da Sanata Ndume ta hanyar ƙwace mukamin sa na mai tsawatarwa saboda yadda ya ke fita kafafen yaɗa labarai yana sukar gwamnatin APC.

    Daga baya sanatan ya nemi afuwa kuma jam'iyyar ta yafe masa.

  4. Harin soji ya kashe mutane 23 a kasuwar Sudan

    Harin rundunar sojin Sudan ya kashe mutane aƙalla 23 da kuma raunata wasu fiye da 40 a kudancin birnin Khartoum.

    An kai harin ne a kan babban sansanin mayaƙan RSF a kudancin Khartoum, amma ya kuskure, inda ya faɗa a kan wata babbar kasuwa da ke kusa da gidajen mutane.

    Mutanen da hari ya ritsa da su sun haɗa da masy shaguna da kuma abokan cinikin su.

    Ƙiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya ce yaƙin da RSF ke yi da sojin Sudan a tsawon wata 18 ya yi sanadiyyar kisan mutane fiye da 150,000 da kuma raba wasu da dama.

    Rahotanni sun ce yawan waɗanda suka samu rauni ya zarce wanda asibitoci a yankin za su iya kula da su.

    Tun daga ranar Juma'a faɗa ya ƙazance tsakanin RSF da sojin Sudan, a yankin da mayaƙan na RSF suke da ƙarfin iko sosai.

  5. An kama wani mutum da bindiga a wajen yaƙin neman zaɓen Trump

    Ƴan sanda a jihar California ta Amurka sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi a cikin motarsa ​​kusa da wani gangamin Donald Trump.

    An bayar da belin mutumin wanda aka tsare a wani shingen binciken ƴansanda yankin Coachella.

    Shugaban ƴansanda yankin Chad Bianco ya ce a yayin gudanar da bincike, an gano sami fasfo da dama masu sunaye da daban daban da kuma lasisin tuƙi masu ɗauke da sunaye daban-daban.

    An dai kara tsaurara matakan tsaro a wuraren gangamin Mista Trump bayan an yi yunƙurin kashe shi har sau biyu a baya bayan nan.

  6. Rundunar sojin Isra'ila tana bincike kan harin da Hezbollah ta kai mata

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike kan yadda wani harin da ƙungiyar Hezbullah ta kai wani sansanin soji da ke arewacin ƙasar ya kashe sojoji huɗu tare da raunata wasu mutane 60.

    Yana daya daga cikin manyan hare-hare da aka kai Isra'ila tun ɓarkewar rikici tsakanin ɓangarorin biyu shekara guda da ta gabata.

    Hezbollah ta ce tana mayar da martani ne kan munanan hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon da kuma Beirut.

    A wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ta yi barazanar ci gaba da kai hare-hare matukar Isra'ila ta daina kai hare-hare a Lebanon ba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da dubu.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Litinin.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.