Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 7 zuwa 12 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Lahadi 7 zuwa 12 ga watan Satumbar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Watakila Osimhen ba zai buga wa Najeriya karawa da Afirka ta Kudu ba

    Super Eagles za ta fuskanci Afirka ta Kudu ba tare da Victor Osimhen ba a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya ranar Talata, saboda raunin da ya ji kamar yadda aka sanar ranar Litinin.

    Osimhen ya ji rauni ranar Asabar a lokacin da yake buga wa Najeriya karawar da ta doke Rwanda 1-0 a Uyo, yanzu ba zai samu buga fafatawar da za a yi a Blomfontein ba.

    Afirka ta Kudu tana jan ragama a rukuni na uku da tazarar maki shida tsakaninta da Najeriya, koda yake ana sa ran Fifa za ta rage maki uku daga na Afirka ta Kudu, saboda amfani da ɗan wasan da bai cika ka'ida ba.

    Duk wadda ta ja ragamar rukunin ita ce za ta wakilci Afirka daga taran da ake sa ran za su je gasar cin kofin duniya daga nahiyar da za a yi a 2026 a Amurka da Mexico da kuma Canada.

  2. Mbappe ya yi kan-kan-kan da Henry a cin ƙwallaye a Faransa

    Ƙyaftin ɗin tawagar Faransa, Kylian Mbappe ya yi kan-kan-kan da Thierry Henry a yawan ci wa kasar ƙwallaye yana da shekara 26.

    Mai taka leda a Real Madrid ya ci ƙwallo na 51, iri daya da yawan ta tsohon ɗan wasan Arsenal, bayan da ya zura na biyu a raga a karawar da suka doke Ukraine 2-0 ranar Asabar a wasan neman shiga gasar kofin duniya.

    Yanzu haka saura ƙwallo shida tsakanin Mbappe da tsohon ɗan wasan Chelsea da Arsenal, Olivier Giroud mai 57 a raga mai rike da tarihin yawan cin ƙwallaye a tawagar Faransa.

  3. Watakila Onana ya koma wasannin aro a Trabzonspor

    Golan Manchester United, Andre Onana na duba yiwuwar komawa buga wasannin aro a Trabzonspor ta Turkiya

    Tun farko ana ta alakanta Onana da Galatasaray, sai dai kuma ta dauki mai tsaron raga, Ugurcan Cakir.

    Cakir, wanda ya tsare ragar tawagar Turkiya a wasan neman shiga gasar kofin duniya da ta yi nasara a kan Georgia ranar Alhamis ya koma Galatasaray daga Trabzonspor ranar 2 ga watan Satumba kan fam miliyan 31.2.

    Ita dai Trabzonspor tana ganin Onana zai taka rawar gani a ƙungiyar.

    Kawo yanzu Onana yana tare da tawagar Kamaru, domin buga mata wasannin neman shiga gasar kofin duniya, kuma sai a ranar 2 ga watan Satumba za a rufe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a Turkiya.

    United za ta iya barin Onana ko Altay Bayindir ya motsa, bayan da ta ɗauki mai tsaron raga, Senne Lammens daga Royal Antwerp.

  4. Depay ya zama kan gaba a cin ƙwallaye a Netherlands

    Memphis Depay ya zama kan gaba a yawan cin ƙwallaye a tawagar Netherlands, bayan da ya ci Lithuania biyu a karawar da suka yi nasara 3-2 a wasan neman shiga gasar kofin duniya ranar Lahadi.

    Mai shekara 31, wanda ke taka leda a Corinthians ta Brazil shi ne ya fara cin ƙwallo kuma na 51 daga baya ya kara na biyu kuma na 52 jimilla.

    Tun farko Robin van Persie ne ke rike da tarihin a tawagar Netherlands mai 50 a raga a karawa 102 tsakanin 2005 zuwa 2017.

    Shi dai Depay ya taka leda a PSV da Manchester United da Lyon da Barcelona da kuma Atletico Madrid, sannan ya koma buga babbar gasar tamaula ta Brazil a bara.

    Ya fara buga wa Netherlands tamaula a 2013 a karawa da Turkiya, ya ci ƙwallon farko a wasa da Australia a gasar kofin duniya a 2014 da aka yi a Brazil

    Tawagar Netherland tana jan ragamar rukuni na bakwai da maki 10 daga karawa huɗu, bayan nasara da ta yi a Kaunas.

  5. Sakamakon mako na uku a gasar Premier ta Najeriya

    • Barau 1-1 Bendel Insurance
    • El Kanemi Warriors 0-0 Rivers United
    • Enugu Rangers International 2-0 Plateau United
    • Enyimba 0-0 Nasarawa United
    • Katsina United 1-0 Kano Pillars
    • Kwara United 2-0 Kun Khalifat
    • Niger Tornadoes 1-0 Bayelsa Utd
    • Remo Stars 1-0 Warri Wolves
    • Shooting Stars 1-1 Ikorodu City
    • Wikki Tourists 1-0 Abia Warriors
  6. Barau FC ta raba maki da Bendel Insurance a Kano

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC ta tashi 1-1 da Bendel Insurance a wasan mako na uku a gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata a jihar Kano, Najeriya.

    Bendel Insurance ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Alex Oweilayefa a minti na 10 da take tamaula.

    Daga baya ne Barau FC ta farke ta hannun Ibrahim Yahaya.

    Da wannan sakamakon Barau FC wadda ke buga babbar gasar tamaula ta Najeriya a karon farko tana da maki biyu a wasa uku, bayan 0-0 da Enyimba a makon farko da rashin nasara 2-0 a gidan Bayelsa United a mako na biyu.

    Kano Pillars, wadda itama daga jihar Kano take ta yi rashin nasara 1-0 a gidan Katsina United a dai wasan makon na uku a gasar Premier ta Najeriya ranar Lahadi.

    Pillars ta yi rashin nasara ta hannun Azeez Falolu saura minti huɗu lokaci ya cika.

    Kenan a karawa uku Pillars tana da maki ɗaya, bayan rashin nasara 1-0 a Abia fa yin 1-1 da Wikki Tourist ta garin Bauchi a Kano.

  7. PSG ta zargi Faransa kan raunin Dembele da Doue

    Paris St-Germain ta zargi tawagar Faransa da yin biris kan haɗarin dake tattare da Ousmane Dembele da Desire Doue da cewa za a iya kaucewa raunin da suka ji a wasan da suka doke Ukraine a neman shiga gasar kofin duniya.

    Dembele zai yi jinyar mako shida, shi kuwa Doue jinyar mako huɗu zai yi kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

    Ba za su samu buga wa ƙungiyar wasu mahimman wasanni ba, ciki har da karawar farko a cikin rukuni a Champions League, kofin da take rike da shi na farko a tarihi.

    PSG ta ce ta aike da wasika zuwa hukumar ƙwallon kafar kasar, inda ta sanar da yawan wasannin da ƴan ƙwallon suka buga da jan kunnen hukumar cewar za su iya cin karo da rauni, amma aka yi watsi da batun.

    Dembele ya canji Doue lokacin da ya ji rauni bayan hutu a wasan da suka ci 2-0 ranar Juma;a daga baya aka sauya shi a minti na 81 shima saboda raunin da ya ji.

    BBC ta tuntuɓi hukumar ƙwallon kafar Faransa da jin karin bayani.

    .

  8. US Open: Wa zai zama zakara tsakanin Sinner da Alcaraz?

    Carlos Alcaraz da Jannick Sinner za su buga wasan karshe a US Open ranar Lahadi.

    Tsakaninsu sun lashe Grand Slam bakwai, kuma karawar za ta yi zafi ganin ta hamayya ce kuma kowa na kan ganiya.

    Tun kafin wasan ana cewa karawa tsakaninsu biyu ta zama ta hamayya ta farko tun bayan tsakanin ta Djokovic da Federer da Nadal

    Sinner mai shekara 24 da Alcaraz mai shekara 22 da za su kara a wasan karshe a Grand Slam, kenan za su yi kokari cin babban kofin tennis na huɗu kuma karo na biyu a jere.

    A kakar nan Sinner ya kare kofinsa na Australian Open daga baya ya sha kashi a hannun Alcaraz a French Open.

    Sai dai kuma Sinner ya yi namijin kokari wajen karɓe Wimbledon Open a hannun Alcaraz.

    Wasan da za su kara a birnin New York din Amurka zai zama karon farko da ƴan wasa biyu suka hadu sau uku a Grand Slam a kaka ɗaya

  9. Ko Super Eagles za ta samu shiga kofin duniya 2026?

    Najeriya ta farfaɗo da damar samun tikitin shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2026, bayan da ta doke Rwanda 1-0 a Uyo ranar Asabar.

    Sabon ɗan wasan Wolverhampton, Tolu Arokodare ne ya ci ƙwallo a minti na shida da shiga zagaye na biyu a karawar.

    Da wannan sakamakon Super Eagles ta hau kan Rwanda ta koma ta uku a rukuni na uku da tazarar maki shida tsakani da wadda take ta ɗaya Afirka ta Kudu - wadda Najeriya za ta fuskanta a Bloemfoentein ranar Talata.

    Saura wasa uku-uku a kammala karawar cikin rukuni, kuma guda ɗaya ce za ta wakilci Afirka daga kowanne rukuni tara.

    Kenan ya zama wajibi Najeriya ta lashe wasan da za ta je Afirka ta Kudu, domin kada ta kasa zuwa gasar kofin duniya karo na biyu a jere, bayan da ba ta je wanda aka yi a Qatar ba.

    Wani fatan da Super Eagles take da shi, shi ne idan Fifa ta soke maki uku daga na Afirka ta Kudu, sakamakon amfani da ɗan wasan da bai cika ka'ida ba a karawar da ta yi da Lesotho a cikin watan Maris.

    Kawo yanzu hukumar ƙwallon kafa ta duniya Fifa, ba ta yanke hukunci ba kan lamarin.

    Idan kuma Najeriya ba ta samu doke Afirka ta Kudu ba, watakila ta kare a mataki na biyu idan ta ci sauran wasanninta - daga nan za a zaɓo waɗanda suka kare a mataki na biyu masu maki da yawa su huɗu domin karawa a tsakaninsu daga nan a fitar da ɗaya.

    Wannan ɗayar za a haɗa ta wasan cike gurbi da wata nahiyar da itama ta samu wannan damar.

  10. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.