Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 03/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Umar Mikail

  1. Adadin mutanen da ambaliya ta kashe a jihar Neja ya kai 230

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Neja sun ƙaru zuwa 230 yayin da har yanzu ake neman sama da mutum 400, a cewar Mataimakin shugban ƙaramar hukumar Mokwa, Musa Kimboku.

    A makon da ya gabata ne ambaliyar, wadda ruwan sama mai ƙarfin gaske ya haifar, ta ɗaiɗaita ɗaruruwan gidaje da mazauna cikinsu.

    Mataimakin shugban ƙaramar hukumar ya faɗa wa BBC cewa ana ci gaba da aikin tona ƙasa domin neman mutanen da ake tunanin ƙasa ta binne su.

    Ya ce hakan ya taimaka wajen rage warin da yake tashi a yankin saboda gawarwaki.

    Ana kallon ambaliyar a matsayin mafi muni cikin shekara 50 da aka taɓa gani a Najeriya, wadda ta zarta ta birnin Maiduguri a watan Satumban 2024.

  2. MDD ta caccaki Isra'ila kan raba kayan agaji a Gaza

    Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), Volker Turk, ya yi Allah wadai da ayyukan sabuwar ƙungiyar agajin da Amurka da Isra'ila ke tafiyar da harkokinta a kudancin Gaza.

    Ya ce akwai matuƙar takaici da sosa rai ganin yadda ƙungiyar ke cin zalin fararen hula.

    Mista Turk na waɗannan kalamai ne bayan harbe gwamman Falasdinawa a kusa da inda ƙungiyar ke rabon kayan tallafi a ranar Lahadi a Zirin Gaza.

    Shaidu da waɗanda suka tsira sun ce sojojin Isra'ila ne ke harbin su.

    Wakiliyar BBC ta ce Mista Turk ya kuma ce abubuwan da Isra'ila ke aikatawa kokari ne na ganin bayan al'ummar Falasdinawa.

    Kakakin hukumar asusun yara na MDD wato Unicef, Ricardo Pires, ya ce abubuwan da ake aikatawa sun yi matukar muni. Ya ce MDD na da dubban manyan motoci maƙare da kayan abinci da magunguna da ruwan sha, amma an hana su shiga Gaza.

  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na ranar Talata.

    Za mu kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman ma a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.