Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/11/2024

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Lucky Aiyedatiwa na APC na kan gaba a sakamakon zaɓen gwamnan Ondo

    Dan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa na gaba gaba a sakamakon da aka fitar kawo yanzu.

    Hukumar zaɓen ƙasar ta karɓi sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomi 15 cikin 18 na jihar, inda kuma a jam'iyyar APC ke kan gaba a duka ƙananan hukumomin da aka tattara, sai kuma PDP ke biye.

    Ɗan takarar na APC ya samu ƙuri'a 301,113, yayin da ɗan takarar PDP ya samu ƙuri'a 97,051.

  2. Sarauniyar kyau ta Najeriya ta zo ta biyu a gasar kyau ta duniya ta 2024

    Sarauniyar kyau ta Najeriya, Chidimma Adetshina ta ƙare a mataki na biyu a gasar sarauniyar kyau ta duniya ta 2024 da aka gudanar karo na 73.

    Wakiliyar ƙasar Denmark, Victoria Kjaer Theilvig ce ta zo ta farko a gasar da aka gudanar a birnin Mexico City na ƙasar Mexico.

    A cikin watan Agusta ne aka zaɓi Chidimma a matsayin sarauniyar kyau ta Najeriya, bayan ta fice daga takarar gasar a Afirka ta Kudu saboda matsalolin da suka taso kan asalinta.

    Mutum 125 ne suka shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya a bana, ciki har da wakilan ƙasashen Iran da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Somaliya da suka shiga gasar a karon farko.

    Bayan tankaɗe da rairaya an zaɓi 30, sannan aka sake rairayewa aka zaɓi 12, daga ciki kuma aka sake zaɓar biyar da suka fi yi zarra.

    Biyar ɗin farko sun haɗa da Denmark da Najeriya da Mexico da Thailand da kuma Venezuela.

  3. Trump ya naɗa sakataren kula da makamashi na Amurka

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya zaɓi wani jami'in kula da harkokin mai a matsayin sakataren kula da harkokin makamashi.

    Chris Wright shi ne Shugaban Kamfanin Liberty Energy, wanda, a baya, ya yi watsi da batun sauyin yanayi yana mai cewa makamashi mai gurɓata muhalli babban ci gaba a duniya.

    Naɗin nasa ya yi dai-dai da alƙawarin da Trump ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓensa, na goyon baya da kuma farfaɗo da masana'antar mai da iskar gas.

  4. Al'ummar Senegal na zaɓen 'yan majalisun dokokin ƙasar

    A yau Lahadi ne Senegal ke gudanar da zaɓen ƴan majalisun dkokokin ƙasar, wata takwas bayan zaɓar shugaban ƙasar da ya yi alƙawarin samar da manyan sauye-sauye.

    An rantsar da shugaba Basiru Diyomaye Faye a watan Maris, inda ya yi alƙawarin samar da sauye-sauye ga tattalin arziƙi da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

    Sai dai ƴan hamayyar ƙasar sun ce bai yi wani kataɓus ba wajen kawo ƙarshen rashin ayyukan yi da kuma dakatar da mutanen da ke sayar da rayukansu wajen ƙoƙarin tsallakawa ƙasashen Turai ta hanyar amfani da jiragen ruwa ba bisa ƙa'ida ba.

    Zaɓen 'yan majalisun ne zai zama zakaran gwajin dafi na farin jinin sabuwar gwamnatin, inda magoya bayanta ke cewa akwai buƙatar ta samu rinjaye a majalisar ƙasar kafin ta samu ta iya cika alƙawurran da ta yi wa ƴan ƙasar.

  5. Birtaniya za ta ninka tallafin da take bai wa Sudan

    Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta ninka talafin kuɗin da take bayarwa domin tallafa wa fararen hular da yaƙi ya rutsa da su a Sudan.

    Birtaniya ta ce za ta samar da sama da dala miliyan 140.

    Za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen samar da abinci da matsugunni da kuma ilimi ga mutane sama da miliyan guda - da ke cikin ƙasar da kuma waɗanda suka tsere zuwa ƙasashe makwabta.

    Shirin samar da abinci na duniya ya ce kusan rabin al'ummar Sudan na fama da matsananciyar yunwa.

    Yaƙin da aka kwashe wata 18 ana yi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF ya jefa ƙasar cikin mawuyacin hali.

  6. Aasslamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa kan labaran da muke wallafawa.