Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/11/2024

Wannan shafi ne da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Rufewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da maƙwabtanta da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Lahadi 17/11/2024

    A madadin kowa da kowa ni Muhammad Annur Muhammad nake fatan za ku kasance da mu gobe Litinin.

    Mu rufe da wannan karin maganar da ke cewa - Ɗaki ba ya tashi ragaya ta zauna

  2. Biden ya zama shugaban Amurka na farko mai ci da ya ziyarci dajin Amazon

    dajin Amazon

    Asalin hoton, Getty Images

    Joe Biden ya zama shugaban Amurka na farko da ke kan mulki da ya kai ziyara katafaren dajin Amazon.

    Mist Biden ya sauka a birnin Manaus na ƙasar Brazil, inda zai yayata abubuwan da ya cimma wajen yaƙi da sauyin yanayi sannan kuma zai gana da shugabannin yankin da ke iki domin kare dajin.

    Saɓanin hakan kuma ana sa ran shugaban Amurkar mai jiran-gado, Donald Trump, ya janye wasu dokoki na sauyin yanayi domin samar da kuɗi ga shirin rage haraji.

    Trump ya zaɓi ƙwararre kan mai da iskar gas domin ya jagoranci ma'aikatar makamashi a shekara mai zuwa .Saɓanin hakan kuma ana sa ran shugaban Amurkar mai jiran-gado, Donald Trump, ya janye wasu dokoki na sauyin yanayi domin samar da kuɗi ga shirin rage haraji.

    Trump ya zaɓi ƙwararre kan mai da iskar gas domin ya jagoranci ma'aikatar makamashi a shekara mai zuwa

  3. Ana ƙirga ƙuri'un zaɓen majalisar dokoki a Senegal

    Jami'an zaɓe a Senegal na aiki

    Asalin hoton, Muhamadou Bittaye/AFP via Getty Images

    Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u a Senegal bayan zaɓen majalisar dokoki da aka yi wanda shugaban ƙasar ya kira a ƙoƙari da yake yi na samun goyon baya a majalisar domin aiwatar da sauye-sauyensa masu tsauri.

    Bayan da ya ci zaɓen shugaban ƙasa a watan Maris, Bassirou Diomaye Faye, ya yi alƙawarin gudanar da sauye-sauye na tattalin arziƙi da tabbatar da adalci da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

    Bayan da ya naɗa maigidansa na siyasa, Ousmane Sonko a matsayin firaminista, shugaban ya kasance cikin matsin lamba saboda rashin aikin yi na matasa da ke ƙaruwa.

    Ana ganin babban kalubalensa a wannan zaɓe zai kasance ne daga tsohon shugaban ƙasar, Macky Sall, wanda a yanzu yake zaune a Moroko, kuma yana daga cikin haɗakar 'yan hamayya.

  4. Harin Isra'ila ya kashe aƙalla mutum arba'in da shida a Gaza - Jami'an lafiya

    Gine-gine a rushe da mutane da kallo

    Asalin hoton, ep

    Jami'an kiwon lafiya a Gaza sun ce harin baya-bayan nan da Isra'ila ta kai ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 46.

    Mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya Mahmud Bassal ya ce mummunan harin ya faru ne a wani gini mai hawa biyar da ke yankin Beit Lahiya a arewacin Gaza.

    Wakilin BBC ya ce wannan ya kasance ɗaya daga cikin hare-hare da ya kashe fararen hula mafi yawa cikin wata 13 uku da aka yi ana luguden wuta a zirin.

    A wasu hare-hare daban-daban da Isra'ila ta kai, an bayar da rahoton an kashe Falasɗinawa goma a sansanin ƴan gudun hijira na Bureij da ke tsakiyar Gaza, da kuma wasu biyar a birnin Khan Younis a kudancin ƙasar.

  5. Sama da mutum 30,000 aka yi wa magani a asibiti a Sudan

    Mutanen Sudan

    Asalin hoton, AP

    Jami’an kiwon lafiya a Sudan sun ce sama da mutum dubu talatin da uku suka sami kulawa a asibiti a birnin Khartoum tun bayan ɓarkewar yaƙin basasa a watan Afirilun bara.

    Shugaban kwamitin gaggawa na kiwon lafiya ya ce an yi wa mutane sama da dubu ashirin aikin tiyata kyauta domin cire harsasai daga sassan jikinsu.

    Yaƙin da ake gwabzawa tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun ƙungiyar RSF ya raba aƙalla mutane miliyan goma sha ɗaya da muhallansu a faɗin kasar Sudan.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane dubu dari uku da arba'in ne suka tsere daga gidajensu a cikin watan da ya gabata kaɗai.

  6. Shugaban gwamnatin Jamus ya kare tattaunawarsa da Putin

    Olaf Scholz da Vladimir Putin

    Asalin hoton, AP

    Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya kare tattaunawar da ya yi ta waya da Shugaban Rasha, Vladimir Putin a shekaran jiya Juma'a abin da Ukraine ta bayyana rashin jin daɗinta a kai.

    Yayin da yake bayani kan komawar Donald Trump fadar White House, Mista Scholz ya ce ba zai dace a ce Washington tana tuntuɓar Moscow akai-akai ba yayin da shugabannin ƙasashen Turai ke ƙaurace wa Rashar ba.

    Mista Scholz ya ce a nasa ra'ayin, bai kamata a ce a yi zaman tattaunawa tsakanin shugaban Amurka da na Rasha ba a nan gaba, ba tare da shugaban wata muhimmiyar ƙasa ta Turai ya yi tasa tattaunawar ba.

  7. APC za ta daɗe tana mulki a Najeriya - Ganduje

    Abdullahi Umar Ganduje

    Asalin hoton, DR

    Shugaban APC Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa yadda jam'iyyar ke ƙara farin jini da samun karɓuwa a Najeriya alama ce da ke nuna cewa za ta daɗe tana mulki a ƙasar.

    Hasashen na Ganduje na cikin wata sanarwa ne da babban sakataren yaɗa labaransa Edwin Olofu, ya fitar a yau Lahadi a Abuja, a kan sake zaɓen Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo da aka yi.

    Shugaban jam'iyyar ta APC na ƙasa ya ce sakamakon zaɓukan jihar Edo da kuma yanzu na Ondo, alama ce ta cewa 'yan Najeriya sun rungumi jam'iyyar mai mulki a ƙasar.

    A yau Lahadi ne hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC ta bayyana Gwamna, Lucky Aiyedatiwa na APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen da aka yi jiya Asabar, da ƙuri'a 366,781, inda zai ci gaba da wa'adinsa na biyu, bayan ya kada babban abokin hamayyarsa Agboola Ajayi na PDP wanda ya samu ƙuria'a 117,845.

    Jam'iyyar PDP ta soki sakamakon zaɓen na Ondo da cewa shi ne mafi muni da INEC ta taɓa yi - babban sakataren watsa labaranta Debo Ologunagba ya ce an yi amfani da kuɗi wajen sayen kuri'a fiye da hankali, baya ga tarin maguɗi.

  8. Yahudawa masu bin addinin gargajiya na zanga-zanga kan sa su aikin soji a Isra'ila

    Tarin Yahudawa 'yan gargajiya ɗauke da allunan zanga-zanga

    Asalin hoton, Reuters

    Yahudawa masu bin addininsu na gargajiya da ke zanga-zangar ƙin yarda da shirin gwamnatin Isra'ila na tilasta shigar da su aikin soja sun datse babban titin da ke kusa da birnin Tel Aviv.

    Matakin nasu ya biyo bayan umarnin da aka bayar a yau Lahadi na tura sababbin rukunin waɗanda za a sa aikin na soji maza daga cikin al'ummar Yahudawan na Haredi.

    A ka'ida ba a shigar da su aikin soji idan suna cikin karatun addini ka-in-da-na-in. To amma a wata Yuni yayin da rikicin Gza ya tsananta sai kotun ƙolin Isra'ila ta kawar da wanan doka.

    Yahudawan masu bin addinin gargajiya sun kafe cewa aikin soja na barazana ga harkokinsu na addini da wanzuwar al'ummarsu.

  9. Isra'ila ta kashe babban jami'in yaɗa labarai na Hezbollah - Rahoto

    Mohamad Afif

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotanni na cewa Isra'ila ta kashe babban jami'in yaɗa labarai na Hezbollah, Mohamad Afif, ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ƙalilan da suka rage, a wani hari ta sama a tsakiyar Beirut.

    An kai harin ne a kan hedikwatar wata jam'iyya da ke goyon bayan Syria a yankin birnin Ras al-Naba.

    A ranar Litinin da ta wuce ne aka yi wa Mohamad Afif ganin ƙarshe a wani taron manema labarai a wajen kudancin Beirut, inda ƙungiyar take.

    Haka kuma sojojin Isra'ilar sun kai hari kan wani wajen sojin Lebanon inda suka kashe soja ɗaya da raunata wasu uku a kudancin ƙasar.

    Isra'ila ta ce a cikin 'yan sa'o'in da sua gabata an harba mata makamai masu linzami wajen ashirin daga Lebanon, amma kuma ta ce ta tare yawancinsu.

  10. Najeriya da India sun jaddada aniyar tallafa wa juna ta fannonin tsaro da kasuwanci

    Firaminista Modi da Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Najeriya da India sun kara jaddada aniyar bunkasa kawance a tsakaninsu don karfafa alaka a fannoni da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro da harkar lafiya da samar da abinci.

    Wannan na kunshe ne a sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa da aka fitar a yau Lahadi a Abuja bayan kammala ziyarar da Firaministan Indiyar ya yi a Najeriya, wadda Shugaba Bola Tinubu ya gayyace shi.

    A lokacin tattaunawar, shugabannin biyu sun amince su hada kai wajen yaki da ta'addanci da tabbatar da tsaro a teku da kuma musayar bayanan tsaro na sirri.

    Firaminista Modi ya jaddada aniyar kasarsa ta taimaka wa shirin Najeriya na zamanantar da harkar tsaronta, inda ya nuna yadda kasarsa take abar amincewa a fannin kera makamai

    Shugabannin biyu sun kuma nuna yadda kyakkyawar alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da India, inda India take kasa mafi girma a alakara kasuwanci da Najeriya da kuma bayar da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin Najeriyar.

    Najeriya ta yaba da gudummawar kamfanonin Indiya sama da 200 da ke aiki a cikinta, inda suka samar a ayyuka masu yawa da kuma damarmaki na zuba jari.

    A fannin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari kuwa shugabannin biyu sun umarci jami'ansu da su kammala dukkanin yarjeniyoyin da ke tsakaninsu a wannan fanni.

    A bangaren samar da kayayyakin jin dadin jama'a kuwa sanarwar hadin gwiwar ta bayyana cewa India ta jaddada kudurinta na taimaka wa Najeriya ta hanyar bashi mai sassauci da taimaka mata da kwararru.

  11. An ceto mutum 77 da rai bayan faɗuwar gini a Tanzaniya

    ..

    Hukumomi a Tanzaniya sun tabbatar da ceto mutum 77 da ransu bayan wani gini mai hawa huɗu ya faɗi a babban birnin ƙasar, Dar es Salaam.

    Kwamishinan birnin, Albert Chalamila, ya ce tun bayan fara aikin ceton a ranar Asabar mutum biyar ne aka tabbatar da muturwarsu, tare da ceto 77 da ransu.

    Mista Chalamila ya ce tawagar aikin ceton ta gano daidai wurin da mutanen da suke maƙale a ginin, kwana guda bayan faɗuwar ginin.

    Tawagar ceto ta riƙa tura wa mutanen da ke maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ruwan sha da iskar shaƙa da ɗan abinci ta hanyar ramukan da ke tsakanin ɓaraguzan.

    A ranar Asabar ne aka girke jami'ai daga sashen kare aukuwar bala'o'i da rundunar 'yansanda da ta sojoji domin taimaka wa aikin ceton.

  12. Mutane na bin layuka don samun ruwan sha a Odesa bayan harin Rasha

    mutane

    Asalin hoton, Reuters

    Wasu daga cikin hotunan yadda mutanen yankin Odesa na Ukraine, ke bin layi domin samun ruwan sha, bayan hare-haren Rasha sun faɗa kan tashar samar da ruwan sha ta yankin.

    Tun da farko shugaban yankin, Oleh Kiper ya ce an samu katsewar lantarki da ruwan sha a yankin sakamakon harin na Rasha.

    To sai dai ya ce jami'an na ƙoƙari don maido da ruwan shan.

    mutane

    Asalin hoton, Reuters

  13. An gudanar da jana'izar babban limamin masallacin Juma'a na Minna

    Masu janaza

    Asalin hoton, Nuruddeen Isyaku Daza

    Anyi Jana'izar babban limamin masallacin Juma'a na garin Minna, Sheikh Isah Fari.

    Marigayin mai shekara 93, ya rasu ne ranar Asabar da daddare bayan fama da doguwar jinya.

    Masu janaza

    Asalin hoton, Nuruddeen Isyaku Daza

    An gudanar da jana'izar ne ranar Lahadi a babban masallacin Juma'a na garin Minna.

    Masu janaza

    Asalin hoton, Nuruddeen Isyaku Daza

    Cikin waɗanda suka halarci Jana'izar har da Mataimakin Gwmanan Jihar Neja Yakubu Garba, da tsohon gwmanan Jihar, Abubakar Sani Bello da Maimartaba Sarkin Minna Dakta Umar Faruk Bahago.

    Masu janaza

    Asalin hoton, Nuruddeen Isyaku Daza

  14. Tinubu ya bai wa firaministan Indiya lambar yabo ta GCON

    Narendra Modi da Bola Tinubu

    Asalin hoton, Narendra Modi/X

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karrama firaministan Indiya, Narendra Modi da lambar yabo ta biyu mafi daraja a ƙasar wato GCON.

    Tinubu ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da Mista Modi a fadar gwamnatinsa da ke Villa a Abuja.

    A ranar Asabar da daddare ne firaministan na Indiya ya isa Najeriya a wata ziyara ta kwana guda da zai yi a ƙasar

    Shugaban na Najeriya ya ce ya bai wa Modi lambar girmamawar ce domin ''nuna godiyarmu ga Indiya a matsayin ƙawar Najeriya''.

    Ziyarar Modin ita ce ta farko da wani firaministan Indiya ya kai wa Najeriya tun 2007, lokacin da Firaminitan na wancan lokaci Dakta Dr Manmohan Singh ya kai ƙasar.

    Shugabannin biyu za su mayar da hankali a tattaunawrsu wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Narendra Modi da Bola Tinubu

    Asalin hoton, Narendra Modi/X

  15. An kashe mutum biyu a birnin Odesa - Shugaban yankin

    ..

    Asalin hoton, State Emergency Service of Ukraine

    Shugaban yankin Odesa na Ukraine ya ce an kashe mutum biyu tare da raunata wani yaro mai shekara 17 a Odesa Oblast.

    Oleh Kiper ya ce yanzu haka ana ci gaba da aiki domin maido da lantarki da ruwa a yankin da ke kudancin Ukraine.

    Haka ma a yankin Dnipropetrovsk, shugaban sojin yankin, Serhiy Lysa ya ce an kashe wasu mutum biyu tare da raunata biyar a gundumar Nikopol.

  16. INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan Ondo

    ..

    Asalin hoton, Channels Youtube

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓe daga ƙananan hukumomin jihar.

    A yanzu za a karɓi sakamakon ne daga ƙananan hukumomi uku da suka rage cikin 18 na jihar, bayan karɓar na ƙananan hukumomi 15.

    Kawo yanzu ɗan takarar jam'iyyar APC, wato gwamnan jihar Lucky Aiyedatiwa ne ke kan gaba a sakamakon da aka tattara, sai na PDP ke biye da shi.

  17. Cikin hotuna: Yadda mazauna Kyiv ke neman mafaka a tasoshin jiragen ƙasa

    Mutane

    Asalin hoton, Reuters

    Mun samu hotunan yadda wasu mazauna birnin Kyiv ne neman mafaka a tasoshin jiragen ƙasa na ƙarƙashin ƙasa a babban birnin ƙasar, yayin da hare-haren Rasha suka gigita Ukraine.

    Wuraren da jama'a ke taruwa domin jiran jirgi na maƙare da jama'a rufe da barguna, da rigunan sanyi, yayin da wasu da dame ke riƙe da karnuka da magunansu.

    Mutane

    Asalin hoton, Reuters

    Mutane

    Asalin hoton, Reuters

    Mutane

    Asalin hoton, Reuters

  18. Rasha ta hari tashar makamashinmu - Zelensky

    Zelensky

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ta ƙaddamar da ''munanan hare-haren makamai masu linzami 120 da jirage marasa matuƙa 90 a duka yankunan Ukraine'

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Telegram, shugaban na Ukraine ya ce Rasha ta ƙaddamar da hare-haren ne kan tashar samar da makamashi ta Ukraine.

    Mista Zelensky ya ce wasu sassan ƙasarsa a yanzu haka ba su da wutar lantarki, amma ya ce ana koƙarin maido da ita.

    Shugaba Zelensky ya ƙara da cewa rundunar tsaron samaniyar kasa ta kakkaɓo fiye da makamai 140.

  19. An kashe mata biyu a birnin Mykolaiv - Hukumomin Ukraine

    Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce wasu mata biyu sun mutu bayan harin jirgi maras matuƙi da Rasha ta ƙaddamar kan birnin Mykolaiv.

    Haka kuma harin ya raunata mutum shida ciki har da ƙananan yara biyu, kamar yadda hukumar ta yi ƙarin haske.

    Gwamnan yankin Mykolaiv, Vitaliy Kim ya ce an samu ''yawaitar'' hare-haren jiragen marasa matuƙa da tsakar daren da ya gabata.

    An lalata gidaje da dogayen gine-gine da motoci da manyan kantuna da sauran ababen more rayuwa, yayin da gobara ta tashi bayan harin, kamar yadda gwamnan ya bayyana.

  20. Rasha ta ƙaddamar da hari mafi muni tun farkon Satumba kan Ukraine

    .

    Asalin hoton, State Emergency Service Of Ukraine

    An kwashe tsawon daren da ya gabata ana jin ƙarar amon sautin na'urorin ankararwa a faɗin Ukraine, yayin da Rasha ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa a wasu sassan ƙasar.

    Ukraine ta fuskanci hare-hare masu muni irin waɗannan, to amma wannan shi ne mafi muni da aka kai ƙasar tun farkon watan Satumba.

    Ana ganin an kai harin kan tashar makamashin ƙasar - wadda ta ƙunshin manyan injinan samarwa da rarraba wutar lantaki a ƙasar.

    A kudancin ƙasar, birnin Mykolaiv na daga cikin wuraren da hare-haren suka fi muni, inda mutum biyu suka mutu, da dama suka jikkata.

    Haka ma birnin Odesa da ke gaɓar tekun Black Sea an fuskanci katsewar lantarki.

    Sannan a babban birnin ƙasar, Kyiv, tarkacen makamai da jirage marasa matuƙan da aka kakkaɓo sun faɗa a wurare daban-daban, amma babu rahoton jikkata.