Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 6 ga watan Maris 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza

  1. Amurka da Isra'ila sun ce suna shirin shiga sabon mataki a yaƙin Iran

    Amurka da Isra'ila sun ce suna shirin shiga sabon mataki na gaba a yakin da suke yi da Iran

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya ce, suna dab da kara karfin hare-haren da suke kai wa Iran din sosai.

    Rundunar sojin Isra'ila kuma ta ce, ta fara, kai abin da ta kira manyan hare-hare a kan cibiyoyi da kayayyaki a Tehran, babban birnin Iran din.

    Shugaban babbar rundunar sojin Amurka, ya ce an kassara duk wani karfi na amfani da kai hari da makamai masu linzami na Iran, na yanzu da kuma na nan gaba.

    Admiral Brad Cooper ya kuma ce Amurka ta nutsar da jiragen sojin ruwa na Iran sama da talatin.

  2. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami da aka harba cikin dare

    Ma’aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ta ce dakarunta sun kakkaɓo wasu jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami da aka kai harba zuwa ƙasar cikin dare.

    A cikin wasu saƙonni da ma’aikatar ta wallafa a shafinta na X ta bayyana cewa an gano wani makami mai linzami wanda daga bisani aka kakkabo shi tare da lalata shi a kusa da birnin Al-Kharj, da ke kudu maso gabashin babban birnin ƙasar Riyadh.

    Ma’aikatar ta ƙara da cewa a cikin sa’a ta ƙarshe ma an sake kakkabo wasu jirage marasa matuƙa da dama a kusa da birnin Riyadh.

    Jami’an tsaro kasar sun ce dakarun ƙasar na aiki don dakile duk wata barazana da ka iya shigowa cikin ƙasar.

    Ba a bayar da rahoton jikkata ko asarar rayuka ba zuwa yanzu.

  3. Wane ne Mojtaba Khamenei, wanda ake hasashen zai zama jagoran addinin Iran?

    Bayan kashe jagoran addinin Iran, Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila a Iran, sai aka fara tunanin ko ɗan marigayin Mojtaba wanda shi ma yake da ƙarfin faɗa a ji ya rasu.

    Sai da aka yi kwanaki ba a ji ɗuriyarsa ba, kuma babu tabbaci. Sai a ranar Talata 3 ga watan Maris ne kafofin watsa labarai suka tabbatar da cewa Mojtaba yana raye, kuma yana cikin ƙoshin lafiya. Sai dai har yanzu bai fito ba.

    Yanzu yana cikin na gaba-gaba a cikin waɗanda ake hasashen za su iya maye gurbin jagoran addinin ƙasar, kamar yadda kafar Reuters ta ruwaito daga wasu majiyoyi guda biyu a Iran.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

    Aisha Babangida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.