Ana ce-ce-ku-ce kan shawarar Trump na mata masu ciki su daina amfani da paracetamol
Ana ci gaba da sukar shawarar da shugaban Amurka, Donald Trump ya bayar akan daina amfani da kwayar paracetamol ga mace mai dauke da juna biyu saboda haɗarin haihuwar jariri mai lalurar Autism .
Gidauniyar kula da masu lalurar Autism ta ce ta damu matuka, sannan kuma ta bayyana cewa babu wani ingantaccen bincike na kimiyya da ya danganta alakar maganin da lalurar Autism.
Trump ya ce ya bayar da shawararce saboda ana samun ƙaruwar masu lalurar Autism, kuma yana ganin kamar maganin na da alaka da hakan.
Da ya ke jawabi a fadar white house tare da sakataren kula da harkokin lafiya na kasar Robert F Kennedy, shugaban ya kuma soki wasu alluran rigakafin da ake yi wa yara inda ya ce wasunsu na janyowa yara kamuwa da cutuka masu matukar hadari.
Mahukunta a ɓangaren lafiya a kasar za su yi nazari akan wanann shawara inda za su zabi ko su yi amfani da shawarar shugaban kasar ko kuma a'a.