Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Gobe Laraba za a sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Malawi

    Hukumar zaɓen Malawi ta musanta cewa an ba ta umarnin kotu, wanda ya hana ta bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasar bayan zaɓen da aka yi a ranar 16 ga Satumba.

    Kakakin hukumar ta MEC, Sangwani Mwafulirwa, ya ce hukumar ta kusa kammala shirye-shirye domin bayyana sakamakona ranar Karaba da rana.

    An ayyana sakamakon gundumomi 24 daga cikin 36 na ƙasar, inda tsohon shugaban ƙasar, Peter Mutharika ya ci gaba da kasancewa a kan gaba, yayin da shugaba mai ci Lazarus Chakwera ke biye masa.

  2. Isra'ila ta rufe mashigar Falasɗinu daga Jordan

    Isra’ila ta rufe iyakar ALan-Bi wadda ita ce kaɗai hanya tsakanin Jordan da yankin Falasɗinu da Isra’ila ta mamaye a Yammacin Kogin Jordan har sai baba-ta-gani, kwanaki kaɗan bayan an sake buɗe ta sakamakon harbin da ya hallaka sojojin Isra’ila biyu.

    Bayanai daga sojojin Isra’ilar sun ce jami’an su sun samu umarnin rufe iyakar ne daga Firaminista Benjamin Netanyahu.

    Sun kuma tambayi ofishinsa Netanyahu ko wannan mataki na da alaƙa da matakan wasu ƙasashen duniya na baya-bayan nan kan amincewa da kafa ƙasar Palasɗinu, amma babu wata amsa game da batun.

    Iyakar ALan-Bi ce kaɗai hanyar fita da shiga Falasɗinu daga Yammacin Kogin Jordan ta ƙasa, kuma ita ce babbar hanyar jigilar kayayyaki.

  3. Trump ya ce Ukraine za ta ƙwace duka yankunanta

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna wata alama da ke nuna gagarumin sauyin matsayarsa game da yakin Ukraine, da kuma abin da ka iya faruwa bayan arewar yaƙin.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Mista Trump ya ce ''Ina ga ya kamata Ukraine ta samu nasarar ƙwato duka yankunanta ta hanyar goyon bayan Tarayyar Turai''.

  4. Mutum biliyan ɗaya da rabi ne ke fama da hawan jini a duniya - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce kusan mutum biliyan ɗaya da rabi ne ke fama da hawan jini a duniya.

    Cikin wani rahoto da hukumar lafiyar ta gabatar kan matsalar hawan jini a babban taron Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 1,000 ne ke mutuwa a kocewa sa'a sakamakon bugun zuciya da mutuwar ɓarin jiki, waɗanda dukkaninsu hawan jini ke haifar da su.

    Da yake jawabi, shugaban hukumur WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce akwai buƙatar ƙasashe su tashi tsaye, domin ɗaukar matakan daƙile barazanar hawan jini domin ceto rayukan al'ummar duniya.

    ''Hawan jini ne babban abin da ke haifar da bugun zuciya da ciwon koda da kuma mutuwar ɓarin jiki - waɗanda ta ce dukkaninsu ana iya magance su'', in ji shi

    Ya ƙara da cewa mutum biliyan 1.4 ne ke fama da hawan jini a duniya a shekarar 2024, kuma a cewar rahoton kashi ɗaya ne cikin biyar aka iya magancewa ta hanyar magani da kuma bin matakan da suka dace na lafiya.

    Dakta Ghebreyesus ya ce hawan jini na kashe mutum miliyan 10 a kowace shekara, duk da cewa ana iya magance shi.

    Hukumar lafiyar ta yi nazari ne a ƙasashe 195, kuma ƙananan ƙasashe ne galibi matsalar ta fi kamari.

    ''Kashi 28 na ƙananan ƙasashe ne kawai suka bayar da rahoton samun wadatattun maganin hawan jini a ɗakunan shan magani da wuraren sayar da maganin'', a cewar Mista Ghebreyesus .

    Ya ci gaba da cewa abubuwan da ke ƙara haifar da matsalar sun haɗa da barasa da taba sigari da kuma rashin motsa jiki da shan gishiri da ya wuce kima a cewar rahoton na WHO.

    WHO ta ce idan har hukumomi ba su ɗauki mataki ba, to miliyoyin mutane za su ci gaba da mutuwa ba shiri, wanda zai iya shafar tattalin arzikin ƙasashen duniya.

  5. 'An samu ƙaruwar gawarwaki a babban asibitin Gaza'

    Likitoci a babban asibitin Gaza sun ce sun asibitin na ci gaba da fuskantar gawarwaki masu tarin yawa kusan kowanne lokaci.

    Ɗaya daga cikin likitocin asibitin Dakta Arub ta ce yaƙin ya tilasta musu yin tiyata ba tare da alluran rage zogi ko sanya barci ba.

    Rahotanni sun ce tankokin yaƙin Isra’ila a yanzu suna nisan mita ɗari biyar daga asibitin Al Shifa, da ke tsakiyar birnin Gaza, a ci gaba da farmaki da suke da sunan kai wa Hamas.

    Shi ma wani likitan sa kai ya bayyana yadda ya ceci wani jariri daga cikin gawar wata mata mai juna-biyu da ta rasa ranta bayan an harbe ta a kai.

  6. Ƙasashen Nato su harbi duk jirgin Rasha da ya keta samaniyarsu - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ƙasashen Nato za su iya harbo duk wani jrigin Rasha da ya keta sararin samaniyar ƙasashen.

    Yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan gabatar da jawabi a taron MDD, Mista Trump keta sararin samaniyar ƙasashen Nato saɓa doka ne.

    A lokacin ganawarsa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, an tambayi Trymp ko zai goyi bayan hakan, sai ya ce ''ƙwawari kuwa''.

  7. Sanata Natasha ta koma ofishinta a Majalisar Dattawa

    Yar majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta koma ofishinta da ke harabar majalisar bayan ƙarewar wa'adin dakatarwar wata shida da majalisar ta yi mata.

    Cikin wani bidiyon komawarta ofishin nata, da ya karaɗe shafukan sada zumunta, yar majalisar ta zargi shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Godswill Akpabio da ɗaukarta a matsayin baiwarsa.

    Ta ce kamar yadda Akpabio ke matsayin sanata haka ita ma sanata ce.

    Sanata Natasha ta ce duk da cewa an dakatar da ita ba bisa ƙa'ida ba, ta riƙa sauke nauyin al'ummar mazaɓarta na Kogi ta Tsakiya, saboda a cewarta ba ta son al'ummarta su ji kamar an yi watsi da su.

  8. Ƙasashen da suka amince da kafuwar ƙasar Falasɗinu

    Ƙasashen Birtaniya da Australia da Kanada da kuma Portugal sun amince da kafa ƙasar Falasdinu a hukumance a ranar Lahadi.

    Ana sa ran wasu da dama za su amince a taron ƙolin Majalisar dinkin Duniya da ake yi a a birnin New York na Amurka.

    Fiye da kashi uku cikin hudu na ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193 suka amince da kafa ƙasar Falasɗinu.

    Ƙasashen da ba su amince da matakin ba sun haɗa da Amurka da isra'ila da Italiya da Jamus

    Ga jerin ƙasashen da suka amince da waɗanda ba su amince da kafuwar Falasdinu ba:

  9. Trump ya zargi MDD da haddasa tuɗaɗar baƙin haure zuwa ƙasashen Yamma

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya zargi Majalisar Dinkin Duniya ya ɗaukar nauyin haifar da matsaloli a kan iyakokin ƙasashen Yamma.

    Yayin da yake jawabi a babban zauren taron Majalisar a birnin New York, Mista Trump ya yi zargi majalisar da bai wa ƴancirani kuɗi, musamman waɗanda ke shiga Amurka daga kan iyakarta ta kudanci.

    "Ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da mamayar ƴan ci-rani, kada ta yi abin da zai haifar da su, sannan ta daina ɗaukar nauyinsu'', in ji shi.

    Shugaban na Amurk aya yi dogon jawabia a majalisar na kusan sa'a guda, yana yi wa shugabannin duniya jawabi kan batutuwa daban-daban.

  10. Babban Bankin Najeriya ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin ɗari.

    Gwamnan CBN, Dr. Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa shawarar rage kuɗaɗen ruwa ta biyo bayan ci gaba da saukar hauhawar farashin kayayyaki da aka samu cikin watanni biyar da suka gabata.

    Haka kuma, bankin ya ce ya rage ƙa'idar kuɗaɗen ajiya ga manyan bankuna zuwa kashi 45, yayin da aka bar na bankunan kasuwanci a kashi 16.

    Kwamitin manufofin kudi na Babban Bankin ya sanar da wata sabuwar ƙa'idar ajiyar kuɗ a ɓangaren ɓangaren gwamnati.

    Matakin na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar NBS ta sanar da ƙaruwar arzikin cikin gida na ƙasar a rubu'in na biyu na shekarar 2025.

  11. China ta kwashe ɗimbin mutane yayin da take shirin fuskantar mummunar guguwa

    China ta kwashe dubban mutane tare da rufe makarantu da wasu kasuwanci a akalla birane 10, yayin da aka yi hasashen mummunar guguwar da ake kira da Super Typhoon Ragasa da ake ganin za ta auka wa gaɓar kudancin ƙasar.

    Rahotanni sun ce sama da mutum 370,000 aka riga aka kwashe daga lardin Guangdong inda ake sa ran guguwar za ta yi ƙarfin gaske a ranar Laraba, sannan daga baya ta nufi arewacin Vietnam, inda za ta iya shafar miliyoyi.

    A Hong Kong kuwa, an fitar da gargadi kan zuwa guguwar mataki na takwas, yayin da shaguna suka rage kaya, kuma filin jirgin saman ƙasar ya gargadi cewar zirga-zirgar jirage za ta fuskanci cikas daga yamma zuwa washegari.

  12. Ƴansanda sun kama ɗansandan bogi a Kano

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta kama wani mutum da ya ke yaudarar jama’a da sunan shi jami’in ‘yan sanda ne domin karɓar musu kuɗi.

    An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi 21 ga Satumbar 2025 a wajen Kofar Dawanau,sanye da kayan ƴansanda.

    Sanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ‘yan sanda domin damfarar jama’a.

    Binciken farko ya tabbatar cewa wanda ake zargin ba ɗan sanda ba ne, kuma ba shi da alaƙa da rundunar kwata-kwata.

    Sai dai ya dade yana amfani da sunan jami’in ƴansanda domin yaudarar mutane.

    Rundunar ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bayan kammala bincike.

    Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai ko ƙorafe-ƙorafe idan sun san wani abu game da wanda ake zargi ko makamantansa.

  13. Cutar mashaƙo ta kashe mutum biyu a Kaduna

    Rahotanni daga ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa an rufe wasu makarantun gwamnati bayan ɓullar cutar mashaƙo wato diptheria a jihar, inda ta ti sanadiyar kashe mutum biyu.

    Kwashishinar lafiya a jihar, Hajiya Umma K. Ahmed ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce sun killace wasu da dama a sanadiyar ɓullar cutar, amma sun samu sauƙi, kuma an sallame su.

    Cutar mashaƙo dai cuta ce da take shaƙe mutane, sannan ta sarƙe musu numfashi, lamarin da ke kai wa ga kashe mutum idan ba a kai masa matakin gaggawa ba.

  14. Ƴansanda sun jefa wa magoya bayan Natasha barkono mai sa hawaye

    Ƴansanda sun tarwatsa magoya bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, waɗanda suka raka ta zuwa Majalisar Dattawa daga babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda suka watsa musu barkono ma isa hawaye domin tarwatsa su.

    Magoya bayan sun yi tattaki ne domin raka sanatar zuwa majalisar domin komawa bakin aikinta.

    Tun da farko, majalisar ta buɗe ofishin sanatar da ke cikin ginin Majalisar ta Dattawa.

    Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa Majalisar Dattawa mako guda da ya wuce domin sanar da niyyarta ta komawa aiki bayan dakatarwa na tsawon wata shida, amma majalisar ta ce ta ɗan jira tukuna.

    A watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawa tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da Sanata Natasha al'amarin dai ya kai ga har Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da ita daga zauren majalisar lamarin da ya kai ga dakatar da ita na tsawon wata shida.

  15. Sama da kashi 90 sun amince da gyaran ƙundin tsarin mulki a Guinea

    Fiye da kashi 90% na ƴan ƙasar Guinea sun amince da gyaran ƙundin tsarin mulki a zaɓen raba gardama da aka gudanar ranar Lahadi, kamar yadda sakamakon farko ya nuna a daren Litinin.

    Ana ganin wannan zaɓen mataki ne na dawo da mulkin farar hula.

    Duk da haka, sabon tsarin mulkin zai ba Janar Mamady Doumbouya damar yin takara a zaben shugaban ƙasa kuma ya tsawaita wa’adin mulkinsa daga shekaru 5 zuwa 7.

    Shugabannin jam’iyyu biyu masu adawa da suka haɗa da Cellou Dalein Diallo da tsohon shugaban ƙasar Alpha Condé, sun yi kira ga mutane da su yi watsi da zaɓen.

    A halin yanzu dai an dakatar da jam’iyyunsu.

    Masu sukar gwamnati sun ce zaɓen yunƙuri ne na kama iko, yayin da ƙungiyar kare haƙƙn bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnati da dakatar da jam'iyyun adawa da kuma rufe kafafen yaɗa labarai.

    A makonni kafin zaɓen, rundunar soji ta dakatar da jam’iyyu uku da rushe fiye da jam’iyyun siyasa 50.

    Kimanin mutum miliyan 6.7 ne suka yi rajista don kada kuri’a a ƙasar.

    Ana sa ran gudanar da zaben shugaban ƙasa kafin ƙarshen shekara.

  16. Majalisar dokoki ta buɗe ofishin Sanata Natasha

    Majalisar Dokoki ta buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke Suite 2.05 a sashen Majalisar Dattawa.

    Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa Majalisar Dattawa mako guda da ya wuce domin sanar da niyyarta ta komawa aiki bayan dakatarwa na tsawon watanni shida.

    A watan Fabrairu ne dai tankiya ta ɓarke a zauren majalisar dattawa tsakanin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da Sanata Natasha al'amarin dai ya kai ga har Akpabio ya umarci ɗaya daga cikin masu yi wa sandan majalisar hidima da ya fitar da ita daga zauren majalisar lamarin da ya kai ga dakatar da ita na tsawon wata shida.

    Wannan lamarin ya kai ga har Sanata Natasha ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta hukunta majalisar dattawan Najeriya game da dakatarwar da aka yi mata.

  17. Babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh ya rasu

    Allah Ya yi wa babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya, Sheikh Abdul Aziz Al-Sheikh rasuwa.

    Za a yi jana'izar marigayin a masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke Riyadh bayan sallar La'asar, kamar yadda Sarkin Saudiyya ya sanar.

    Haka kuma, za a yi masa Salatul Gaib a masallacin Ka’aba, masallacin Annabi Muhammad SAW, da dukkan masallatan da ke Saudiyya.

    Sheikh Abdul Aziz ibn Abdullah Al-Sheikh, wanda ya kasance babban mai fatawa na ƙasar Saudiyya, ya shahara wajen kyakkyawan shugabanci da tasiri a al’umma.

    Ya kasance mutum mai girmamawa da kyawawan halaye, wanda mutane da dama suka ɗauka a matsayin jagora wajen shari’a da addini.

  18. An yanke wa sojojin Najeriya uku hukuncin ɗaurin rai da rai

    Wata kotun soji a Najeriya ta yanke wa sojoji huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, jihar Borno.

    A cikin wata sanarwa da kotun ta fitar, shugaban Kotun, Brigadier Janar Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari.

    Wannan hukunci ya biyo bayan amincewar su kan aikata laifuffukan da suka haɗa da "sata da kasuwancin makamai ba bisa ka’ida ba, da taimaka wa maƙiya" wanda duka laifuka ne ƙarƙashin dokar sojojin Najeriya.

    Kotun ta bayyana cewa "irin wannan safarar da ba bisa ƙa’ida ba na zamewa haɗari ga sojoji da ayyukan soja, da kuma tsaron ƙasa, don haka yana nufin taimaka wa maƙiyan ƙasar".

    Shugaban Kotun, Brigadier Janar Abdullahi, ya ce waɗannan laifuka da sojojin suka aikata ba matsala ce kawai ta karya doka ba, har ma da cin amana, da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.

    Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci irin waɗannan rashin ɗa’a da halayen damfara ko rashin kwarewa ba.

    Borno ce cibiyar rikicin Boko Haram da Najeriya ta kwashe kimanin shekara 15 tana fama da shi, lamarin da ya laƙume rayukan dubban mutane da haifar da matsalar jin-ƙai.

  19. Majalisar dokokin ƙasa ta ɗage ranar komawa hutu

    Majalisar dokokin Najeriya ta ɗage ranar komawa hutu daga 23 ga Satumba zuwa 7 ga Oktoba, amma ta ce kwamitoci za su ci gaba da gudanar da ayyukan su.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanawa da majalisar ta aika wa dukkan ‘yan majalisar, inda ta yi kira da su sake shirye-shiryensu da tsare-tsarensu domin su yi daidai da canjin da aka samu.

    Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce yana yi ‘yan Najeriya albishir cewa majalisar za ta hanzarta amincewa da dokar gyaran kundin tsarin mulki na 1999.

    Tajudeen ya ce za a tattauna da majalisun jihohi cikin mutunci don samun amincewarsu, sannan za a ci gaba da aiki tare da ɓangaren zartarwa da sauran jama’a domin tabbatar da cewa tsarin gyaran ya gudana cikin sauƙi.

    Mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin gyara kundin tsarin mulki, ya ce za a gudanar da tsarin cikin haɗin kai da ba kowane ɓangare dama domin tabbatar da cewa kowa ya samu damar shiga cikin harkar.

  20. Museveni zai sake tsayawa takarar shugaban Uganda bayan shekara 40 a mulki

    Hukumar zaɓen ƙasar Uganda ta amincewa shugaba ƙasar mai shekaru 81, Yoweri Museveni, wanda ya riƙe mulkin ƙasar kusan shekaru arba’in, ya tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaben da za a gudanar shekara mai zuwa.

    A jawabin amincewarsa, Museveni ya yaba wa jam’iyyarsa kan zaɓen sa a matsayin wanda zai tsaya takara.

    Museveni yana neman wa’adi na bakwai a shugabancin ƙasar.

    Ana sa ran zai yi magana ga magoya bayansa a wani taron jama’a a filin ‘Independence Grounds’ kusa da Kampala.

    Za a tsayar da babban abokin hamayyarsa, Bobi Wine a gobe.

    Jam’iyyu hudu sun riga sun fice daga takarar, ciki har da jam'iyyar Democratic da jam'iyyar PFF ta Dr. Kizza Besigye.

    Besigye, wanda aka kama a Kenya a shekarar da ta gabata kan zargin cin amanar ƙasa, ba zai bayyana a takardar zabe ba.

    Masu sukar gwamnati na cewa Museveni ya mulki Uganda da karfi tun 1986.

    A zaben 2021, ya samu kashi 58 yayin da Bobi Wine ya zo na biyu da kashi 34.

    Ana sa ran gudanar da zaɓen a ranar 12 ga Janairu a shekara mai zuwa.