Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Umar Mika'il

  1. Tinubu ya umarci sojoji su canza salo wajen yaƙi da ’yan bindiga a Katsina

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci rundunar sojojin ƙasar da su canza salo wajen fatattakar ƴan bingida a jihar Katsina ta hanyar amfani da na'urori na zamani wajen sanya ido kan matsalar tsaro.

    Tinubu bayyana hakan ne yayin ganawarsa da gwamnan jihar Dikko Radda da wasu shugabannin jihar a fadar gwamnati.

    Tinubu ya kuma jaddada muhimancin magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

    "Za a ƙara ɗaukar matakan tsaro na cikin gida, ciki har da yiwuwar kafa ƴan sandan jihohi da ƙarfafa masu gadin daji."

    Ya kuma buƙaci a rika samun rahoton aiki kullum daga Katsina.

    Shugaban ya ce dole ne a kare rayuka da yara da wuraren ibada da kasuwanci, yana mai cewa: “Ba za mu bari waɗannan ƴan bindigan su tsoratar da mu ba.”

  2. Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Maulidi

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana Juma'a 5 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidi na tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammad (S.A.W).

    Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta fitar ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun babbar sakatariya a ma'ikatar, Magdalene Ajani.

    Miliyoyin al'ummar Musulmi ne ke bukukuwan Maulidi a Najeriya da kuma faɗin duniya a duk irin wannan lokaci, kowace shekara.

    Sanarwar da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta buƙaci al'ummar ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yin addu'o'in samun zaman lafiya a ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.

  3. Poland ta tada jiragen yaƙi don kare kanta bayan harin Rasha a Ukraine

    Ƙasar Rasha ta kaddamar da wani gagarumin hari a yammacin kasar Ukraine, lamarin da ya jefa jama'a cikin kidima.

    Wanna harin ya tursasawa Poland mai makwabtaka ta da jiragenta masu saukar ungulu don kare sararin samaniyarta.

    Harin na Rasha ya zo ne a daidai lokacin da shugaban ƙasar Vladimir Putin ke halartar wani gagarumin faretin soji a birnin Beijing, tare da shugaban China Xi Jinping da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un.

    A jiya Talata ne aka ji cewa shugaban Amurka Donald Trump na cewa ya ji takaicin yadda shugaba Putin ke masa wasa da hankali, yana mai cewa gwamnatinsa na nan na shirin ɗaukar wasu matakai da nufin kawo karshen yakin.

  4. Babu wata ƙasa da ta isa ta ɗaga mana yatsa - Shugaban China

    Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani mahaluki a doron duniya, da zai ɗagawa kasarsa yatsa, ko yi mata barazana ko ci zarafinta.

    Yana magana ne yayin da ya ke baje kolin manyan makaman da ƙasar ta mallaka, ciki har da makamai masu linzami na Nukiliya da ka iya kaiwa ko wanne lungu da saƙo na duniya.

    An kuma nuna wasu manya manyan jiragen ruwan soji, da ka iya nutsewa a cikin ruwa harma su yi nisan akalla mita ashirin a karkashin ruwan.

    A sararin samaniya, jiragen yaƙi masu layar zana sun yi ta shawagi, a wani salo na nuna wa duniya irin shirin da Chinar ta yi.

    Ƙwararru a ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da ma masana harkar tsaro a duniya na nan na ta nazartar faretin na China.

  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Laraba

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.