Rufewa
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnim.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/09/2025
Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida da Umar Mika'il
Masu bin shafin namu nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnim.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Wani jagoran farar hula a wani yanki na Darfur da ke ƙarƙashin ikon ‘yan tawaye ya ce an gano gawawwaki 270, bayan zaftarewar ƙasa da ta afka wa wani ƙauye da ke kan dutse a ranar Lahadi.
Shugaban hukumar yankin, Mogeeb al-Rahman, ya ce ana kyautata zaton ɗaruruwan mutane maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan duwatsun.
Wani Bidiyo ya nuna yadda mazauna yankin ke haƙar ƙasa da hannayensu domin ceton rayuka.
A ranar Talatar da ta gabata ne, ƙungiyar ‘yan tawayen ta ce kusan duk mazauna ƙauyen waɗanda yawansu ya kai 1,000 sun mutu, in banda mutum guda kacal da ya tsira.
Sai dai hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da suka rasu ba kawo yanzu.
Gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya fifita komawaaikin haƙar man fetur a rijiyoyin Kolmani da na yankin tafkin Chadi a wani ɓangare na yunƙurin farfaɗo da tattalin arziki da rage matsalar tsaron yankin.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a lokacin da suka ziyarci shugaban ƙasar a fadarsa da ke Abuja.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin, ya ce komawa aikin haƙar man yankin zai taimaka wa ayyukan soji a yankin tare da buɗe ƙofar ayyukan ci gaba a yankin.
Zulum ya yaba wa Shugaba Tinubu kan ci gaba da yaƙi da Boko Haram tare da bayar da tallafi ga iftila'in ambaliya da ya auku a jiharsa a shekarar da ta gabata.
Aƙalla mutum 30 sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a ƙaramar Borgu ta Jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya.
Ya zuwa yanzu dai ba a tabbatar da musababbin hatsarin ba ba amma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ƙaddamar da bincike kan lamarin.
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Ara ya shaida wa BBC cewa mutanen sun taso ne daga garin Dugga domin zuwa ta'aziyya lokacin da hatsarn ya rutsa da su.
Baba Ara ya ce bayanan farko-farko da suka samu sun nuna cewa kututture ne da ke cikin ruwan ya haddasa hatsarin.
Batun hatsarin kwale-kwale a Najeriya na neman gagarar kundila, inda a lokuta da dama yake sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Ɗnnmajalisar tarayya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa har yanzu ƙofar jam'iyyar APC a buɗe take ga tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa kwankwaso domin shiga jam'iyyar mai mulki.
Abdulmumin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Politics Today na gidan talbijin na Channels, da yammacin ranar Laraba.
“Dangane da abin da ya shafi APC, ya (Kwankwaso) nanata cewa har yanzu ƙofarsa a buɗe take ga tattaunawa. Komai mai yiwuwa ne," in ji Abdulmuminu
Ɗanmajalisar ya kuma ce shi har yanzu bai ga "wani abu da zai iya hana Tinubu yin tazarce."
Ko a kwanakin baya ma, Rabi'u Musa Kwankwaso ya tabbatar da hakan da bakinsa.
Babban jami'in lafiyar jihar Florida ta Amurka ya bayyana aniyar kawo ƙashen duka riga-kafin da aka wajabta a jihar, ciki har da waɗanda ake son yi wa ƙananan yara saboda makaranta.
Matakin zai sa jihar ta kasance ta farko a Amurka da ta janye kacokan daga allurar riga-kafin da ake da yaƙinin na hana kamuwa da cutuka masu yaɗuwa.
Babban Jami'in lafiyar jihar, Joseph Ladapo ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar tare da gwamnan jihar, Ron De Santis.
Mista Ladapo ya kwatanta tilascin riga-kafin da bautarwa, yana mai cewa mutane na da ƴancin ƙin karɓarsa.
To sai dai ƙwararru a fannin lafiya sun ce matakin zai sanya rayuwar ƙananan yara cikin hatsari.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, DSS ta gurfanar da wasu mutum tara da take zargi da hannu dumu-dumu a kashe-kashen jihohin Benue da Filato.
An gurfanar da mutanen a yau Laraba a babbar kotun tarayya da ke Abuja, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.
Jihohin Benue da Filato sun fuskanci munanan hare-hare a bayana-bayan nan da suka janyo mutuwar ɗaruruwan mutane.
Cikin watan Yuni ne shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ziyarci jihar Benue bayan da aka samu wani mummunan hari da ya haddasa mutuwar mutane da dama.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ciki har da Amnesty International sun yi Allah wadai da sabuwar dokar da gwamnatin mulkin sojin Burkin Faso ta yi na bayyana neman jinsi a matsayin babban laifi.
Burkina Faso ta shiga jerin ƙasashen Afrika da ke nuna rashin amincewarsu da neman jinsi a nahiyar.
A ranar Litinin ne dai ƴanmajalisar ƙasar da aka naɗa ba tare da an gudanar da zaɓe ba, suka haramta nema ko auren jinsi a ƙasar.
Wannan dai na zuwa fiye da shekara guda bayan da majalisar zartarwar ƙasar ta amince da hakan.
Jami’an gwamnati na kallon dokar a matsayin abin da ake da matuƙar buƙata domin kare al’adunsu, inda gwamnatin mulkin sojin ke cewar ta dauki matakin ne don kare martabar aure da na iyali.
China ta karɓi baƙuncin shugabannin duniya fiye da 20 domin bikin cika shekara 80 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.
Shugaba Xi Jinping na tare da shugaban Rasha, da na Koriya ta Arewa a lokacin da suka halarci wani gagarumin faretin soji a dandalin Tiananmen da ke ƙasar.
Wannan ne karo na biyu da China ke bikin faretin nasara.
An yi baje kolin manyan makaman yaƙi tare da nuna ƙarfin sojin ƙasar China.
Kasar Habasha ta bayyana shirinta na komawa kan teburin tattaunawar da ta tsaya tsakanin ta da Sudan da Masar kan cike babbar madatsar ruwa da ke Kogin Nilu, kamar yadda Wazema Radio ta ruwaito.
Habasha na shirin kaddamar da babbar madatsar da ta jima tana jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ta da ƙasasehen da ke makwabtaka da ita..
Ministan ruwa da makamashi na Habasha, Habtamu Etefa, ya ce Masar ce ta janye daga tattaunawar shekaru biyu da suka gabata bayan ta kasa samun adadin ruwan da take nema a duk shekara daga dam din.
Ya kuma bayyana shirin gwamnati na ƙara samun wutar lantarki daga kashi 56 zuwa kashi 90 na jama’a cikin shekaru biyar masu zuwa.
A watan Agusta, Habasha ta yi watsi da yaƙin diflomasiyyar Masar kan madatsar ruwan tana mai cewa ba barazana ba ne.
Wannan madatsar ruwan zai kasance mafi girma a nahiyar Afirka wajen samar da wutar lantarki.
Sai dai hakan ya taɓarɓare dangantaka tsakanin Habasha da Masar.
Taron wanda cibiyar yaki da ta‘addanci na ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, da hadin gwiwar hukumar kula da Kungiyar Ecowas su ka shirya, zai mayar da hankali ne kan yadda za a hada kai wajen kawar da kungiyoyin ta’addanci da karfafa tsaron yankin.
Taron, wanda za a shafe kwanaki biyu ana yi, ya hada jam’ai daga kasashen ECOWAS har ma da wakilan wasu kasashen da suka yi fice daga ecowas din kuma suka hada kawancen kasashen AES, domin tattauna yadda za a magance matsalar ayyukan yan ta’adda da suka addabi yankin baki daya.
Leonardo Santos Simão shi ne mai wakiltar sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya a yankin yammacin Afirka da Sahel, ya kuma ce akwai buƙatar haɗa kan ƙasashen ganin cewa rarrabuwar kan da ake da ita na ragewa kasashen karfin daukar matakin gaggawa a kan barazanar tsaro.
"A cewar alkaluman ta’addanci na duniya na 2025,Africa ta yamma da yankin sahel, su suka fi kowanne yanki fama da matsalar a 2024, inda adadin wadanda abin ya shafa ya karu daga 2023.
A cikin kasashe goma da suka fi mana da matsalar ta’addannci, kasashe biyar na yankin mu. Kuma karuwar ba wai kawai a adadin wadanda abin ya shafa ba, har da girman hare haren sakamakon kara hada kai da suke yi da kuma fadada ayyukan su." In ji Leornado.
A yayin da ake ci gaba da samun karuwar ayyukan ta‘addanci a yankin, alkaluman da wakilin Majalisar Dinkin duniyar ya bayar ya nuna cewa akalla yara 1,364 suka shiga kungiyoyin ta’addanci a kasashe huɗu, yayin da aka ci zarafin mutane 466 ta hanyar lalata.
An kuma kulle makarantu 14,000 saboda matsalar tsaro, inda kuma ake ganin duk da dabarun da akan samar a irin wadannan tarukan, matsaloli kamar na rashin isassun kudi da kuma rarrabuwar kai nah ana shawo kan matsalar.
Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5 ga Shirin Abinci na Duniya (WFP) domin samar da tallafin abinci da na abinci mai gina jiki ga ‘yan Najeriya, musamman ma waɗanda rikice-rikice suka raba da muhallansu.
Wannan tallafi zai bai wa WFP damar kai agajin abinci da kula da lafiyar gina jiki ga mutum 764,205 a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Najeriya da rikici ya shafa.
A cewar shirin, daga cikin masu amfana akwai mata masu juna biyu da masu shayarwa 41,569, da kuma yara 43,235, waɗanda za su karɓi tallafin abincin.
Shirin ya ce wannan taimako daga gwamnatin Amurka na da matuƙar muhimmanci wajen ceto rayuka da rage matsalar yunwa da rashin abinci mai gina jiki a yankunan da rikici ya daɗe yana addaba.
Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) kan yunƙurinta na kafa sabuwar majalisar dattawan Kano.
Gwamnatin ta bayyana cewa tun a Janairun 2024 gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa Majalisar Dattawan jihar ta Kano, wato (KEAC) wadda za ta riƙa ba da shawara kan ci gaban al’umma.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a yau Laraba.
Sanarwar ta ce "Tun bayan sanar da kafa wannan majalisar, ana ci gaba da shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da ingantaccen tsarin da zai ba da damar fara aiki yadda ya kamata."
Sanarwar ta ƙara da cewa "Wannan majalisar ba ta da wata alaƙa da siyasa ko jam’iyya, sai dai ta kasance dandalin bayar da shawara bisa hikima da gogewa."
"Majalisar za ta ƙunshi fitattun mutane daga Kano ciki har da tsofaffin shugabanni, alƙalan kotuna, malamai, sarakuna, ƴan kasuwa da shugabannin tsaro," kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
Gwamnatin ta kuma bukaci dukkan ƙungiyoyi da mutane su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon kirkirar wani abu sabo.
Wannan, a cewar ta, zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan majalisar da tabbatar da cimma burinta na kawo ci gaba da haɗin kai ga jama’ar Kano.
An ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a kammala tsarin kafa majalisar kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da ita.
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan ta yi ta’aziyya ga wadanda zaftarewar kasa ta shafa a yankin tsaunukan Jebel Marra na Darfur, inda ta nemi agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, kamar yadda jaridar gwamnati ta Suna ta ruwaito.
Gwamnatin ta ce za a yi amfani da dukkan hanyoyi don tallafawa wadanda abin ya shafa.
Firaministan farar hula da sojoji ke goyon baya, Kamil Idris, ya ce gwamnati na bibiyar lamarin sosai kuma za ta samar da tallafi daga ciki da wajen kasar.
Kungiyar ‘yan tawaye ta SLM/A ta ce kusan mutum 1,000 na kauyen Tarsin ne suka makale a ƙarƙashin kasa sakamakon ruwan sama mai ƙarfi a ranar 31 ga Agusta.
Shugaban kungiyar, Abdel Wahid Mohamed al-Nur, ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya da su taimaka wajen ceto gawarwaki.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana shirya tallafi ga wadanda abin ya shafa.
Wannan bala’i ya faru ne yayin da rikici mai tsanani ke ci gaba a sassa da dama na Sudan, ciki har da Darfur, tsakanin sojoji da dakarun RSF.
Hukumar Tsaro ta DSS ta gurfanar da mutum tara da ake zargi da hannu a kashe-kashe da suka faru a jihohin Benue da Plateau, kamar yadda Gidan talabijin ta Channels ta ruwaito.
An gurfanar da su ne a yau, ranar Laraba a kotun tarayya da ke Abuja.
Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika, ya musanta zargin cewa aikin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya na 'Nigeria Air' da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ta ƙaddamar a zamaninta na bogi ne.
Sirika, wanda ya rike mukamin minista sau biyu, ya bayyana hakan ne ga gidan talabijin na Channels a ranar Talata inda ya ce an bi dukkan ƙa’idoji.
Ya ƙara da cewa aikin samar da jirgin saman haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da masu zaman kansu, ƙarƙashin kulawar hukumar tafiyar da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu.
Tsohon ministan ya musanta batun cewa ya kashe naira biliyan 100 wajen aikin inda ya ce jimillar kuɗin da aka yi kasafi domin aikin samar da kamfanin sufurin shi ne naira biliyan 5 inda aka saki naira biliyan 3 kuma ya bar fiye da biliyan ɗaya lokacin da ya sauka daga muƙaminsa.
An kaddamar da Nigeria Air a ƙarshen mulkin Buhari, duk da cewa wasu sun ce aikin na bogi ne da kuma zamba.
Tun bayan ƙarewar wa'adinsa na minista a 2023, Sirika ya riƙa fuskantar shari’a kan zargin almundahana da amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba.
Hukumar EFCC ta zarge shi da bai wa kamfanonin ‘yan'uwansa, ciki har da ‘yarsa kwangiloli da suka kai na biliyoyin naira.
Ana ci gaba da aikin ceto a wani ƙauye mai nisa a Darfur da ke Sudan, inda aka yi zaton zabtarewar ƙasa ta hallaka ɗaruruwan mutane tare da shafe wani ƙauye baki ɗaya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana haɗa kai da ƙungiyoyin agajin yankin wajen bayar da taimakon gaggawa a kusa da kauyen Tarsin da ke yammacin El Fasher.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.
Amma kuma MDD ta ce aƙalla mutum 370 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da ƙungiyar ‘yan tawaye masu iko a yankin ke cewa waɗanda suka mutu sun fi 1,000.
Ƙoƙarin kai agaji yana fuskantar cikas saboda yaƙin da ake yi a Sudan, lamarin da ya sa Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta nemi a dakatar da faɗa domin taimako ya isa wurin.
A ranar Talata ne wata kotun Majistare da ke Ikorodu ta bayar da umarnin a gudanar da gwajin ƙwayar gado (DNA) kan Liam Aloba, ɗan marigayi, mawaki Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mohbad.
Alƙali Adefisoye Sonuga ya bayar da umarnin ne bayan ya saurari ƙarar da mahaifin marigayin, Joseph Aloba, ya shigar, inda ya nemi a tantance matsayin yaron.
Umarnin ya ƙunshi cewa a gudanar da gwajin a sanannan asibiti a Najeriya da kuma a ƙasashen waje.
A cikin takardun da aka miƙa wa kotu, mahaifin Mobad ya bayyana cewa akwai rashin tabbas game da ko Mobad ne ainihin mahaifin Liam, don haka dole ne a tabbatar da gaskiya bisa la’akari da muhimmancin lamarin.