Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 31/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Mu kwana lafiya

    Masu bibiyar wannan shafi na kai tsaye, da haka ne za mu dakata da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Sai ku tara da mu gobe da safe idan Allah ya kai mu inda za mu kawo maku wasu ƙarin labaran.

    Kafin nan kuna iya duba ƙasa domin karanta labaran da muka wallafa maku tsawon wannan rana ta Alhamis.

  2. 'Ba mu ji ɗuriyar manoma 21 da ƴanbindiga suka sace ba'

    Bayanai na cewa ana can cikin damuwa, dangane da batun wasu manoma 21 da 'yan bindiga suka sace a garin Bena na yankin ƙaramar hukumar Danko-Wasagu na jihar Kebbi.

    An sace manoman ne yayin da suke aiki a gonakinsu a farkon wannan mako.

    Jama’ar yankin na Danko Wasagu ta gabas dai sun kwashe tsawon aƙalla shekara biyar suna fama da wannan matsala ta hare-haren 'yan bindiga.

    Tun da 'yan bindigar suka sace manoman daga gonakinsu, a garin Bena na yankin karamar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, ake dakon jin duriyar inda aka yi da su. Amma har yanzu ba amo ba labari, a cewar wani mutumin yakin.

    Ya shaida wa BBC cewa kwana kusan biyar da ɗauke mutanen amma har yanzu shiru.

    Matsalar hare-haren da 'yan bindigan ke kai wa yankin na Bena dai ta kai intaha kamar yadda wani mazaunin garin ya ce.

    A cewarsa akwai ƙauyuka da dama da ɓarayin daji suka mamaye kuma sun hana mutane zama ko ma zuwa gona.

    Dangane da matakan tsaro da ake ɗauka, game da wannan matsala ta 'yan bindiga, sai mutumin na yankin Bena ya ce ana ɗaukan matakai amma ba su wadata ba.

    Ya ce akwai buƙatar gwamnati ta kawo masu ɗauki domin cire su daga ƙangin da suka tsinci kansu ciki.

    Mun dai yi ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Kebbi, game da manoman ashirin da daya da 'yan bindiga suka sace a yankin na Bena. Amma bai amsa kiraye-kirayen da muka yi masa, da saƙon da muka aika masa a rubuce ta waya ba.

  3. NNPCL bai ba mu izinin bai wa dillalai mai ba - Ɗangote

    Matatar Ɗangote ta ce har yanzu ba ta karɓi kuɗi daga ƙungiyar dillalan mai ta Najeriya Ipman ba domin sayen tataccen mai.

    Wata sanarwa da matatar ta fitar a shafin X, ta ce ana tattaunawa da Ipman sai dai ta ce bai dace mambobin Ipman su nuna cewa suna fuskantar matsala ba wajen sayen tataccen mai daga matatarmu kasancewar "babu wata alaƙar kasuwanci ta kai tsaye da Ipman.

    A cewar matatar ta Ɗangote, cikin sanarwar da jami'inta na hulɗa da jama'a, Anthony Chiejina ya sanyawa hannu, "an biya kuɗin da ake magana a kai ta hannun kamfanin mai na NNPCL, ba wurinmu ba."

    "NNPCL ba ta amince da kuɗin ba, kuma ba ta ba mu izinin bai wa Ipman mai ba." in ji sanarwar.

    Matatar ta ce "muna son mu jaddada cewa za mu iya wadatar da Najeriya da duk albarkatun mai har da man jirgi."

    "A yanzu, muna iya fitar da tirela 2,900 na mai duk rana kuma muna fitar da albarkatun mai ta hanyar ruwa." in ji matatar Ɗangote.

  4. Kusan mutum 160 ne suka mutu a ambaliyar ruwan Sifaniya

    Gwamnatin Sifaniya ta ce har kawo yanzu ba a gano gwamman mutane ba bayan ambaliyar ruwan da ta afku a cikin makonnan.

    Kusan mutum 160 ne suka rasa ransu a ambaliyar.

    Wani minista a ƙasar Angel Victor Torres, ya ce zai yi wuya a gane irin ɓarnar da ambaliyar ta haddasa yanzu.

    Wakilin BBC a Valencia ya ce akwai tashin hankali sosai a kan wannan iftila'i da ya faru.

    Akwai wasu wuraren da ba za a iya kai wa gare su ba ma a yayin da masu aikin ceto ke ƙoƙarin kwashe motoci da ɓuraguzan ginin da suka cika titunan yankin.

    Wani jami'in hukumar agaji ta Red Cross ya bayyana cewa a yanzu haka muna ɗaya daga cikin wuraren fakewa da aka samar a birnin Valencia, a wannan wajen kaɗai akwai mutum fiye da 600.

    Firaiministan ƙasar Pedro Sanchez, ya buƙaci mutane da su zauna a gida sannan kuma su kiyaye da shawarwarin da jami'an ceto ke basu.

  5. Hotuna: Yadda shugaban Senegal ya shiga ɗakin Ka'aba da matarsa

    Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye tare da mai ɗakinsa sun ziyarci ɗakin Ka'aba bayan sauke Umrah ranar Talata.

    Hakan wata karramawa ce daga yarima mai jiran gado Mohammed bn Salman.

    An wallafa hotunan a shafin shugaban ƙasar na X. Shugaba Faye ya yi wa ƙasarsa ta Senegal addu'oin samun zaman lafiya da haɗin kai.

  6. Ko matasa na samun abubuwan da suke so a biranen Najeriya?

    Akan gudanar da Ranar Kula da Birane ta Duniya duk 31 ga watan Oktoba.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya taken ranar na wannan shekara a matsayin "jagorancin matasa game da yanayi".

    Albarkacin wannan rana, BBC ta tattauna da matasa a Najeriya domin jin ko suna samun abubuwan da suke buƙata a biranen ƙasar.

  7. 'An kama shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta a Tunisia'

    Rahotanni na cewa an kama wasu shahararru a shafukan sada zumunta a Tunisia saboda wallafa bidiyon da ake ganin ya ci da karo da tarbiyya.

    Kafafen yaɗa labarai a ƙasar sun ce ɗaya daga cikin waɗanda aka tsare na da mabiya sama da miliyan ɗaya a shafin Instagram.

    An kama matar, wadda aka fi sani da Lady Samara a intanet, kan zarge-zargen shiga ta rashin ɗa'a.

    Ma'aikatar shari'a ta Tunisia a farkon watan nan ta sanar cewa za ta ɗauki matakin shari'a kan masu amfani da shafukan sada zumunta da suke bayyana ɗabi'u na rashin ɗa'a.

    Masu suka sun ce kamen ɓangare ne na murƙushe masu sukar gwamnati.

  8. Kamala ta soki Trump kan ƙudirinsa na kare mata

    Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris, ta soki Donald Trump, kan ƙudirinsa na son kare mata ko sun ƙi ko sun so.

    Da take jawabi kafin fara yaƙin neman zaɓe a jihohin yammacin ƙasar, Ms Harris, ta bayyana kalaman abokin hamayyarta a matsayin waɗanda ba su dace ba.

    Ta ce tsohon shugaban Amurkan ya zaci cewa zai iya yanke hukunci a kan abin da ya kamata mata su yi da jikinsu.

    Shi ma Mr Trump na yaƙin neman zaɓe yau a jihohin yammacin.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi a ranar talata ta nuna cewa za a yi kankankan a zaɓen.

  9. Hotunan ɓarnar ambaliyar ruwa a Sifaniya

    Mamakon ruwan sama a Sifaniya ya yi gagarumar ɓarna a yankunan gabashin ƙasar yayin da ambaliyar ruwa ta yi gaba da gidaje da lalata gadoji da kuma tara ɓuraguzai a kan tituna.

    Ga hotunan irin ta'adin da ambaliyar ta yi.

  10. Ba za mu amince da yarjejeniyar wucin-gadi ba - Jami'in Hamas

    Wani babban jami'in Hamas ya ce ƙungiyarsu za ta yi watsi da kowanne irin tayi na yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin-gadi.

    Sanarwa da Taher al-Nunu ya fitar ta zo ne sabod rahotannin da ke cewa masu shiga tsakani na shirin yi wa Hamas ɗin tayin yarjejeniyar tsagaita wuta ta ƙasa da wata guda.

    Ana ganin ƙunshin yarjejeniyar zai iya tsawaita batun tsagaita wuta da kuma taɓo batun musayar Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su dama ƙara shigar da kayan agaji ckin Gaza.

    To sai dai Mr Al Nunu, ya ce Hamas, za ta amince da batun yarjejeniyar tsagaita wuta ta din-din din ne da dawo da mutanen da suka rasa muhallansu da ma ficewar dakarun Isra'ila kwata-kwata daga Gaza.

  11. Musk ya ƙi bayyana a kotu kan tuhumar bai wa masu zaɓe a Amurka maƙudan kuɗi

    Attajiri Elon Musk ya gaza bayyana a gaban kotu da ke Pennsylvania domin fuskantar tuhume-tuhume game da kyautar dala miliyan ɗaya gabanin zaɓen shugaban Amurka.

    A maimakon haka, lauyoyin attajirin sun nemi a mayar da shari'ar ƙarƙashin kotun tarayya wanda hakan ka iya jinkirta yanke hukunci har zuwa bayan zaɓe.

    Mista Musk ya yi wa masu zaɓe tayin kuɗi a jihohi marasa alƙibla da suka sa hannu kan takardar ƙorafi.

    Ma'aikatar shari'a ta yi gargaɗi cewa shirin na iya cin karo da dokar zaɓe. Amma kamata ya yi a zaman kotun a duba koken cewa tsarin ya saɓa dokokin cikin gida kan caca ba bisa ƙa'ida ba.

  12. Matan da aka yi wa fyaɗe a Sudan na kashe kansu - Ƙungiyoyi

    Masu fafutuka sun ce mata da dama a Sudan sun kashe kansu bayan da dakarun RSF suka yi masu yaɗe.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta faɗa wa BBC cewa akwai wasu matan da ke son kashe kansu saboda barazanar yin lalalata da su.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta zargi dakarun RSF da aikata miyagun laifuka a jihar Gezira har da kashe-kashe da kuma aikata fyaɗe.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce batun yin lalata da mata a Sudan abu ne mai taɓa zuciya.

    Ƙungiyar ta yi watsi da rahotannin. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi cewa Sudan na iya fuskantar matsalar jin ƙai mafi girma idan ba a cimma yarjejeniya tsakanin RSF da sojoji ba.

    Yaƙin da ake a ƙasar ya kashe dubban mutane tare da tilasta wa mutum miliyan 11 barin gidajensu tun soma yaƙin a Aprilun bara.

  13. Manyan alƙalai za su ajiye aiki a Mexico

    Takwas daga cikin alƙalan kotun ƙolin Mexico sun sanar da cewa za su ajiye muƙamansu a wani yunƙuri na nuna rashin amincewarsu kan matakin da majalisar ƙasar ta ɗauka na yin wasu sauye-sauye masu cike da ce-ce-ku-ce a ɓangaren shari'ar.

    Sabuwar dokar ta yi tanadin cewa dukkan alƙalan ƙasar za a riƙa zaɓarsu ne ta hanyar yin zaɓe.

    Wakilin BBC ya ce alƙalan Kotun Ƙolin sun ce ba za su shiga zaɓen farko da za a yi a watan Yunin shekara mai zuwa ba, sai dai za su kasance bisa muƙamansu har zuwa lokacin da za a yi zaɓe.

    Masu suka na ganin cewa sabon tsari zai kawo cikas ga harkar shari'a.

  14. Labarai da dumi-dumi, Majalisar tattalin arziƙi ta nemi Tinubu ya dakatar da ƙudirin gyaran haraji

    Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa a Najeriya ta ba da shawarar dakatar da ƙudirin yi wa haraji kwaskwarima da gwamnatin tarayyar ƙasar ke shirin yi.

    Mambobin majalisar National Economic Council (NEC) sun ƙunshi gwamnoni ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.

    Da yake magana da manema labarai bayan zaman majalisar a yau Alhamis, Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya ce sun yanke shawarar dakatar da ƙudirin ne bayan cecekucen da ya biyo baya "da zimmar bai wa mahukunta dama".

    A yau Alhamis ne fadar shugaban ƙasa ta ce ta aike wa majalisar dokoki ƙudirin gyaran karɓar harajin domin amincewa da shi.

  15. Waɗanda suka rasu a ambaliyar Spain sun haura 158

    A daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan ceto, hukumomi a ƙasar Sifaniya sun tabbatar da cewa aƙalla mutum 158 ne suka mutu zuwa yanzu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Efe ya ruwaito.

    Da safiyar yau Alhamis, an ruwaito cewa mutum 95 ne suka rasu, duk da cewa hukumomin ƙasar sun ca ba su tantance mutum nawa ba ne suka ɓace a sanadiyar ambaliyar.

  16. Gwamnan Kaduna ya amince da naira 72,000 mafi ƙarancin albashi

    Gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya amince da naira 72,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi ga ma'aikatan jihar.

    A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jihar, Ibraheem Musa ya fitar, ya ce ƙarin zai fara aiki daga watan Nuwamban da ke tafe.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan zai kuma samar da motocin sufuri kyauta ga ma'aikatan jihar, ta hanyar ba su motoci guda 100 masu amfani da iskar gas, domin kai su aiki, ya koma da su.

  17. Ambaliyar Spain: An ɗage wasan Real Madrid da Valencia

    Hukumar ƙwallon ƙafar Sifaniya, ta ɗage wasan da ƙungiyoyin Real Madrid da Valencia za su buga a gasar La Liga ranar Asabar, sakamakon mummunar ambaliya da ta shafi ƙasar.

    Hukumar ta kuma dakatar da duka wasan da za a buga a ƙarshen mako a yankin Valencia, yayin da aka fuskanci mummunar ambaliya a yankin.

    Cikin wasannin La Liga da aka dakatar a yankin har da wasan da za a kara tsakanin Villarreal da Rayo Vallecano.

    Hukumar ta ce ta samu ƙorafi ne daga hukumar La Liga tare da buƙatar ɗage wasannin da za a yi a yankin a ƙarshen mako, lamarin da ya sa hukumar ta amince da ɗage duka wasannan da za a yi a yankin, cikin har da waɗanda ba na La Liga ba.

  18. Za mu hana ababen hawan da ba mu da bayanansu aiki a Abuja daga 2025 - Wike

    Ministan Abuja, babban birnin Najeriya, Nyesom Wike, ya ce daga watan Janairun 2025, duka ababen hawan da ake haya da su a birnin, za su kasance jami'an 'yansanda da DSS na da cikakkun bayansu.

    Mista Wike ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin bikin raba tallafin sabbin motocin Taxi ga wasu matasa.

    Ministan ya zargi wasu masu amfani da ababen hawan da kasancewa masu yi wa 'yan bindiga leƙen asiri.

    “Mafi yawan masu tuƙa Keke Napep da masu achaɓa masu bai wa 'yan bindiga bayanai ne.''

    “Don haka daga watan Janairun sabuwar shekara, babu wanda za mu bari ya ɗauki fasinja a motarsa ba tare da samun sahalewar jami'an tsaro ba, sannan dole ya yi wa motarsa fenti'', in ji ministan.

    Ya ƙara da cewa “ba za mu bari a sake amfani da kowace irin mota wajen ɗaukar fasinja a Abuja ba''.

    ''Za mu ɗauki bayanan direba da na motarsa, kamar sunan direba da lambar motarsa da sauran muhimman bayanai'', in ji mista Wike.

  19. Rasha ta ci tarar Google kuɗin da babu su a duniya

    Wata kotun Rasha ta ci tarar kamfanin google Ondiciliyon biyu na roubles, saboda taƙaita wa kafofin yaɗa labaran ƙasar amfani da dandalin Youtube.

    Idan aka kwatanta kuɗin da dalar Amurka sun kama dala 20,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000,000.

    Duk da cewa kamfanin na Google na cikin manyan kamfanoni mafiya arziki a duniya, wannan kuɗi sun zarta arzikinsa da aka ƙiyasta da dala tiriliyan biyu.

    A taƙaice wannan kuɗi sun zarta gaba ɗayan arzikin duniya, da IMF ya ƙiyasta da dala tiriliyan 110.

    Kamfanin dillancin labaran Rasha ya ambato kakakin gwamnatin ƙasar, Dmitry Peskov, duk da cewa ba zai iya ambata wannan adadi ba, amma yana da kyau kamfanin ta ''mayar da hankali kan wannan hukunci''.

    Kawo yanzu dai kamfanin bai amsa tambayar da BBC ta yi masa kan batun ba.

  20. An kama sarauniyar kyau ta Rwanda kan zargin shan barasa lokacin tuƙi

    'Yansandan Rwanda sun kama sarauniyar kyau ta ƙasar bisa zargin shan barasa a lokacin tuƙi da kuma rashin lasisin tuƙi.

    Divine Muheto, wadda ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta ƙasar da aka gudanar a baya-bayan nan - ta shiga hannun 'yansanda bayan motar da take ciki ta daki wani gini, ita kuwa ta tsere daga wurin.

    'Yansandan sun ce ba wannan ne karon farko da aka taɓa samun matashiyar mai shekara 21 da tuƙi bayan ta sha barasa ba.

    Wata kotu a Kigali, babban birnin ƙasar ta fara sauraron ƙararta a ranar Alhamis, kamar yadda kakakin masu shigar da ƙara na ƙasar ya bayyana.

    MS Muheto ta shahara a Rwanda bayan da ta lashe gasar sarauniyar kyau da aka gudanar a 2022.