Sai da safe
Nan za mu rufe wannan shafi na rahotonni kai-tsaye na ranar Lahadi.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/07/2025.
Ahmad Bawage da Umar Mikail
Nan za mu rufe wannan shafi na rahotonni kai-tsaye na ranar Lahadi.
Mu haɗu da ku gobe da safe domin samun wasu sababbi.

Asalin hoton, X/Peter Obi
Ɗaya daga cikin manyan 'yan'adawa a Najeriya Peter Obi ya ce zai nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 domin kawo ƙarshen mulkin APC.
Da yake magana ta cikin shirin Sunday Politics na Channels TV, Obi ya ce ba su taɓa yin magana da wani ba kan cewa zai yi masa mataimaki a takarar.
"Zan yi takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, kuma ina da imanin cewa na cancanta," in ji Obi wanda ya yi wa jam'iyyar Labour Party takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Da aka tambaye shi ko zai yi takara da tare da Atiku Abubakar na PDP a matsayin mataimaki, Obi ya ce: "Babu wannan maganar. Babu wanda ya taɓa yin magana kan haka...babu wanda ya yi min magana na zamar masa A ko B ko C."
Peter Obi ya kuma tabbatar da cewa har yanzu ɗan jam'iyyar Labour ne shi duk da cewa yana cikin jam'iyyar haɗaka ta ADC da ta ƙunshi sauran jagororin adawa da za su ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu na APC a 2027.
Tinubu ya hau mulki a 2023 kuma zai nemi wa'adi na biyu kuma na ƙarshe ƙarƙashin jam'iyyarsu tasu, wadda ta fara mulki bayan doke PDP a zaɓen 2015.

Asalin hoton, FRSC
Aƙalla mutum 21 ne suka mutu sakamakon wani hatsarin mota a kan hanyar Zariya zuwa Kano a yau Lahadi, kamar yadda hukumar kiyaye haɗurra ta Najeriya ta bayyana.
Hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC) ta faɗa cikin wata sanarwa cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:23 na safiya a daidai Dakatsalle.
Wata motar bas ƙirar Toyota ce ta yi karo da babbar mota ƙirar DAF, inda rahoton hukumar ya nuna cewa mai motar bas ɗin ne ya saɓa ƙa'idar tuƙi ta hanyar bin hannun da ba nasa ba.
Ta ƙara da cewa hatsarin ya jawo motar ta kama da wuta, inda akasarin mutanen suka ƙone ƙurmus.
"Mutum 24 ne hatsarin ya ritsa da su. Abin takaici 21 sun mutu, yayin da uku suka ji raunuka daban-daban, a cewar Olusegun Ogungbemide mai magana da yawun hukumar.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama wani ɗankasuwa da matarsa da 'ya'yansa mata biyu da zargin safarar ƙwaya.
National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta ce ta kama mutumin mai suna Ajah Johnson Uchenna ne bayan gudanar da bincike da kuma wasun ayyuka kafin hakan.
Kakakin NDLEA Femi Babafemi ya faɗa cikin wata sanarwa cewa 'yansandan farin kaya ne suka fara kama mutanen tun ranar 13 ga watan Yuni, amma da bincike ya tsananta sai aka sake kai samame gidansu ranar 1 ga watan Yuli a jihar Legas.
An kama su ne da ƙunshin ƙwayar skunk mai nauyin 277.5kg tun da farko, kafin a sake gano wata mai nauyin 231kg, inda daga nan ne aka mayar da su hannun NDLEA.
Mutanen da ambaliya ta kashe a jihar Texas da ke Amurka sun ƙaru zuwa 68 sakamakon ambaliyar ruwan da ta ɗaiɗaita larduna biyar.
Shugaban 'yansandan lardin Kerr, Larry L. Leitha, ya ce ana tsammanin adadin zai ƙaru.
"Zuwa yanzu mutanen da suka mutu a Kerr sun kai 59," kamar yadda ya faɗa wa gidan talabijn na Fox News.
An zaƙulo gawar sauran mutum bakwai ne a sauran lardunan da ke jihar.

Asalin hoton, @nysc360
Gwamnan jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya ya amince da ƙara yawan alawus ɗin da jihar ke bai wa matasa masu hidimar ƙasa daga N5,000 zuwa N20,000.
Ƙarin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Agustan 2025, kamar yadda Gwamna Umo Eno ya bayyana yayin jawabin da ya gabatar ranar Juma'a a fadar gwamnatin jihar.
Ya ce sun ɗauki matakin ne da zimmar ƙara taimaka wa 'yan hidimar ƙasar bayan gwamnatin tarayya ta mayar da alawus ɗin N77,000 daga N33,000 a kwanan nan.
"Akwai 'yan hidimar ƙasa fiye da 10,000 da akan turo jihar Akwa Ibom duk shekara, ya kamata mu ci gaba da taimakawa da kuma ƙarfafa musu gwiwa," in ji gwamnan.

Asalin hoton, Nuhu Ribadu/X
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce Najeriya na cikin wani mawuyacin hali a shekarar 2022, sakamakon fuskantar matsaloli da dama da ke barazana ga haɗin-kai, ɗorewar zaman lafiya da kuma makomarta har sai da shugaba Bola Tinubu ya zo ya cece ta bayan hawa mulki a shekarar 2023.
Ribadu ya bayyana haka ne a wani jawabi a taron kwalejin horas da sojoji ta Najeriya, inda ya bayyana lamarin da mai muni - inda sassan ƙasar duka suka shiga cikin matsalolin rashin tsaro.
Ya ce kafin zuwan Tinubu kan mulki matsaloli sun dabaibaye ƙasar - kama daga ayyukan masu ta da ƙayar-baya a arewa maso gabas sai kuma matsalar ƴanbindiga a arewa maso yamma, ta da zaune tsaye a yankin Neja Delta da kuma masu fafutukar ɓallewa a kudu maso gabashin ƙasar.
Ribadu ya ƙara tabbatar da hoɓɓasar da gwamnatin Tinubu take yi wajen ganin ta magancew matsalolin tsaro da ta gada.
A cewarsa, an ɗauki tsauraran matakai wajen dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya ce ƙoƙarin da gwamnati take yi wajen yaƙi da masu ta da ƙayar-baya ya kai kashe sama da ƴan ta'adda 13,500, yayin da sama da mayakan Boko Haram da na ISWAP 124,000 haɗe da iyalansu ne suka miƙa.

Asalin hoton, Reuters
Mutanen da ambaliya ta kashe a jihar Texas da ke Amurka sun ƙaru zuwa 59, a cewar gwamnan jihar Dan Patrick.
"Zuwa yanzu mutanen da suka mutu sun kai 59 daga 51," kamar yadda ya faɗa wa gidan na Fox.
Ya kuma ce "Muna tsammanin alkaluman za su iya ƙaruwa."

Asalin hoton, ZULUM/X
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya musanta raɗe-raɗen da ake yi cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Wata sanarwa da gwamna Zulum ya fitar a shafinsa na X, ya ce wasu mutane ne kawai suka kirkiro da labarin don cimma wata manufa.
Zulum ya ce har yanzu yana nan daram cikin jam'iyyar APC.
"Mun samu labarin da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta cewa ina shirin komawa ADC tare da wasu gwamnoni biyar. Wannan labari ba shi da gaskiya, wasu ne kawai suka kirkiro shi domin janyo ruɗani.
"Har yanzu APC nake goya wa baya, da kuma ganin cigaban jihar Borno," in ji Zulum.
Don haka gwamnan ya buƙaci al'ummar jihar da su yi watsi da labarin.
A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa na Najeriya suka tabbatar da amincewa da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Texas ɗa ke Amurka ta hallaka mutum 51, ciki har da yara 15.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda ruwa ya fantsama tsakiyar jihar.
Ruwan ya malale garin Georgetown - mai nisan kilomita 45.
Wannan bidiyo ya nuna yadda ruwan kogin San Gabriel ya cika, sannan ya afka wa gidaje.

Asalin hoton, EPA
Tsohon mashawarcin shugaba Donald Trump, Elon Musk ya ce zai ƙaddamar da wata sabuwar jam’iyyar siyasa, makonni bayan sa-in-sar da ta faru tsakaninsa da shugaban na Amurka.
Hamshaƙin billoniyan, ya sanar a dandalinsa na X, cewa ya kafa jam’iyyar America Party wadda ya tallata a matsayin ƙalubale ce ga tsarin jam’iyya biyu na Republican da Dimokrat.
Sai dai babu haske kan ko hukumomin zaɓen Amurka sun yi wa jam‘iyyar rajista sannan Musk bai yi cikakken bayani game da wanda zai jagoranci jam’iyyar ba ko ma irin salon da za ta ɗauka.
Ya fara taɓo batun ƙaddamar da sabuwar jam’iyyar ne lokacin da yake takun saƙa da Shugaba Trump lamarin da ya sa ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin ta Trump.
Musk dai ya nemi jin ra’ayin ma’abota shafin X kan ko ya kamata a kafa sabuwar jam’iyya a Amurka.
A cewar wakilin BBC, kusan mutum miliyan guda ne suka bayyana ra’ayinsu, kuma cikin wannan adadi, kashi 60 sun yi na’am da batun kafa sabuwar jam’iyyar.

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi alwashin fada da duk wanda ya ce zai yi sata muddin ya zama shugaban ƙasa.
Atiku ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar masu ruwa da tsaki daga jihar Gombe da suka kai masa ziyara, karkashin jagorancin tsohon Sanata Idris Abdullahi.
Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen cin hanci a Najeriya.
"Ya isa haka, kowace ƙasa na cigaba amma ban da mu sakamakon wasu mutane kalilan da kuma rashin gwamnati na gari," in ji Atiku.
Ya ce shugabannin haɗaka karkashin inuwar jam'iyyar ADC, za su yi aiki tukuru domin kawo canji mai nagarta wanda zai inganta rayuwar ƴan Najeriya.

Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya zama babban jami’in ƙasar na farko da ya ziyarci Syria tun soma rikicin da ya janyo ƙasar ta shiga yaƙin basasa shekaru 14 da suka gabata.
Lammy ya gana da shugaban Syria Ahmad al-Sharaa watanni takwas bayan kifar da gwamnatin Assad da kuma yadda sabuwar gwamnatin ta musulunci ke ci gaba da samun iko a faɗin ƙasar.
Gwamnatin Birtaniya ta sanar da tallafin fam miliyan 94 da ɗoriya domin ayyukan jin-ƙai da kuma tallafa wa ƙoƙarin farfaɗo da Syria da ƙasashen da ke taimaka wa ƴangudun hijirar ƙasar.
Lammy ya shaida wa BBC cewa maƙasudin ziyarar tasa shi ne inganta haɗin-kai da gaskiya da adalci tare da sabuwar gwamnatin.

Asalin hoton, Gwamnatin Najeriya/X
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa domin bunƙasa harkar noma da kuma samar da abinci a Najeriya.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugaban Brazil Inacio Lula Da Silva, a daidai lokacin da ake fara taron ƙungiyar ƙasashe ta Brics karo na 17.
A cewar sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya ce wasu tsare-tsare mara kyau a baya sun taimaka wajen hana samun cigaba a ɓangaren noma a ƙasar.
Shugaban ya fada wa takwaransa na Brazil cewa tuni Najeriya ta fara aiwatar da wasu manufofi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar wanda zai yi gogayya da sauran duniya, musamman a ɓangaren noma.
Ya ƙara da cewa a shirye Najeriya take wajen kulla hulɗa da Brazil don ganin an ɗauki mataki nan take wajen ƙara bunƙasa samar da abinci.
"Za mu aiwatar da duk yarjejeniya da muka amince da Brazil, domin kawo gyara a ɓangaren kasuwanci, sufurin jiragen sama, makamashi, samar da abinci da kuma haƙar ma'adinai," in ji Tinubu.
Ya kuma ce gwamnatinsa na ƙoƙari don bunƙasa harkar kiwon dabbobi.
A nasa ɓangare, shugaba Lula ya tabbatar da cewa za a aiwatar da duk wata yarjejeniya da aka cimma da Najeriya ba tare da ɓata lokaci ba, don ganin kyautatuwar tattalin arziki da kuma hulɗa tsakanin ƙasashen biyu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, EPA
Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana gaban jama’a a karon farko tun soma yaƙi tsakanin ƙasarsa da Isra’ila, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka shaida.
Wani hoton bidiyo daga gidan talabijin na Iran ya nuna jagoran yana gaisawa da masallata a wani masallaci ranar Asabar yayin wani biki gabanin bikin Ashura na Mabiya shi’a.
Fitowa ta ƙarshe da Khamenei ya yi ita ce bayyanarsa a wani jawabi da aka naɗa a lokacin da ake tsaka da yaƙi da Isra’ila da aka soma ranar 13 ga watan Yuni wanda kuma a lokacin aka kashe manyan kwamandojin Iran da masana kimiyyar nukiliya.
Isra’ila ta ƙaddamar da wani harin ba-zata kan cibiyoyin nukiliyar Iran lamarin da yasa Iran ɗin ta mayar da martani da hare-hare ta sama kan Isra’ila.

Asalin hoton, Reuters
Isra’ila ta yanke shawarar aika wata tawaga zuwa Qatar yau Lahadi domin tattaunawa da Hamas kan shawarar baya-bayan nan ta neman tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da ƙungiyar ke tsare da su.
Ofishin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shugaban ya amince da gayyatar duk da rashin gamsuwa da sauye-sauyen da Hamas ta nema a yi wa tsarin da masu shiga tsakani daga Qatar da Amurka da Masar suka gabatar.
A raanr Juma’a ne Hamas ta ce ta gabatar da matsayarta ga shawarar tsagita wutar na tsawon wata biyu kuma a shirye take ta shiga tattaunawar.
Sai dai wani jami’in Falasɗinawa ya ce ƙungiyar ta nemi a yi gyare-gyare da ya haɗa da samun tabbacin cewa Isra’ila ba za ta ci gaba da kai farmaki ba ko da ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin ba.

Asalin hoton, Reuters
Ɗaruruwan masu aikin ceto ne aka tura domin nemo mutanen da suka ɓata a ambaliyar da ta afku a jihar Texas da ke Amurka, inda mutum 51 suka mutu - ciki har da yara 15.
Ambaliyar ta fi shafar lardin Kerr inda mutum 43 suka mutu, sannan yara 27 suka ɓace a kusa da kogin Guadalupe.
"Ana ci gaba da aiki kuma ba za a tsaya ba har sai an gano dukkan waɗanda suka ɓata," kamar yadda shugaban yankin Kerr Larry Leitha ya bayyana.
An kuma tabbatar da mutuwar mutane a wasu sassan jihar, ciki har da lardunan Travis da kuma Tom Green.
Zuwa yanzu dai an samu nasarar ceto mutum 850.
Wakilin BBC ya ce ambaliyar Ruwan ta shafe wasu tituna kuma ba a san irin ɓarnar da ruwan ya yi ba.
Ma'abota BBC Hausa barkan mu da safiyar Lahadi.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.