Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Wasanni da sharhi da kuma bayanan da suka shafi gasar cin kofin duniya 2026 da wasu batutuwan da suka shafi wasanni

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran wasannin da ake fafatwa, da sharhi da kuma bayanan da suka shafi gasar cin kofin duniya 2026 da wasu batutuwan da suka shafi wasanni

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ana sa ran James zai dawo a wasan daf da na kusa da na ƙarshe da Norway

    Ana sa ran Reece James zai dawo domin taka leda a wasan daf da na kusa da na ƙarshe da Ingila za ta fafata da Norway.

    Matsalar rashin ɗan wasan baya na hannun dama da Tuchel ke fuskanta ta ƙara tsananta bayan an bai wa Jarell Quansah jan kati a wasan da suka doke Mexico da ci 3-2 ranar Lahadi.

    Hakan na nufin ɗan wasan bayan na Bayer Leverkusen ba zai buga wasan gaba da tawagar Ingila za ta yi a Miami ba.

    James bai koma cikakken atisaye ba tukuna sakamakon raunin da ya samu a tsokar cinyarsa yayin wasansu na biyu a matakin rukuni da suka buga da Ghana, kuma bai samu buga wasannin suka yi da Panama da DR Congo da Mexico ba.

  2. Firaminista ya shiga tsakani kan taƙaddama kan lokacin fara wasan Mexico da Ingila

    Firaminista da sakataren harkokin waje sun shiga cikin jayayya kan cewa kada a dawo da lokacin fara wasan Ingila da Mexico baya - kamar yadda Fifa ta yi nazarin yin hakan ƴan kwanaki kafin wasan.

    Sir Keir Starmer ya umurci jami'ai tare da haɗin gwiwar Hukumar Kwallon Kafa ta ƙasar da su gabatar da hujjoji — cewa ya kamata a bar wasan a lokacin da aka tsara shi tun farko, kamar yadda jaridar The Sun ta ruwaito.

    Yvette Cooper ta tattauna da jakadan Birtaniya a Mexico domin neman jami'an diflomasiyyar Birtaniya su nuna rashin amincewarsu da duk wani sauyi, ta yadda magoya bayan tawagar Ingila su 3,000 da suka yi tafiya zuwa wurin ba za su rasa damar kallon wasan ba sakamakon hakan.

    An dai shirya Fifa za ta dawo da wasan baya da sa'o'i shida, saboda hasashen tsawa da aka yi.

    A ƙarshe dai, Fifa ta tsaya kan lokacin da aka shirya farawa, amma sai aka jinkirta wasan da awa ɗaya saboda rashin kyawun yanayi.

  3. Za a yi wa Henderson tiyata a hannu bayan raunin da ya ji

    Ana sa ran za a yi wa ɗan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson tiyata a wuyan hannunsa bayan da ya ji rauni yayin da yake murnar nasarar da ƙasarsa ta samu a zagayen ƴan 16 na gasar cin kofin duniya da Mexico, lamarin da ke jefa shakku kan ko zai iya taka wata rawa a sauran wasannin gasar ta bana.

    Henderson ya faɗo ne daga allon talla da ke kewaye da filin wasan Azteca da ke Mexico City bayan nasarar da Ingila ta samu da ci 3-2, kuma an fitar da shi daga filin wasa a kan gadon ɗaukar marasa lafiya.

    "Jordan [Henderson] ya faɗi kuma ya ji rauni a wuyan hannunsa. Lamarin yana da matuƙar muni," in ji Thomas Tuchel, babban kocin tawagar Ingila, ya shaida wa tashar BBC One bayan nasarar da suka samu.

    "Rauni ne mai tsanani, kuma rashin kasancewar Jordan tare da mu a yanzu bai dace da yanayin wannan dare ba. Likita ya sanar da ni cewa yana asibiti."

    Bayan wasan da aka buga ranar Litinin, wani ma'aikacin tawagar Ingila ya raka Henderson zuwa asibiti a birnin Mexico City, kuma bai koma tare da sauran ƴan wasan zuwa sansaninsu da ke Kansas City ba.

    Ana tunanin cewa ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar Brentford ɗin yana da matuƙar sha'awar ci gaba da zama tare da tawagar na tsawon lokacin zaman da za su yi a Amurka.

  4. Queiroz ya sauka daga muƙaminsa na kocin Ghana

    Carlos Queiroz ya sauka daga muƙamin kocin Ghana bayan watanni uku yana jagorantar tawagar bayan sun fice daga gasar cin kofin duniya a zagaye na ƴan 32.

    Kocin mai shekara 73 ya karɓi ragamar horas da tawagar a watan Afrilu kuma ya jagoranci tawagarsa zuwa matsayi na uku a rukunin L kafin Colombia ta doke su da ci 1-0 a zagaye na ƴan 32 na gasar cin kofin duniya.

    Tsohon kocin Manchester United ya je gasar cin kofin duniya sau biyar a jere, bayan ya jagoranci Iran da Portugal da Masar a manyan gasanni.

    Queiroz na ɗaya daga cikin kociyoyin tawagogin ƙasa biyu da suka bar muƙamansu a ranar Lahadi, inda ƙasar Jordan ma ta raba gari da babban kocinta Jamal Sellami bayan tawagar ta zo ta huɗu a Rukunin J.

    A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Queiroz ya bayyana ɗan lokacin da ya yi tare da Ghana a matsayin tafiya mai cike da "alfahari," yana mai yan wasansa sun dawo wa tawagar Black Stars kimarta a fagen wasan ƙwallon ƙafa na duniya.

    Tawagar Black Stars za ta koma fagen wasa a watan Satumba, lokacin da za a fara fafutukar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (Afcon) ta shekarar 2027.

  5. Trump ya tabbatar da cewa ya buƙaci FIFA ta sake duba hukuncin dakatar da Balogun.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa ya nemi Fifa ta sake duba hukuncin dakatarwar da aka yi wa ɗan wasan gaban Amurka Folarin Balogun na wasa ɗaya a gasar cin kofin duniya.

    Trump ya ce hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya "ta yanke shawarar da ta dace" wajen jingine hukuncin Balogun, inda ya ƙara da cewa da an aiwatar da hukuncin da hakan ya rage karsashin gasar ta bana.

    Balogun, wanda shi ne ɗan wasan tawagar Amurka da ya fi zura ƙwallaye a gasar da ake yi a yanzu, an shirya dakatar da shi ne a fafatawar da ƙasarsa za ta yi da Belgium a wasan zagaye na 16 a Seattle ranar Talata.

    Amma a daren Litinin, Fifa ta jingine hukuncin dakatarwar na wasa ɗaya na tsawon watanni 12, wanda hakan ya ba da damar a zaɓi ɗan wasan gaba mai shekaru 25.

    Da yake magana a Fadar White House ranar Litinin, Trump ya ce ya nemi Fifa ta sake duba hukuncin saboda "bai yi tunanin laifi ba ne".

    Trump ya tabbatar da cewa ya tattauna da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, amma ya ce abin da kawai ya yi shi ne neman a sake duba lamarin, tare da ƙarin bayanin cewa bai ce wa shugaban na Fifa ɗin ya jingine hukuncin dakatarwar da aka yi wa Balogun ba.

  6. Jordan henderson ya ji rauni a hannunsa yayin murnar nasarar Ingila

    Kocin Ingila Thomas Tuchel ya ce ɗan wasan tsakiya Jordan Henderson ya ji rauni a wuyan hannu yayin da yake murnar nasarar da tawagarb ƙasarsa ta samu a gasar cin kofin duniya a zagayen ƴan 16, inda suka doke Mexico.

    Henderson ya faɗo ne daga allon talla da ke kewaye da filin wasan Azteca da ke Mexico City bayan nasarar da Ingila ta samu da ci 3-2, kuma an fitar da shi daga filin wasa a kan gadon ɗaukar marasa lafiya.

    Ɗan wasan tsakiya na Brentford mai shekaru 36 ya buga minti shida ne kacal a gasar cin kofin duniya inda ya shigo a ƙarshen wasan da Ingila ta doke Panama a rukunin L.

    Wasan Ingila na gaba shi ne na matakin daf da na kusa da na ƙarshe (quarter-final) da Norway a Miami ranar Asabar.

  7. Hukumar ƙwallon ƙafar Belgium ta soki hukuncin FIFA kan Balogun

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Belgium (RBFA) ta bayyana cewa ta yi matuƙar mamakin matakin da FIFA ta ɗauka, na jingine hukuncin jan katin da aka dannawa ɗan wasan Amurka Folarin Balogun, kuma ta ce tana nazarin duka matakan da za ta iya ɗauka a matsayin martani.

    Tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ya shaida wa BBC cewa matakin da Fifa ta ɗauka na jingine hukuncin a matsayin ''rashin adalci ne".

    Folarin Balogun zai samu bugawa Amurka wasan na zagayen ƴan 16 na gasar cin kofin duniya da Belgium bayan da Fifa ta jingine hukunci da aka yi masa na dakatarwar wasa ɗaya bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sa baki cikin lamarin.

    An bai wa ɗan wasan gaba mai shekaru 25, wanda shi ne ɗan wasan gaba mafi zura ƙwallaye a gasar da ƙwallaye uku, jan kati kai tsaye saboda ƙetar da ya yi wa ɗan wasan baya na Bosnia-Herzegovina Tarik Muharemovich, yayin da masu masaukin baƙin suka lashe wasansu na ƙarshe na zagayen ƴan 32 da ci 2-0.

    Fifa ta ce za a jingine dakatarwar na tsawon shekara guda.

    Babu wani dalili da ya sa aka ɗauki matakin, sai dai ta ambaci wata doka da ta ba da damar jingine hukunci. Trump ya gode wa Fifa saboda "dakatar da babban rashin adalci" a cikin wani sakonda ya wallafa a shafinsa na dandalin Truth Social.

  8. Glasner ya zama kocin Nottingham Forest na biyar cikin shekara guda.

    Ƙungiyar Nottingham Forest ta naɗa tsohon kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner, a matsayin kociyanta na biyar cikin ƙasa da shekara guda.

    Ɗan kasar Austriyan ya iso filin wasa na City Ground ne domin maye gurbin Vitor Pereira, wanda aka kora a ranar Talata - mintuna biyu kacal kafin wa'adin wani sharaɗi na musamman a cikin kwantiraginsa ya ƙare.

    "Oliver mutum ne mai son nasara," in ji mamallakin ƙungiyar Forest, Evangelos Marinakis. "A bayyane yake cewa muna da manufa ɗaya, buri ɗaya, da kuma kishin ganin mun samu nasara ba tare da gajiyawa ba."

    An fara tattaunawa da Glasner, mai shekaru 51 - wanda ya bar Palace a ƙarshen kakar wasan da ta gabata - tun farkon wannan bazarar.

    Nuno Espirito Santo ne ya fara kakar wasan bara a matsayin kocin Forest, yayin da Ange Postecoglou da Sean Dyche da Pereira suka yi aiki tun daga watan Satumba.

    Glasner ya zama kocin Palace ne 2024 kuma ya jagorance su zuwa lashe babbar gasarsu ta farko a kakarsa ta farko - Kofin FA - kafin su lashe gasar Europa Conference League a kakar wasa ta bara.

    Sun lashe Community Shield a watan Agusta, inda suka doke Liverpool da bugun fanareti. A watan janairu ne Glasner ya ce zai bar Palace saboda yana son ya fuskanci wani sabon ƙalubale, duk da cewa an miƙa masa sabon kwantiragi.

    Glasner yana daya daga cikin kociyoyi uku kacal da suka taɓa lashe gasar Europa League da Conference League, bayan ya jagoranci Eintracht Frankfurt zuwa nasara a gasa Europa League a kakar wasa ta 2021-22.

  9. Tottenham ta kammala yarjejeniyar sayen Tonali kan fam miliyan 100 daga Newcastle

    Tottenham ta kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Newcastle, Sandro Tonali, kan kuɗin da ya karya tarihin cinikin ƙungiyar, wanda zai iya kai wa fam miliyan 100.

    Ɗan wasan mai shekaru 26 ya koma ƙungiyar ta Landan ne bayan ya shafe kaka uku tare da ƙungiyar ta Magpies.

    Da farko Newcastle ta yi watsi da tayin fam miliyan 80 da Spurs ta yi, amma daga bisani suka cimma yarjejeniyar da za ta sa su biya fam miliyan 92.5 kai-tsaye, tare da ƙarin fam miliyan 7.5 idan har aka cimma wasu sharuɗɗa na musamman. "Ina matuƙar farin cikin kasancewa a nan," in ji Tonali. "Mutane sun yi ta cewa akwai ƙungiyoyi huɗu ko biyar da ke zawarcina, amma a zahiri ƙungiya daya ce kawai.''

    Tonali ya zama ɗan wasa na biyu da spirs ta saya da maƙudan kuɗaɗe bayan ta ɗauki Mateus Fernandes daga West Ham kan farashin fam miliyan 85.

  10. Neymar ya yi ritaya daga taka leda a tawagar Brazil

    Neymar ya ce lokacinsa na laka leda a tawagar Brazil ya 'zo ƙarshe' bayan da tawagarsa ta sha kashi a hannun Norway a gasar cin kofin duniya ta 2026.

    Ɗan wasan mai shekaru 34 ya shigon wasan ne a minti na 67, a daidai lokacin da Norway ke doke Brazil da ci 2-0 , amma bai iya hana a yi waje da Selecao daga gasar ba.

    Neymar ya zura ƙwallo da gubun febariti a cikin ƙarin lokaci a wasan da aka buga a filin wasan MetLife da ke New Jersey, amma ƙwallon da ya ci bai sauya sakamakon wasan ba, wanda shi ne ya zama wasan ƙarshe da Neymar zai bugawa ƙasarsa.

    "Na yi ƙoƙari, na yi ƙoƙari. Yanzu ya ƙare. Na fara a nan, na gama a nan," in ji Neymar a wata hira da ya yi da TV Globo bayan wasan.

    Neymar ya guga wasansa na farko a tawgar Brazil a wannan filin wasa ne a watan Agusta na 2010, lokacin da ya zura ƙwallo a wasan sada zumunta a wasan da Brazil ta yi nasara kan Amurka da ci 2-0.

    Ya ci gaba da zama fitaccen ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin Brazil da ƙwallaye 80, yayin da wasanni 130 da ya buga wa ƙasarsa suka sanya shi a matsayi na biyu a jerin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallaye a tarihi bayan Cafu wanda ya buga wasanni 142.

    Neymar bai buga wa Brazil wasa ba tun shekarar 2023 sakamakon matsalolin raunuka dsa ya yi fama da su, kafin daga bisani a saka shi cikin tawagar ƙasarsa ta gasar cin kofin duniya ta 2026.

    Yana buga gasar cin kofin duniya ta huɗu - inda ya wakilci Brazil a gasannin shekarun 2014, 2018 da 2022.