Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 30/05/2024

Rahoto kai-tsaye

Badamasi Abdulkadir Mukhtar, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ƙasashen Sahel na atisayen nuna ƙarfin soji a Nijar

    Ƙasashe biyar a yankin Sahel na gudanar da atisayen soji na hadin gwiwa a yammacin jamhuriyar Nijar, wanda shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan atisayen a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula na masu iƙirarin jihadi.

    Kafar yaɗa labaran kasar ta Nijar ta bayar da rahoton cewa sama da sojoji 2,500 daga ƙasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Nijar da kuma Togo ne ke gudanar da wannan shirin.

    Hukumomin soji a Burkina Faso da Nijar da Mali na ƙara neman goyon bayan Rasha bayan korar dakarun Faransa da ta yi mulkin mallaka a Nijar daga ƙasar

    Waɗannan ƙasashe dai sun fice daga ƙungiyar Ecowas na yankin yammacin Afirka a watan Fabrairu tare da ƙulla yarjejeniyar kare juna da aka fi sani da kawancen kasashen Sahel.

    • Me ya rage wa Nijar, Mali da Burkina Faso bayan ficewa daga Ecowas?
    • Jamhuriyar Benin za ta haɗa kai da ƙasashen da aka yi juyin mulki
  2. Mun gaji bashin sama da naira biliyan 200 a jihar Rivers - Fubara

    Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji wasu ayyuka 34 da ba a kammala ba waɗanda kuɗinsu ya kai sama da naira biliyan 225.279, waɗanda suka bazu a ƙananan hukumomi 13 na jihar.

    Gwamnan ya kuma bayyana cewa, a karkashin jagorancinsa, gwamnatin jihar Ribas ta bayar da wasu sabbin ayyukan titina guda tara wadanda kudinsu ya kai naira biliyan 534.332.

    Ya bayyana rikicin siyasar da ya ɓarke tsakaninsa da ministan Abuja, Nyesome Wike cikin watanni uku da hawarsa kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, a matsayin wani mummunan alamari.

    Sai dai gwamnan ya tabbatar da cewa yanayi mafi muni ya wuce, domin gwamnatinsa ta samu nasarar kare hakkinta na gudanar da mulkin jihar tare da tabbatar da ci gabanta cikin ‘yanci da walwala, ba tare da wata tangarda ba.

    Gwamna Fubara ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani asusun gudanar da aiki da katin shaida domin bikin cika shekara guda da hawa kan mulki, wanda aka gudanar birnin Fatakwal.

    Gwamna Fubara ya yi nuni da cewa, tun bayan rikicin, abubuwa da dama sun canja a fagen siyasa, kuma ya ci gaba da tsayawa tsayin daka kan alkawarin da ya ɗauka shekara guda da ta wuce na bai wa jihar Ribas fifiko, da kare muradunta, da tabbatar da cewa al’ummar jihar sun samu rabon dimokuradiyya da shugabanci na gari.

    • Abu biyar da ke da ɗaure kai a rikicin siyasar Rivers
    • Ko Jonathan zai iya sasanta rikicin Wike da Fubara?
  3. An gano gawarwakin mutane yayin neman uba da ɗa da suka ɓace a Scotland

    An gano gawarwakin mutum biyu a wani bincike da ake yi a garin Glen Coe da ke Scotland domin neman wani uba da dansa da suka ɓata..

    'Yan sanda sun ce har yanzu ana ci gaba da gudanar da tantance gawarwakin a hukumance, amma an sanar da dangin Tom Parry mai shekaru 49 da dansa Richie mai shekaru 12, daga Cheshire, wadanda aka bayar da rahoton ɓacewarsu a yankin.

    Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike amma babu wani abin tuhuma.

    Sufeto Craig Johnstone ya ce: “damuwarmu da hankalinmu yana tare da duk wadanda abin ya shafa. Ina so in gode wa duk masu ba da agajin gaggawa da masu aikin ceton"

    Glen Coe sanannen wuri ne na baƙi.

    Uban da ɗansa na shirin komawa gida ranar Laraba bayan sun ziyarci Glen Nevis da Glen Coe na Scotland.

    'Yan sanda sun tabbatar da cewa an gano motar su a wurin ajiye motoci na Three Sisters da ke Glen Coe, inda suka tashi daga ranar Talata.

    Yanayin Glen Coe da Glen Nevis da tarihinsu ne ke jawo dubban daruruwan baƙi kowace shekara.

  4. Baƙaƙen fata uku sun maka kamfanin jirgin sama kotu kan zargin su da warin ƙashi

    Wasu baƙaƙen fata uku sun kai ƙarar kamfanin jirgin sama na American Airlines bisa zargin nuna masu tsangwama bayan an fitar da su daga jirgi na wani an lokaci, yayin da aka koka kan wani wari cikin jirgin.

    Baƙaƙen fatar uku sun ce a lokacin da suke shiga jirgi zuwa jihar New York daga filin jirgi na Phoenix da ke jihar Arizona, a ranar 5 ga watan Janairun bana, an yi ƙorafin kan warin jiki da ake ji, kuma nan take aka fitar da duk wani baƙar fata daga cikin jirgin na ɗan wani lokaci.

    Sanarwar haɗin gwiwa da mutanen suka fitar ta ce: "Kamfanin American Airlines ya fitar da mu daga cikin jirgin saboda mu baƙaƙen fata ne, an kunyata mu, kuma an ci mutumcin mu".

    Kamfanin ya ce yana bincike kan lamarin saboda zargin ya saɓa wa ƙa'idojin aikin.

    Alvin Jackson da Emmanuel Jean Joseph da kuma Xavier Veal sun yi zargin cewa bayan sun zauna a kujerunsu ne wani ma'aikacin jirgin ya bi su ɗaya bayan ɗaya, inda ya nemi su sauka, kuma a kan hanyar fita ne suka fahimci cewa an zaɓo duk baƙaƙen fatar da ke cikin jirgin ne domin fitar da su.

    Sun kuma ce sun hau jirgi daga Los Angeles, a ranar, ba tare da fuskantar irin wannan tsangwama ba.

  5. Ina cika alƙawurran da na ɗauka - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa tana cika alƙawurran da ta yi wa jama'ar ƙasar.

    Tinubu wanda ya taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 25 kan mulkin dimokuraɗiyya babu katsewa, ya kuma nemi haɗin kan al'umma domin samar da kyakkyawar ƙasa da za ta zamo abin alfahari ga ƴan baya.

    Ya kuma yi gargaɗi a kan jefa dimokuraɗiyya cikin mawuyacin hali yana mai cewa “Dole mu ci gaba da haɗa kai wajen gina ƙasarmu da kuma jaddadawa a koda yaushe, cewa ba mu da wata ƙasa da ta fi Najeriya’’.

    A wani jawabi da ya yi wa majalisar dokokin Najeriya, shugaba Tinubu ya nemi haɗin kan ƴan majalisar da ma sauran jama'ar ƙasar wajen ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnatinsa da kuma bunƙasa Najeriya.

    Shugaban Najeriyar ya kuma nemi goyon bayan majalisar wajen kammala aiki a kan kasafin kuɗin da ya gabatar mata, wanda ya ce zai taimaka wajen aiwatar da tsare-tsaren da gwamnati ke da su, masu muhimmanci ga jama'ar ƙasa.

    • Najeriya ta sauya taken ƙasa
    • Jihohin Najeriya biyar da aka fi kashe mutane bayan hawa mulkin Tinubu
  6. Isra'ila ta ƙwace iko da ɗaukacin iyakar Gaza

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙwace iko a wuraren da suka fi muhimmanci a kan iyakar Gaza da Masar, wajen da aka fi sani da mashigar Philadelphi kuma hakan na nufin ta karɓe iko a dukkan iyakar Gaza.

    Kakakin rundunar tsaron Isra'ila ya ce sun kuma tarwatsa hanyoyin ƙarƙashin ƙasa aƙalla 20, waɗanda Hamas ke amfanin dasu wajen shigar da makamai Gaza.

    Sai dai wata kafar talabijin ɗin Masar ta ruwaito wata majiya da ke musanta wannan ikirari, tana cewa Isra'ila na ƙoƙari ne domin kare kutsen da sojinta suka yi cikin birnin Rafah na kudancin Gaza.

    Wannan sanarwa na zuwa ne a lokacin da ake ƙara shiga fargaba game da halin da ake ciki a yankin.

    Kakakin rundunar tsaron Isra'ila, Rear Admiral Daniel Hagari ya ce "a ranar Laraba, dakarunmu sun ƙwace iko da mashigar Philadelphi a kan iyakar Masar da Rafah".

    Mr Hagari ya kuma shaida wa wani taron manema labarai cewa babu tabbacin ko dukkan hanyoyin ƙarƙashin kasar sun ɓulla cikin Masar ne, amma ana ci gaba da gudanar da bincike.

    A baya ma Masar ta taɓa sanar da cewa ta rusa wasu hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da suke yankin, a wani mataki na daƙile safarar makamai.

    • Me umarnin ICC na kama Netanyahu da shugabannin Hamas ke nufi?
    • Shugaba Biden ya yi watsi da buƙatar kama Firaministan Isra'ila
  7. Jam'iyyar ANC na kan gaba a samakon farko-farko na zaɓen Afirka ta Kudu

    An fara bayyana sakamakon farko-farko na zaɓen da ake yi wa kallon mafi zafi a Afirka ta Kudu tun bayan da jam'iyyar ANC ta hau kan karagar mulki shekaru 30 da suka gabata.

    Yayin da aka ƙidaya sama da kashi 11 cikin 100 na gundumomin zaɓe, jam'iyyar ANC ce ke kan gaba da kashi 43 cikin 100, sai kuma jam'iyyar Democratic Alliance (DA) da kashi 26 cikin 100.

    Jam'iyyu masu tsattsauran ra'ayi ta Economic Freedom Fighters (EFF) da jam'iyyar uMkhonto weSizwe Party (MK Party) na tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, kowannensu yana da kusan kashi 8 cikin 100 na sakamakon zaɓen na farko-farko.

    Ana sa ran kammala sanar da sakamakon zaɓen a ƙarshen mako.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa jam'iyyar ANC na iya rasa rinjayen 'yan majalisar dokokin ƙasar a karon farko cikin shekaru 30, wanda hakan zai iya tilasta mata shiga ƙawance.

    Goyon bayan da jam'iyyar ANC ke samu ya ragu saboda rashin gamsuwa da yawan cin hanci da rashawa, da laifuka, da kuma rashin aikin yi.

    Masu kaɗa kuri'a da dama dai a faɗin ƙasar sun fita rumfunan zaɓe har a cikin dare domin kaɗa kuri'arsu.

    Wani jami'in zaɓe a birnin Johannesburg ya shaida wa BBC cewa jerin masu kaɗa kuri'ar da suka fita zaɓen sun yi daidai da yawan mutanen da suka fita a zaɓen da aka gudanar a 1994 mai cike da tarihi wanda ya kai ga shugabancin Nelson Mandela.

    Duk da cewa an rufe rumfunan zabe a hukumance da karfe 9 na dare, dubbai da yawa suna jiran kada kuri'arsu.

    Hukumar zaben ta bayar da tabbacin cewa duk wanda ke kan layi za a ba shi damar kada kuri’a.

    • Manyan kalubale a zaɓen Afirka ta Kudu
    • Dattijuwar da ta zaɓi Nelson Mandela yanzu ba ta goyon bayan magadansa
  8. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na ranar Alhamis daga BBC Hausa.

    Ku biyo mu don sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.