Usyk ya zama zakaran duniya na damben ajin masu nauyi
Dan damben boksin na ƙasar Ukriane, Oleksandr Usyk ya zama zakaran duniya na ajin masu nauyi a karon farko cikin shekara 25.
Usyk ya doke Tyson Fury na Birtaniya bayan zagaye 12 a fatatawar da aka yi a birnin Riyadh na ƙasar Saudiyya.
Duk da rashin nasarar da Fury ya yi, shi ne zai samu kaso mafi tsoka na kuɗin da za a biya 'yan damben, wanda ake hasashen adadinsu zai kai dala miliyan 100.