Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 22 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Kungiyar Afenifere ta bukaci Tinubu ya bayar da umarnin kafa 'yansandan jihohi

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, KANO STATE GOCT/FACEBOOK

    Kungiyar kishin kabilar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya da ya yi amfani da ikonsa ya bayar da umarnin kafa rundunar 'yansandan jihohi da ta kananan hukumomi.

    Sakataren yada labarai na kungiyar, Jare Ajayi, ne ya fitar da sanarwar da ke dauke da kiran yau Asabar, a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Sanarwar ta ce, kungiyar ta yi kiran ne sakamakon rahotannin da ake ta samu na karin hare-haren 'yan bindiga da satar jama'a a jihohin Ogun da Edo da Ekiti da Oyo da Kogi da Zamfara da kuma Naija, abin da har wata kungiya mai bincike ta ayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin manyan kasashe da aka fi satar mutane a duniya.

    Kungiyar ta ce ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya tabbatar da kafa rundunonin 'yansandan jihohi da na kananan hukumomi ba tare da bata wani lokaci ba, ta hanyar bayar da umarni, yayin ake ci gaba da aikin yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

    Haka kuma kungiyar ta Yarabawa ta yi kira da a kakkafa na'urorin daukar hoto na tsaro da sauran kayayyakin fasaha na tabbatar da tsaro a muhimman wurare domin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar.

  2. 'Yar gwagwarmaya ta zargi jami'an tsaron Iran da lalata da mata fursunoni

    Narges Mohammadi

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yar kasar Iran wadda ta samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, Narges Mohammadi, na fuskantar wata sabuwar tuhuma bayan da ta zargi jami'an tsaro da yin lalata da fursunoni mata.

    Iyalanta sun ce za a fara shari'ar a gobe Lahadi.

    A watan da ya gabata ta aike da wani sakon murya ga magoya bayanta daga gidan yarin da take tsare a Tehran, inda ta yi Allah-wadarai da abin da ake aikatawa ga fursunoni mata.

    'Yar gwagwarmayar ta sha nuna adawa da matakin gwamnatin ƙasar na tilasta wa mata rufe kansu.

  3. Babban abokin tsohon shugaban hamayya na Rasha ya lashi takobin ci gaba da yakar Putin

    Leonid Volkov

    bokin tsohon shugaban ƴan adawa na Rasha marigayi Alexei Navalny, ya ce ba zai taɓa daina adawa da Shugaba Vladimir Putin ba, duk da harin da aka kai masa a watan Maris.

    A yayin harin da aka kai wa Leonid Volkov, a Lithuania, wanda kuma shi ne shugaban ma'aikata na Mista Navalty, an karya masa hannu.

    Ya ce ya yi amanna hakan wani saƙo ne Mista Putin ya aike masa da ke nuna za a iya cim masa a duk inda yake.

    Mista Volkov ya bayyana mutuwar Navalny da wani babban tabo, sai dai ya shaida wa BBC cewa mutuwar tasa ba za ta tafi a banza ba ba.

    Ya kuma zargi Shugaba Putin da kashe dubban mutane, da suka hada da yan hamayya da kuma yan Ukhraine.

  4. Isra'ila ta ce sojojinta sun kashe mayakan Hamas 70 a kwana daya

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hari a Gaza, sojojinta sun ce sun kashe mayaƙan Hamas sama da saba'in cikin kwana guda.

    Rahotanni na cewa aƙalla farar hula goma sha biyar ne aka kashe tare da jikkata gwammai a sansanin ƴan gudun hijira na Jabaliya, sai dai ba wata hukuma mai zaman kanta da ta tantance yawan.

    A cikin wannan makon Isra'ila ta zafafa hare-haren da take kai wa sansanin.

    A baya Isra'ilar ta sha bayyana cewa ta kammala samamenta na Jabaliya.

    A halin da ake ciki Isra'ilar na ci gaba da farmaki a Rafah da ke kudancin Gaza, inda mutane sama da rabin miliyan (500,000) suka tsere daga yankin.

  5. Mun rage ta'addancin barayin daji da kashi 70 cikin dari - Gwamnan Katsina

    Gwamna Dikko Ummaru Radda

    Asalin hoton, DIKKO RADDA/FACEBOOK

    Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage yawan ta'addancin 'yan bindiga da kashi 70 cikin dari a cikin shekara daya da ta gabata.

    Gwamnan ya ce an samu wannan nasara ne a sakamakon abin da ya kira kyakkyawan hadin kai tsakanin jami'an tsaro na sa-kai na jihar da kuma jami'an tsaro na kasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, da ya ruwaito labarai ya ce, gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Yola babban birnin jihar Adamawa, a yau Asabar a ziyarar aiki da ya kai.

    Gwamnan ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a samu 'yansandan jihohi da za a sanya su shiga yakin da ake yi da matsalar rashin tsaro a kasar.

    Gwamna Radda, wanda ya ce sun bullo da dabarar yakar barayin, ya kara bayani da cewa abin da ake gani yanzu 'yan bindigar na kai hari ne a kauyuka da yankunan da suke surkuki, inda suke kona gidaje da kashe jama'a.

  6. Mummunar ambaliya ta yi ɓarna a Italiya

    Ambakiya a Italiya

    Asalin hoton, LAPRESSE/REX/SHUTTERSTOCK

    Iska mai karfin gaske da ruwan sama kamar d bakin kwarya sun haddasa ambaliya a arewacin Italiya, inda barnar ta shafi biranen Padua da Vicenza sosai.

    Ma'aikatan agaji na can suna ta amfani da kananan kwale-kwale wajen kwashe jama'a daga gidajensu. Kuma hotunan da ake samu daga biranen na nuna yadda motoci ke ta yawo a kan ruwa.

    Gwamnan yankin Veneyo inda ambaliyar ta auku ya bayyana ruwan da iskar da aka yi da daddare kamar wani bam na ruwa.

    A halin da ake ciki kuma yankin kudancin kasar ta Italiya na fuskantar tsananin zafi inda yanayin zafin ya kai har lamba 35 a ma'aunin selshiyar a birnin Sicily.

    Masani a kan sauyin yanayi, Farfesa Marco Marani, na Jami'ar Padua, ya danganta lamarin da matsalar sauyin yanayi tare da gargadin cewa za a ci gaba da samun dumamar yanayin a duniya, saboda yadda al'amura ke gudana.

    Wani magajin gari Alberto Borsari ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara, cewa ruwa ya mamaye titun da dakunan karkashin kasa na gidaje, amma an yi sa'a ba wanda ambaliyar da lahanta.

  7. Najeriya za ta daina sayo mai daga waje a watan Yuni - Dangote

    Aliko Dangote

    Asalin hoton, X/@ALIKODANGOTE

    Matatar man Dangote da ke jihar Legas a Najeriya ta ce kasar za ta daina sayen man fetur daga waje a watan Yuni, lokacin da matatar za ta fara aiki.

    Mai matatar, Alhaji Aliko Dangote shi ne ya bayyana haka a taron kolin shugabannin kamfanoni na Afirka ranar Juma'a a Kigali, babban birnin Rwanda.

    Hamshakin attajirin ya ce, matatar za ta samar da man da ake bukata a cikin gida ba ga Najeriya ba kadai har ma da sauran kasashen yankin Afirka ta yamma.

    Dangote ya ce, a cikin watan Yuni, wato nan da mako hudu zuwa biyar, ba wani mai da Najeriya za ta rika saye daga waje.

    Bayan man fetur, ya ce matatar za ta kuma samar da isasshen man dizil ga Afirka ta yamma da ma Afirka ta tsakiya.

    Haka kuma ya ce, matatar za ta iya samar da isasshen man jirgin sama ga nahiyar Afirka gaba daya, har ma ta fitar da shi zuwa kasashen Brazil da Mexico.

    Attajirin wanda ya fi kowa kudi a Afirka ya kuma bugi kirji dacewa, nan da shekara uku zuwa hudu nahiyar Afirka ba za ta sake sayen takin zamani daga waje ba, domin matatar za ta wadata nahiyar da takin.

  8. ''An sa ran firaministan Slovakia zai samu sauƙi''

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Mataimakin firaministan Slovakia, Robert Kalinak, ya ce ana sa ran firaministan ƙasarRobert Fico ''zai samu sauƙi'' bayan ƙarin tiyatar da likitoci suka yi masa

    Robert Fico, mai shekara 59, ya samu munanan raunuka bayan harbi da wani mutum ya yi masa a garin Handlova ranar Laraba.

    Jami'ai sun ce ba zai yiwu a mayar da shi Bratislava, babban birnin ƙasar cikin kwanaki masu zuwa ba.

    An gurfanar da mutumin da ya yi yunƙurin kashe shin a gaban kotu.

    Mai magana da yawun kotun ta ce za a ci gaba da tsare shi har zuwa ƙarshen shari'ar da ake yi masa.

    Mataimakin firaministan ya ce mista Fico na samun sauƙidaga raunukan da ya ji, kuma babu buƙatar naɗa mai riƙon ƙwarya don jagorantar gwamnati

  9. Gane Mini Hanya: Tare da tsohon gwamnan Katsina Shehu Shema

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  10. Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya sun koka kan ƙarancin ayyukan gwamnatin tarayya a yankinsu

    ..

    Asalin hoton, Senator Bala A. Mohammed/X

    Ƙungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwarsu kan yadda suka ce gwamnatin tarayyar na nuna musu wariya a ɓangren ayyukan ci gaba da gwamnatin tarayya ke yi, musamman titunan mota da layin dogo da za su haɗa yankin da sauran sassan ƙasar.

    Gwamnonin - da suka haɗa na jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe - sun gudanar da taron ƙungiyar ne karo na 10 ranar Juma'a a jihar Bauchi.

    Cikin sanarwar bayan taro da gwamnonin suka fitar, sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta dubi yankinsu wajen samar da waɗannan abubuwan more rayuwa.

    Gwamnonin sun kuma nuna rashin daɗinsu kan matsalar rashin wutar lantarki da ilahirin yankin arewa maso gabas ya jima yana fama da ita, da kuma yadda kamfanin dakon lantarki na ƙasar TCN ke nuna halin ko'in kula game da batun.

    Gwmanonin sun kuma yaba da irin hadin kan da suka bai wa juna wajen ciyar da yankinsu gaba a fannoni daban-daban.

    .

    Asalin hoton, Senator Bala A. Mohammed/X

    Bayanan hoto, Gwamnonin sun gabatar da taron ƙungiyarsu karo na 10 ranar Juma'a a Bauchi
  11. Rasha ka iya zafafa hare-harenta kan Ukraine - Zelensky

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce Rasha ka iya ƙara zafafa hare-harenta a arewa maso gabashin Ukraine bayan galabar da ta samu a baya-bayan nan a kusa a birnin Kharkiv.

    Dakarun Rasha nba yunƙurin dannawa a yayin da sojojin Ukriane ke fuskantar koma baya sakamakon rashin makamai.

    Mista Zelensky ya amince cewa sojojinsa na fuskantar ƙarancin makami da ƙwarin gwiwa, yana mai cewa babu sojoji a mafi yawan sansanonin sojin yankin.

    Ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa sararin samaniyar ƙasar na fuskantar matsala, yayin da ya sake kira ga ƙawayen Ukraine su aike mata da na'urorin kare sararin samaniya da ƙarin jiragen yaƙi.

    "A yanzu muna da kashi 25 kawai na abin da muke buƙata domin kare Ukraine," in ji Mista Zelensky.

    Shugaban na Ukraine ya ce "Muna buƙatar ƙarin jiragen yaƙi, domin kare kanmu daga hare-haren Rasha''.

    A baya-bayan nan Amurka ta amince da aike wa ƙasar tallafin dala biliyan 61 ga ƙasar, ciki har da tallafin soji.

    A 'yan kwanakin nan dakarun Rasha sun tsananta hare-hare, inda suka ƙwace ƙauyuka da garuruwa masu yawa a yankin arewa maso gabashin Ukraine da ke kusa da Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine.

    Gwamnan Kharkiv, Oleg Synegubov ya ce an tilasta wa kusan mutum 10,000 barin yankunansu cikin mako guda.

  12. Mulkin Buhari ne mafi muni a tarihin Najeriya - SDP

    ..

    Asalin hoton, Buhari Sallau/X

    Shugaban jam'iyyar SDP na Najeriya, Shehu Gabam ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da ta gabata da rashin magance matsalolin Najeriya, lamarin da ya ce ya haifar wa gwamnati mai ci fusknatar tarin matsalolin tattalin arziki.

    Yayin wata hira a shirin 'Politics Today' na gidan Talbijin na Channels, Gabam ya zargi gwamnatin Buhari da gazawa wajen magance matsalolin ƙasar.

    ''Na sha faɗa a lokuta da dama cewa gwamnatin Buhari ita ce gwamnati mafi munin gwamnati da aka taɓa gani na tarihin Najeriya, mulkinsa ne ya gadar wa gwamnatin Bola Tinubu matsin tattalin arzikin da take fuskanta a yanzu'', in ji Gabam.

    Shugaban na SDP ya kuma ce gwamnatin Tinubu ta yi gaggawa wajen kawo wasu sauye-sauyen tattalin arziki a ƙasar.

    “Mun sani ya gaji matsalar tattalin arziki, haƙƙinsa ne ya lalubo hanyoyin farfaɗo da shi, amma bai kamata hanyoyi su zama masu tsauri ba, saboda ba za ka iya farfaɗo da shi a rana guda ba'', in Gabam.

    Tun bayan hawansa mulki, shugaba Tinubu ya ɗauki matakai da dama wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar, ciki har da cire talklafin man fetur da ya yi a jawabinsa na farko bayan shan rantsuwa, lamarin da masana ƙe alaƙantawa da ƙara jefa ƙasar cikin matsin rayuwa da ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki.

    Ko a watan Afrilu ma hukumar ƙididdiga ta ƙasar ta ce hauhawar farashi ya kai kashi 33.69

  13. Kwamitin malaman musulunci a Najeriya ya goyi bayan auren marayu a Neja

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Batun auren marayun ya ja hankali sosai a wannan makon

    Kwamitin malaman addinin musulunci na Najeriya ya goyi bayan auren marayu 100 da kakakin majalisar dokokin jihar Neja ya ƙuduri aniyar ɗaukar nauyi.

    Cikin wata takarda da kwamitin ya fitar, mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Malam Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa, Engr Basheer Adamu Aliyu, sun ce abin da kakakin majalisar ke shirin yi abin a yaba ne, ba na kushewa ba.

    Kwamitin ya ce duba da matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da wasu yankunan arewacin Najeriya ke fuskanta, ɗaukar nauyin aure wani nau'i ne na tallafa wa marasa ƙarfi

    ''A shekarun baya-bayan nan jihar Neja da wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya na fama da matsalar tsaro da 'yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya shafi rayuwar mutanen yankin, iyalai da dama sun rasa iyayensu, kan haka ne shugabannin al'ummar yankin ke ƙoƙarin magance musu wahalhalun da suke fuskanta ta ɓangarori daban-daban, kamar yadda kakakin majalisar dokokin Neja ya yi yunƙurin yi'', in ji sanarwar.

    ''A matsayinmu na musulmi muna ƙoƙarin yin abubuwa kamar yadda shari'a ta tanadar, su kansu 'yan matan sun zaɓi su yi aure, a maimakon su faɗa karuwanci ko a yi safararsu zuwa Turai kamar yadda wasu da ba su da hali ke yi don rage wa kansu matsin rayuwa'', kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

    Kwamitin malaman addinin musuluncin ya ce abin da ministar ta yi bai dace ba.

    ''Abin da minista ta yi nuna wariya ne da wargaza abu mai kyau da rashin ƙwarewar aiki da kuma ƙabilanci, domin kundin tsarin mulkin Najeriya ya amince da 'yancin addinin tare da amincewa ta shari'ar musulunci da ta amince da aure'', in ji sanarwar.

    A makon da ya gabata ne dai ministar mata ta Najeriya ta kai ƙarar kakakin majalisar dokokin jihar Nejan zuwa ga babban sifeton 'yan sandan ƙasar bisa zarginsa da tilasta aurar da 'yan matan da ta ce masu ƙananan shekaru ne.

    Ministar ta ce idan taimakon 'yan matan kakakin majalisar ke son yi, me zai hana ya ɗauki nauyin karatunsu, ko ya basu jari domin su tsaya da ƙafafunsu, a maimakon yi musu aure.

    To sai dai ɗan majalisar ya kare matakin da cewa taimakon yaran ya yi, yana mai cewa galibinsu marayu ne waɗansa suka rasa iyayensu sakamakon matsalar tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta.

  14. Mafi ƙarancin albashi: Gwamnati da NLC za su sake zama a mako mai zuwa

    ..

    Asalin hoton, NLC

    Kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar zai sake zama a mako mai zuwa domin ci gaba da tattauna batun mafi ƙarancin albashin ma'aikatan ƙasar, bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka fice daga tattaunawar ranar Larabar da ta gabata 15 ga watan Mayu.

    Cikin wasiƙar gayyatar da shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya aike wa mambobin kwamitin a matakan jihohi ya ce kwamitin ya amince da sauya matsayarsa kan naira 48,000 da ya ɗauka ranar Larabar.

    Wasiƙar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, da su gayyaci mambobinsu domin halartar zaman da za a yi ranar Talata 21 ga watan Mayu.

    Tun da farko dai ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, lamarin da ya sa tunaninsu da na kwamitin ya yi hannun riga.

    A nasu ɓangare, kamfanoni masu zaman kansu sun amince naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

    Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun ce sun fice daga tattaunawar ta ranar Laraba ne saboda sun fahimci cewa gwamnatin ƙasar ba da gaske ta yi ba.

  15. Ra'ayi Riga: Kan barazanar tsaro da manoma ke fuskanta a Najeriya

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  16. Ana ci gaba da jigigar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya

    ...

    Asalin hoton, Nahcon/X

    Hukumar Alhazan Najeriya, Nahcon na ci gaba da jigilar maniyyatan ƙasar zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce zuwa yau Asabar da safe jirage 12 ne ɗauke da maniyyatan ƙasar 5074 suka isa Saudiyya.

    Hukumar ta ce 11 daga cikin jiragen sun sauka ne a birnin Madina, yayin da ɗaya kuma ya sauka a Jedda.

    Nahcon ta ce daga cikin adadin maniyyatan ta suka isa ƙasa mai tsarkin 2934 maza ne, yayin da 2140 kuma mata ne.

    A makon nan ne dai hukumar Alhazqan ta fara jigilar maniyyatan ƙasar, inda aka fara da jihohin Kebbi da Bauchi da Nasarawa da Legos da kuma birnin tarayya Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    .

    Asalin hoton, Nahcon/X

  17. Kotu ta yanke wa wanda ya farmaki mijin Nancy Pelosi hukuncin shekara 30

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Amurak ta yanke wa wanda ya kai wa mijin tsohuwar kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosy, hukuncin ɗaurin shekara 30 a gidan yari.

    Kotun ta samuDavid DePape da laifin kai wa Paul Pelosi hari tare da yunƙurin garkuwa da shi a watan Nuwamban bara.

    A lokacin harin David DePape ya fasa wa Paul Pelosi mai shekara 84 kai, lamarin da ya sa ya kwashe kusan kwana shida asibiti likitoci na ba shi kulawa.

    Masu gabatar da ƙara sun buƙaci sun buƙaci Alƙalin kotun ya yanke wa DePape - wanda ke fuskantar hukuncin ɗaurin rai da rai sakamakon wasu laifuka da ake zargin ya aikata - hukuncin ɗaurin shekara 40

    Toshuwar kakakin majalisar Amurkan ta buƙaci kotun ta yanke wa maharin mijin nata dogon lokaci a gidan yari.

    Mai magana da yawunta ya ce harin ya razana iyalan Pelosy, don haka suka buƙaci maharin ya girbi abin da ya shuka.

    A cikin bidiyon da kyamarar tsaro ta ɗauka lokacin harin an ga DePape, ɗan asalin Canada - da ya shafe kusan shekara 20 a Amurka - na riƙe da guduma inda ya fasa gidan Pelosyn ya kuma shiga.

    DePape ya tambayi mijin Pelosin inda matar tasa take, wadda ita kuma alokacin ba ta gida.

    Daga nan ne kuma 'yan sanda suka garzaya gidan bayan da suka samu kiran gaggawa, inda suka tarar da maharin tare da mijin Pelosy suna ta kokawa dukkansu riƙe da gudumar.

    Bayan zuwan 'yan sanda ne kuma sai aka ga maharin ya fizge gudumar tare da duka Mr Pelosy da ita, kafin 'yan sandan su raba su tare da kama maharin.

  18. Mutumin da ake zargi da harbin firaministan Slovakia zai gurfana a kotu

    .

    Asalin hoton, .

    Nan gaba a yau ne hukumomin Slovakia za su gurfanar da mutumin - da ake zargi da yunƙurin kashe firaministan ƙasar, Robert Fico a farkon wannan mako - a gaban kotu.

    Masu gabatar da ƙara na son a tsare shi a gidan yari kafin a yi masa shari’a.

    A ranar Juma'a ne aka ƙara yi wa Mista Fico tiyata domin jinyar raunukan da ya samu sakamakon harbin da maharin ya yi masa.

    Likitoci sun ce firaministan ya ci gaba da kasancewa cikin wani mawuyacin hali sakamakon harbin da aka yi masa.

    Wannan hari ya jefa nahiyar Turai cikin mummunan fargaba, inda shugabanni ke alaƙanta tashin hankalin da yanayin siyasa da ke ƙara tabarbarewa a wasu ƙasashen nahiyar.

  19. Zuma zai ƙaddamar da sabuwar jam'iyya kwanaki kafin zaɓen Afirka ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Jacob Zuma ya mulki Afirka ta Kudu daga 2009 zuwa 2018

    Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, zai ƙaddamar da manufofin sabuwar jam’iyyarsa ƙasa da mako biyu kafin babban zaɓen kasar.

    Komawarsa fagen siyasar ƙasar, ta hanyar jam’iyyarsa ta MK, na barazanar hana jam’iyya mai mulki ta ANC samun rinjayen da take buƙata domin ci gaba da gudanar da mulki.

    Jam’iyyarsa ta ɗauki sunan wani ɓangare na jami’yyar ANC mai ɗauke da makamai da aka wargaza a baya.

    ANC dai ta nemi ta yaƙe shi a kotu amma ba ta yi nasara ba.

    To sai dai har yanzu tsohon shugaban na fuskantar ƙalubale, bayan da hukumar zaɓen ƙasa ta shigar da ƙara a kansa a gaban kotun tsarin mulkin ƙasar.

  20. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tseye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello Diginza ne fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.

    Mu je zuwa ...