Ƙasar Benin ta hana fitar da masara zuwa Nijar
Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron zabbi wanda hukumomi suka ɗora alhakin safarar su zuwa ƙasashen da ke maƙwabtaka da ita, musamman ƙasar Nijar.
Kamfanin dillancin labaran kasar ya ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan ma’aikatar sufurin jamhuriyar Nijar ta haramtawa motocin ɗaukar kaya da aka yi wa rajista a Benin jigilar kayayyakinsu.
“Ma’aikatar sufuri da kayan aiki na son sanar da duk masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ƙasashen duniya cewa an keɓe tarin kayayyakin da za su je Nijar daga tashar Lome ko kuma a ko’ina a Jamhuriyar Togo ga motocin da aka yi wa rajista a Nijar kaɗai da Togo," in ji sanarwar da aka fitar.
Nijar dai ta karkatar da akasarin kayayyakin da take shigarwa da su ƙasar Togo, sakamakon yadda alaƙar da ke tsakaninta da ƙasar Benin, mai adawa da gwamnatin mulkin soji da ta hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, ta taɓarɓare.
Nijar dai na zargin ƙasar Benin da ɗaukar nauyin sansanonin ƴan ta’adda na kasar Faransa da ke shirin hargitsa yankin Sahel, kamar yadda ta musanta.
Jamhuriyar Benin ta dakatar da fitar da man fetur a yayin da Nijar ke ci gaba da rufe iyakokinta duk da cewa an ɗage takunkumin da shugabannin kasashen yammacin Afirka suka ƙaƙaba mata kan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023.