Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 14 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na rahotonni kai-tsaye, wanda ya kawo labarai daga sassan duniya a yau Talata.

    Ku tara gobe da safe don samun wasu sababbi.

    Sunana Umar Mikail, nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Lauyoyin Trump sun yi wa Michael Cohen tambayoyi

    Lauyoyin Donald Trump sun fara yi wa tsohon lauyansa, Michael Cohen, tambayoyi a shari’ar da ake wa tsohon shugaban kasan kan aikata laifuka a birnin New York.

    Tun da farko Mista Cohen ya shaida wa kotu yadda aka gana a fadar White House inda ya ce tsohon shugaban ƙasan ya tabbatar da shirin mayar masa da kuɗaɗen da ya kashe wurin biyan wata tauraruwar finafinan batsa kuɗin toshiyar baki.

    Wakiliyar BBC ta ce da aka yi wa Cohen tambaya kan sahihancin shaidar da yake bayarwa ganin cewa sau da yawa a baya ya sha zabga ƙarya, Cohen ya ce ya yi hakan ne don ya kare Donald Trump.

    Donald Trump ya musanta aikata laifin yin karya a bayanan kasuwancinsa tare kuma da yin lalata da Stormy Daniels.

  3. Ambaliyar ruwa na ta'azzara a Brazil bayan kashe mutum 148

    Ambaliyar ruwa a kudancin Brazil na ci gaba da ta'azzara bayan da aka kwashe kwana uku ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.

    An tabbatar da mutuwar mutane 148 a faɗin jihar Rio Grande do Sul kuma aƙalla mutum 600,000 ne aka tilasta wa barin gidajensu tun lokacin da aka fara yanayi mai tsanani sama da mako biyu da suka gabata.

    Yawan ruwa a kogin Guaíba, wanda ya ratsa ta babban birnin jihar, wato Porto Alegre, ya sake ƙaruwa kuma ruwa ya mamaye yankuna da dama na birnin.

  4. Gan Allah ta zargi jami'an tsaro da kisan Fulani a jihar Sokoto

    Kungiyar Fulani ta Gan Allah Association reshen jihar Sokoto ta koka kan abin da ta ce jama’a da ‘yan sa-kai na kashe wasu daga cikin al’ummar Fulani da suke zargi da aikata fashi a jihar.

    Fulanin sun ce ‘yan sa-kan na shiga rugage da kasuwanni a kananan hukumomin Gada da Binji da Goronyo da sauran su, inda suke kama Fulani tare da yi musu kisan gilla.

    Abubakar Hassan Gada, mamba ne a kungiyar Fulani ta Gan Allah a jihar ta Sokoto, kuma ya yi wa Zubairu Ahmad karin bayani.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari hirar:

  5. Dubban masu zanga-zanga na ci gaba da yi wa majalisar Georgia tsinke

    Dubban masu zanga-zanga ne sun ci gaba da zama a wajen majalisar dokoki a Tbilisi babban birnin Georgia bayan da ƴan majalisar suka amince da wata doka kan ƙungiyoyin farar hula.

    Dokar ta tilasta wa duk wata ƙungiyar farar hula da kafofin yaɗa labarai bayyana kudaden da suke samu daga ƙasashen waje.

    An kawo ƴan sandan kwantar da tarzoma domin su tarwatsa masu zanga-zanga a wajen majalisar dokokin ƙasar, amma masu macin sun tsaya tsayin daka.

    Suna ta ci gaba da kira ga gwamnatin ƙasar ta yi murabus.

    Da take magana da BBC, Natia Seskuria - wadda a baya ta yi aiki da Kwamitin Tsaro na Georgia - ta ce babu wani karfi da za a yi amfani da shi wajen hana wannan zanga-zangar.

    "Ganin yadda mutane da yawa suka kwashe tsawon kwanaki a gaban majalisar suna bayyana cewa ba sa goyon bayan wannan doka, abin takaici ne matuka yadda gwamnati ta ki sauraron jama’arta," in ji ta.

  6. Falasɗinwa 450,000 sun tsere daga Rafah cikin mako ɗaya - MDD

    Kimanin Falasɗinawa 450,000 ne suka tsere daga Rafah a cikin mako ɗaya da ya gabata, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da rahotanni ke cewa tankokin yaƙin Isra'ila na ci gaba da nausawa zuwa birnin da ke kudancin Gaza.

    Hukumar ayyuka da agaji ta MDD a yankin Falasɗinawa ta ce "al'umma na shan wahala kuma suna cikin yunwa da fargaba".

    Sojojin Isra'ila sun ce suna ci gaba da "kakkaɓe cibiyoyin ƴan ta'adda" a gabashin birnin, inda sama da mutane miliyan ɗaya ke samun mafaka.

    Sabbin hare-haren da Isara'ila ta ƙaddamar a arewacin Gaza sun tarwatsa wasu mutanen kimanin 100,000.

  7. Yaushe za a samu sauƙin matsalar tsaro a jihar Zamfara?

  8. Yaƙin Gaza: Tattaunawar zaman lafiya ta wargaje saboda farmaki kan Rafah - Firaministan Qatar

    Firaministan Qatar ya yi gargadin cewa an samu cikas a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

    Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya ce an fara samun cigaba a ƴan makonnin nan, amma farmakin da sojojin Isra'ila suka kai a Rafah ya janyo koma-baya.

    Ya ce: "A halin yanzu mun kusa kai matakin kasa cimma matsaya, tabbas abin da ya faru a Rafah ya kawo mana cikas."

    Tun da farko Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi daya cikin biyar na al'ummar Gaza sun sake yin hijira a cikin makon da ya gabata.

    Ta ce Falasdinawa 450,000 ne suka tsere daga Rafah suna ƙoƙarin tsira da rayukansu.

  9. Labarai da dumi-dumi, Shugaba Tiunubu ya dakatar da harajin tsaron intanet

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin dakatar da harajin 0.5 na tsaron intanet - ko kuma cybersecurity levy a Turance.

    Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa manema labarai cewa an ɗauki matakin ne bayan muhawarar da majalisar zartarwa ta yi a yau Talata.

    Sai dai ya ce shugaban ya ba da umarnin a sake duba tsarin da kuma yadda za a aiwatar da shi.

    Tun a ranar 6 ga watan Mayu Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da harajin kuma ya umarci bankuna su fara karɓar kashi 0.5 cikin 100 na kuɗaɗen da 'yan ƙasa suka tura tsakanin asusan ajiya cikin mako biyu.

    • Su wane ne ba za su biya sabon harajin CBN ba?
  10. 'Yanbindiga sun kuɓutar da fursuna tare da kashe jami'an tsaro a Faransa

    Wasu mahara sun far wa motar gidan yari tare da kashe gandiroba biyu a birnin Normandy na Faransa.

    Sun kai harin ne yayin da jami'n gidan yarin ke mayar da wani fursuna ma'ajiyarsa daga kotu a yau Talata.

    Masu bincike sun bayyana sunan fursunan da Mohamed Amra, wanda aka haifa a 1994. An kama shi da laifin fashi sannan kuma ana tuhumar sa da laifin garkuwa da mutane da ya kai ga kisa.

    Abokan fursunan sun harbi jami'an tsaron da bindigogi, in ji Ministan Shari'a Eric Dupond-Moretti.

  11. 'Yanbindiga sun kashe sojojin Najeriya huɗu a jihar Katsina

    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar dakarunta a harin da 'yanbindiga suka kai wa sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

    Tun da farko rahotonni sun ce maharan sun auka wa sansanin rundunar Operation Hadarin Daji ne a ranar Lahadi, inda suka kashe sojoji biyar tare da raunata wasu 11.

    Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust kisan amma ya ce huɗu ne, ba biyar ba kamar yadda aka ruwaito tun da farko.

    "A ranar 12 ga watan Mayu, dakarun Hadarin Daji suka gamu da kwanton ɓauna biyu a ƙauyen Kuran Mota da kuma kusa da Alikere da ke ƙauyen Yarmalimai na jihar Zamfara," in ji shi kamar yadda jaridar ta ruwaito.

    Ya ƙara da cewa "duk da cewa dakarun sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen kare kansu, abin baƙin ciki an kashe sojoji huɗu daga cikinsu kuma aka jikkata uku a harin farko".

    A hari na biyu kuma, sojoji biyar ne suka jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma an ba su kulawar da ta dace bayan kai su garin Faskari, in ji shi.

  12. Maza sun fi mata mutuwa a Ghana cikin 2022 - Rahoto

    Rahoton wata kididdiga da hukumar kula da haihuwa da mutuwa ta Ghana ta gudanar ya nuna cewa kashi 60 cikin 100 na waɗanda suke mutuwa a ƙasar maza ne.

    Rahoton ya kuma nuna cewa shida daga cikin mutum 10 da suka mutu a 2022 maza ne, wanda ya yi daidai da kashi 60.3 na mace-macen da aka yi rajista da hukumar.

    Bugu da ƙari, rahoton ya dora laifin yawaitar mutuwar mazan kan hawan jini, da ciwon zuciya, da kuma cutar shanyewar ɓarin jiki.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari cikakken rahoton Fahd Adam daga Accra:

  13. Zimbabwe za ta ci gaba da amfani da dalar Amurka wajen biyan kuɗin fasfo

    'Yan kasar Zimbabwe za su ci gaba da biyan kuɗaɗen fasfo da dalar Amurka, duk da bullo da sabon kuɗi a ƙasar a watan da ya gabata, in ji mataimakin ministan kuɗi.

    David Kuda Mnangagwa ya fada a ranar Litinin cewa, akwai wata yarjejeniya da ta riga ta kasance tsakanin gwamnati da kamfanin buga fasfo na kasar Lithuania, Garsu Pasaulis, kan kudaden fasfo din da za a rika karba da dala.

    Ƙasar Zimbabwe ta ɓullo da wata sabuwar kudi kuɗi me ruwan gwal da ake kira da 'Zig', ma'ana "Zimbabwe Gold" - a kokarin daidaita tattalin arzikinta da ya durkushe.

    Sabuwar kuɗin zai maye gurbin takardar kuɗin Zimbabwe, RTGS, da ta yi asarar kashi uku cikin hudu na darajarta a bana.

    Matakin na ci gaba da karbar kuɗaden fasfo da daloli ya janyo suka a ƙasar, inda wasu 'yan kasar ta Zimbabwe suka ce hakan na nuni da rashin amincewa da sabon kudin.

    "Muddin sabuwar kuɗin Zig bai samu karɓuwa daga gwamnatin ƙasar da ƴan ƙsar, nan ba da jimawa ba zai zama ba shi da daraja," in ji fitaccen dan jarida Hopewell Chin'ono a kan shafin sada zumunta na X.

    Gwamnatin Zimbabwe dai ta ƙara kuɗin fasfo zuwa dala 200 daga dala 120 a watan Disambar bara.

  14. Garuruwa biyu a Najeriya da ake ƙauna da ƙyamar tagwaye

  15. Shugabannin Somaliya na gudanar da taro kan tsarin mulkin kasar

    A yau ne shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud zai gudanar da wani taro na gwamnatin tsakiya da na ƙasashen yankin da ake sa ran za su tattauna kan sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da kuma yaƙi da kungiyar al-Shabab.

    Shugabannin jihohin Kudu maso Yamma da Jubbaland da kuma Galmudug sun isa birnin Mogadishu don halartar taron da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Afrilu, amma kuma aka ɗage sakamakon takun sakar siyasa a kan gyaran dokar.

    Babu tabbas ko shugabannin Hirshabeelle da Puntland da suka ce sun yanke hulɗa da gwamnatin tsakiya domin nuna adawa da sauya kundin tsarin mulkin za su halarci taron.

    Ana kuma sa ran taron zai tattauna rikicin Somaliya da makwabciyarta Habasha kan yarjejeniyar tekun da ta kulla da 'yan awaren Somaliland a watan Janairu.

    Shugaba Mohamud wanda zai cika shekara biyu akan karagar mulki a gobe ya fuskanci adawa mai zafi bayan ya amince da sauye-sauyen da za su kara masa karfin iko da kuma tsawaita wa'adinsa.

  16. An kama 'riƙaƙƙun ƴan fashi' da ke yaudarar mutane a Nasarawa

    Rundunar ƴan sandan Najeriya, reshen jihar Nasarawa sun kama wani mutum biyu da ake zargi ƴan fashi da makami ne da ake kira 'One Chance' waɗanda kuma suke gudanar da harkokinsu a babbar hanyar Akwanga zuwa Keffi.

    Kakakin rundunar Ramhan Nansel ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna mutanen da ake zargi suna bayyana kansu a matsayin direbobin tasi domin ɗaukan fasinjoji, sannan su kai su wani waje tare da kwashe masu kuɗinsu da kayayyakinsu, sannan kuma su yasar da fasinjojin su kuma tsere.

    Mutanen da ake zargi sun tabbatar da aika-aikatr da suke inda suka ce sun shafe fiye da shekara 10 suna yi wa mutane fashi.

    Sun ƙara da cewa ko a baya-bayan nan an sako su daga gidan gyaran hali na Shendam a jihar Filato saboda aikata makamancin wannan laifin bayan da suka kammala hukuncin da aka yanke masu.

    Kayan da aka gano a hannunsu akwai mota ƙirar Toyota da wata adda da guduma.

    Kwamishinan ƴan sanda na jihar ta Nasarawa Umar Shehu Nadada ya bayar da umarnin a gurfanar da mutanen biyu gaban kotu da zarar an kammala bincike.

    Ya kuma bai wa jama'a tabbaci cewa rundunar za ta ci gaba da aikin kakkaɓe miyagun laifuka a jihar, yana mai neman haɗin kansu wajen cimma ƙudirin.

  17. Adadin marasa aikin yi a Afirka ta Kudu ya ƙaru

    Hukumar ƙididdiga ta ƙasar Afrika ta Kudu ta sanar makonni biyu kafin zaɓe cewa adadin marasa aikin yi a ƙasar ya karu zuwa kashi 32.9 cikin 100 a rubu'in farko na shekarar.

    Hakan na nuna haɓakar kaso 0.8 daga kwata na ƙarshe na shekarar 2023.

    Afirka ta Kudu tana ɗaya daga cikin mafi yawan marasa aikin yi a duniya.

    Ɗaya daga cikin biyu na matasan Afirka ta Kudu ba shi da aikin yi kuma kashi 60 cikin 100 na rayuwa a ƙasa da talauci.

    Rashin aikin da cin hanci da rashawa da kuma rashin daidaiton tattalin arziki na daga cikin batutuwan da suka mamaye zaɓen da za a gudanar.

    Masu kada kuri'a dai na ci gaba da sukar lamirin yadda jam'iyyar ANC mai mulkin kasar ta gudanar da harkokin tattalin arzikin kasar, tun bayan kawo karshen mulkin farar fata a shekarar 1994.

    Wasu rumfunan zabe sun nuna jam'iyyar za ta iya samun kasa da kashi 50 cikin 100 a karon farko na kuri'un da za a kaɗa nan da makonni biyu.

  18. Mutanen da baƙuwar cuta ta yi ajalinsu a Zamfara sun kai 13

    Adadin mutane da suka mutu sakamakon wata baƙuwar cuta da ta fi shafar yara da mata, a wasu yankuna na jihar Zamfara ya ƙaru zuwa 13.

    Bincike daga majiyoyin asibitoci da na gwamnati ya nuna cewa an samu mutum 505 da suka kamu da cutar a sassan ƙananan hukumomin Maradun da Shinkafi da Gusau.

    Sannan wani binciken, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya nuna cewa cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomin Isa da Zurmi a jihohin Sokoto da Zamfara.

    An gano cewa an fara gano cutara ƙauyen Tsibiri a ƙamarar hukumar Maradun cikin watan Fabarairun wannan shekarar.

    Wata majiya ta tabbatar cewa zuwa ranar Lahadi 12 ga watan Mayun 2024, mutum huɗu sun mutu, sai 228 da suka kamu da cutar da kuma marasa lafiya 10 da suke samun kulawa a cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta Shehu Shagari a Gusau.

    Haka nan, a ƙaramar hukumar Shinkafi, an gano cutar a ƙauyen Galadi a Afrilu sakamakon matsanancin ciwon ciki da zazzaɓi.

  19. Mozambique na bincike kan mutuwar jakadan Rasha

    Gwamnatin Mozambique ta ce tana aiki tare da hukumomin Rasha domin gudanar da bincike kan lamarin mutuwar jakadan Rasha Alexander Surikov kamar yadda gidan jaridar Diario de Mocambique mai zaman kansa ya ruwaito.

    "Ma'aikatar Harkokin Waje tana aiki tare da ofishin jakadancin Rasha a Maputo a cikin tsarin yarjejeniyar diflomasiyya da ofishin jakadancin Viena don bayyana yanayin da ke tattare da mutuwar Alexander Surikov, wani jakadan Rasha" in ji Ministan Harkokin Waje Jose Matsinhe.

    An tsinci gawar Surikov a gidan da yake zaune na hukuma a ranar 11 ga Mayu.

    Har yanzu ba a san musabbabin mutuwar tasa ba.

  20. Shirin sake gurfanar da Sirika kan 'badaƙalar' ₦19.4bn ya sami tsaiko

    Shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, Hadi Sirika da wani ɗan uwansa, Ahmad Sirika, a yau talata a wata sabuwar shari’ar kan badakalar kwangilar da ta kai naira biliyan 19.4 ya samu tsaiko sakamakon rashin kasancewarsu a gaban alƙali.

    Gidan talbijin na Channels TV ya ce lauyan Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa alkalin kotun, Mai shari’a Suleiman Belgore, cewa ba a sanar da tsohon ministan da dan uwansa abin da ake tuhumar su ba, a shari’ar.

    Don haka lauyan ya buƙaci a ɗage shari’ar, buƙatar da alkalin ya amince da ita.

    Daga baya alƙalin ya sanya ranar Alhamis 23 ga Mayu, 2024 a matsayin sabuwar ranar da za a gurfanar da su gaban kotu.

    Hukumar EFCC na tuhumar tsohon Ministan ne da ɗan uwansa a wannan karon, da abubuwa takwas da suka jiɓanci tsabar kuɗi har naira biliyan 19.4.

    Adadin dai an ce na wasu kwangilolin ma’aikatar sufurin jiragen sama ne daga tsohon ministan zuwa kamfanin Enginos Nigeria Limited wanda ake zargi mallakar ƙanin nasa ne.

    A makon da ya gabata ne aka gurfanar da Sirika da diyarsa Fatima da kuma sirikinsa a gaban kotu kan zargin badaƙalar naira biliyan 2.7, inda daga bisani kotu ta bayar da belinsu.