Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika da karin wasu a yau Alhamis, a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama.
Sirika, minista ne a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma an gurfanar da shi a gaban kuliya ne bisa tuhume-tuhume shida. Sauran wadanda aka gurfanar da su tare su uku akwai ‘yarsa Fatima Hadi Sirika da Jalal Sule Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, bisa laifin almundahanar kudin da suka kai Naira biliyan 2.7.
A wani bangare na binciken da hukumar EFCC ke yi kan badakalar kudi da ake zargin tsohon ministan ya aikata sun hada da bada kwangilar damfara da ma’aikatarsa ta yi a karkashin sa.
Wata majiyar EFCC ta shaida wa BBC cewa sun gayyaci tsohon ministan domin yi masa tambayoyi daga masu binciken da ke kula da badakalar kwangilar da ake zarginsa da aikatawa lokacin da yake ministan ma'aikatar sufurin jiragen sama.
Ya mutunta gayyatar kuma aka tsare shi.
An tattaro cewa hukumar EFCC ta dade tana binciken badakalar kwangilar da ake zargin ministar yana kan aiki, har ma ya gana da masu bincike kafin a tsare shi da aka yi.
Tun da farko dai an shirya gudanar da shari’ar ne a ranar Talatar da ta gabata amma saboda rokon da EFCC ta yi na gyara wasu tuhume-tuhumen, an bayar da sabuwar rana zuwa yau.
A cewar hukumar EFCC, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bai wa wani kamfani Engirios Nigeria Limited wasu manyan kwangiloli guda hudu da ake zargin yana da alaƙa da ɗan uwansa Abubakar Sirika.
Kamar yadda EFCC ta bayyana, binciken ya tabbatar da cewa an bayyana Abubakar a matsayin Darakta na Kamfanin.
An ambaci cewa shi kadai ne mai izinin sanya hannu kan asusun ajiyar kudi biyu na kamfanin.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta bayyana cewa tsohon Ministan, Hadi Sirika, ya sanya wa dan uwansa Abubakar kwangilolin, duk da sanin cewa Abubakar na rike da mukamin ma’aikacin gwamnati
-
Da gaske Hadi Sirika ya yi barazanar ɗaure Yari da Fintiri?
-
Majalisar Dattijan Najeriya ta musanta zargin almundahana kan aikin Hajji