Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, A'isha Babangida and Umar Mikail

  1. Shawarata ga matasa masu burin shiga gwamnati - Khalil Nur Khalil

    Khalil Nur Khalil, mai bai wa gwamnan jihar Katsina kan tattalin arziƙi ya fara shiga gwamnati tun yana ɗan shekara 25, kuma matashin ya samu ɗaukaka inda har ya riƙe shugabancin hukumar bunƙasa zuba jari ta jihar Kaduna a zamanin Mallam Nasir Elrufai.

  2. An kama mutum 17 da zargin hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba a Kano

    Rundunar ƴan sandan Najeriya, reshen jihar Kano ta kai wani samame kan kasuwar ƴan canji ta Wapa inda ta kama mutum 29 da ake zargi da gudanar da hada-hadar musayar kuɗin waje ba bisa ƙa'ida ba.

    Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.

    Sanarwar ta ce rundunar ta kai samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'ai daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

    A cewar kakakin, mutum 12 cikin mutanen da aka kama daga bisa an sake su bayan da aka gaza gano hujjar da ta tabbatar suna gudanar da hada-hadar ba bisa ƙa'ida ba sai kuma ragowar 17 da aka gano kuɗin CFA kimanin dubu 68 sai kuɗin Rupees 30.

    Ƙarin binciken da aka yi ya nuna mutanen 17 da ake zargi suna aiki ne ƙarƙashin wani kamfanin ƴan canji da ba shi da rajista kuma za a gurfanar da su gaban kotu.

    Rundunar ta ce tana kai samamen ne domin murƙushe masu hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa'ida ba da nufin tsaftace kasuwar musayar kuɗi a Najeriya sannan rangadin bai shafi ƴan canjin da ke gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka.

    • Yadda sabbin ƙa’idojin CBN za su shafi kasuwar canjin kuɗi
  3. Tinubu ya koma Najeriya bayan ziyara zuwa Netherlands da Saudiyya

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya koma gida Najeriya daga bulaguron da ya yi a Turai, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana.

    Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, wanda ya yi sanarwar a shafinsa na X, ya yi wa Tinubu maraba da komawa gida.

    Ya wallafa "maraba da shugaban ƙasa!," kamar yadda ya rubuta.

    Shugaba Tinubu ya yi tafiya zuwa Netherlands inda ya gana da Firaiministan ƙasar Mark Rutte, mako biyu da suka gabata, daga nan kuma ya je Saudiyya domin halartar taron taron tattalin arziki na duniya.

    Daga nan kuma ya yi bulaguro zuwa Turai bayan taron na WEF.

    A ranar 22 ga watan Afrilu ne shugaba Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa Netherlands.

    An yi tunanin shugaban zai koma Najeriya bayan taron da ya halarta a Saudiyya sai dai bai koma ba, lamarin da ya janyo cece-kuce game da inda shugaban yake.

  4. An ruɓanya tsaro a yankunan da ke fama da ambaliya a Brazil

    Gwamnan jihar Rio Grande do Sul a Brazil ya sanar da tura karin 'yan sanda dubu daya domin dakile sata da aikata miyagun laifuka a yankunan da ambaliya ta daidaita.

    Aklla mutane 95 ambaliyyar ta hallaka sannan gwammai sun bata.

    Sai dai Masu aikin ceto na fuskantar kalubale sakamakon ayyukan kungiyoyin daba da ke dakatar da su.

    'Yan daban na kai hari kan masu aikin agaji da sace musu takalma da wawushe kayayyakin gidajen da ambaliyar taci.

    Wata mazauniyar yankin kenan take bayyana girman muni iftila'in da yadda dubban gidajen da suka lalace.

    Gwamna Eduardo Leite, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kai musu dauki.

  5. Barka da hantsi!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, assalamu alaikum. Da fatan mun wayi gari a wannan rana ta Laraba - tabawa ranar samu.

    Kamar yadda muka saba, za mu kawo muku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Instagram inda a nan ma akwai ƙarin labaran da za ku iya karantawa har ma da bidiyo da za ku iya kalla.