Ma'aikatan agaji a Afrika ta Kudu sun dukufa wajen lalubo mutanen da ke da sauran numfashi bayan da wani gini mai hawa biyar da ake ginawa ya ruguje, lamarin da ya halaka mutum biyar, sai wasu 50 da suka maƙale.
Jami'ai a birnin George, da ke lardin Western Cape sun ce mutum 24 aka zaƙulo daga ɓuraguzai kuma an kai su asibiti.
Wasu ma'aikata 75 na wurin lokacin da ginin ya ruguje ranar Litinin.
Ana gudanar da bincike kan musabbabin da ya janyo haɗarin.
Jami'an bayar da agajin gaggawa sun yi hanzarin zuwa wurin bayan ginin ya rufta da ƙarfe 12:09 agogon GMT.
Biyu cikin 22 da aka zaƙulo daga ɓuraguzai sun mutu sakamakon raunin da suka ji. An kuma ba da rahoton mutuwar ƙarin mutum uku.
"Muna tare da iyalai da duka waɗanda hatsarin ya shafa," in ji magajin garin George Ald Van Wyk.
Masu aikin ceto fiye da 100 ne tafe da karnukan farauta suka shafe dare suna aiki domin gano mutanen da suka maƙale cikin ɓuraguzai.
Jami'ai sun ce sun yi nasarar ji daga mutanen da suka maƙale cikin ɓuraguzan gini.
-
An rushe rabin gine-ginen Gaza - Binciken BBC
-
Wa zai kai wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu?