Gwamnonin Arewa na ganawa a Kaduna
Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun hallara a jihar Kaduna inda suke wata ganawa.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya a jawabin da ya gabatar, ya miƙa saƙon jaje ga al'umomin jihar Kaduna da Katsina da Nijar da Filato da Zamfara saboda ƙalubalen tsaro da suka fuskanta a baya-bayan nan.
A cewarsa, tsaro na daga cikin abubuwan da taron ya fi mayar da hankali a kai inda yace tun bayan taron da suka yi a baya, sun gana da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro da hafsoshin tsaro da gamayyar ƙungiyar farar hula a arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da hanyar tabbatar da zaman lafiya da daidaito a yankin.
"Yayin da ƙasar ke ci gaba da tattauna batun ƴansandan jiha, yana da muhimmanci mu fara duba tsarin samar da ƴansandan jihohi da aka gina kan tubalin haɗin kai tsakanin jihohin arewa." in ji shugaban ƙungiyar.
Gwamna Inuwa Yahaya ya ƙara da cewa samar da bunƙasar tattalin arziki abu ne "mai muhimmanci ga yankinmu" kuma "muna ganin samar da ci gaban tattalin arziki malsaha ce mai ɗorewa ga ƙalubalen tsaron da muke fuskanta."
Ya bayyana cewa farfaɗo da kamfanin bunƙasa Najeriya, NNDC na daga cikin manyan abubuwan da suka shafi tattalin arzikin yankin arewa.
Game da batun ilimi, shugaban ƙungiyar ta gwamnonin arewa ya ce abin damuwa ne a ce yankin arewa a yanzu yana da mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya, abin da ya ce ya zama dole a ɗauki mataki a kai.
Gwamna Yahaya ya kuma bayyana muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnonin yankin musamman ta ɓangaren samar da abubuwan more rayuwa da samar da harkokin kasuwanci da tsaro da musayar abubuwan al'ada.
Yankin arewacin Najeriya na fama da tarin matsaloli da dama da suka shafi tsaro da talauci.
Matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ta zama ruwan dare a yankin.