Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi and Umar Mikail

  1. Ana ƙoƙarin bin hanyar diflomasiya domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza

    An sake dawo da ƙoƙarin bin hanyar diflomasiya domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza, inda ake sa rai wakilai daga Hamas za su ci gaba da tattaunawa a birnin Alƙahira na Masar.

    An rawaito wani babban kwamandan Hamas na cewa basu da matsala da sabon daftarin yarjejeniyar da Isra'ila ta gabatar kan tsagaita wuta da sakin fursunoni.

    Sai dai babu alamar da ke nuna za a cimma daidaituwar.

    Rahotanni na cewa sabbin bayanan yarjejeniyar sun ƙunshi dawo da kwanciyar hankali a Gaza, wanda tabbas za su dadaɗa wa Hamas.

    Mataimakin kakakin majalisar Isra'ila Moshe Tur- Paz, ya nuna cewa abin da ya kamata a fi bai wa fifiko a yanzu shi ne dawo da mutanensu da ke garƙame gida.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya je Saudiyya, inda shi ma yake tattaunawa da shugabannin Larabawa kan yiwuwar cimma yarjejeniya.

  2. Assalamu Alaikum!

    Masu bibiyar mu barkan ku da warhaka. Barka da sake haɗuwa da ku a shafinmu da kai tsaye.

    Muna kawo maku bayanan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku kasance da mu a wannan rana ta Litinin - tushen aiki domin ci gaba da kawo muku bayanai kai tsaye.