Likitoci na ci gaba da yajin aiki a Kenya bayan gaza cimma matsaya da gwamnati
Tattaunawa tsakanin gwamnatin Kenya da likitoci masu yajin aiki ta gamu da cikas abin da ke ƙara jefa rayuwar ƴan ƙasar da ke neman magani a asibitocin gwamnati cikin garari.
Yajin aikin da gamayyar ƙungiyar likitoci ta tsunduma tun wata biyu baya kan rashin biyansu kuɗi da gaza ɗaukan likitoci masu neman horo.
Jami'an ƙungiyar sun gaza halartar wani muhimmin taro ranar Talata wanda shugaban ma'aikatan ƙasar, Felix Koskei ya kira bayan shafe kwanaki ana tattaunawa.
Bayan taron majalisar zartaswa da shugaba William Ruto ya jagoranta, gwamnati ta ce an biya buƙatun likitocin ban da rashin jituwar da suke da ita game da likitoci masu neman horo.
Gwamnatin ta ce ba za ta iya biyan likitoci masu neman horo dala 1,500 ba. Ta dage cewa za ta iya biyan dala 520 duk wata ga likitocin.
Ƙungiyar likitocin ta yi fatali da tayin su koma aiki inda ta ce dole ne a biya likitocin masu neman horo abin da suka nema.
Mista Koskei ya zargi likitocin da bijirewa umarnin kotu da kuma rashin mutunta yarjeniyoyin da aka cimma yayin taron.
Likitocin da ke yajin aiki na son gwamnatin Kenya ta inganta walwalarsu da sauran buƙatu.