Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Kotu ta ce EFCC ta ci gaba da tsare Emefiele

    Babbar kotu a Ikeja da ke jihar Legas ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

    Za a ci gaba da tsare Emefiele a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa har zuwa ranar 11 ga watan Afrilu da kotu za ta yanke hukunci kan ba shi beli.

    Tun farko da ya bayyana a kotun, tsohon gwamnan babban bankin Najeriyar ya musanta sabbin tuhume-tuhumen da ake masa na karya dokokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen waje da hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa arzikin ƙasa take masa.

    EFCC ta zargi Emefiele da ware wasu kuɗaɗen waje kusan dala biliyan biyu ba tare da bin ka'ida ba.

    Wannan na cikin tuhume-tuhume 26 da ake masa a ƙarar da aka gabatar gaban babbar kotun da ke Ikeja.

    Matakin ya ƙara ta'azzara taƙaddamar shari'a tsakanin EFCC da tsohon gwamnan babban bankin wanda kuma yake fuskantar tuhuma kan almundahana da rashawa da haɗa baki wajen aikata laifi a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Emefiele, wanda ya bayyana gaban babbar kotu a Legas karƙashin mai shari'a Rahman Oshodi, ya musanta aikata zarge-zargen da ake masa.

    An karanto masa tuhume-tuhume 26 da ake masa da wanda ake kararsu tare Henry Omoile.

    Dukkansu sun musanta zarge-zargen da ake masu.

    Sun kuma nemi kotu ta bayar da su beli zuwa lokacin da za a saurari ƙara.

    Lauyan Emefiele, Lebi Lawal ya ce ya kamata kotu ta duba matsayin wanda yake karewa.

    A cewar lauyan, "tsawon shekara tara, Emefiele ne ma'aikacin banki na ɗaya a Najeriya.

    Lauyan ya kuma roƙi kotu ta sake nazari kan ɗabi'un Emefiele tun bayan kama shi.

    Bayan hawansa kan mulki ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele daga shugabancin babban bankin ƙasar.

    Makonni bayan dakatar da shi ne kuma aka kama shi tare da gurfanar da shi gaban shari'a a watan Nuwamba kan zarge-zargen almundahana.

    • Abin da ya kamata ku sani game da kama gwamnan CBN Emefiele
  2. Yadda sojin Najeriya suka kashe ƴan bindigar da suka addabi jihohin arewa

    Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta halaka gomman ƴan bindiga a jihohin Katsina da Zamfara da Borno, a wasu jerin hare-hare da ta kai a baya bayan nan.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin saman ta Najeriya Air Vice Marshal Edwin Gabkwet ya fitar ya ce cikin wuraren da suka lalata a yayin kai harin har da wani wuri da yan bindigar ke amfani da shi wajen ajiye makamai.

    Ga ƙarin bayani cikin rahoton Khalifa Shehu Dokaji.

  3. Falasɗinawa na komawa Khan Younis yayin da Isra'ila ta janye dakarunta

    Falasɗinawa sun fara komawa gidajensu da yaƙi ya rugurguza a birnin Khan Younis da ke gabashin Gaza bayan da dakarun Isra'ila suka janye daga yankin.

    Farmakin da sojojin Isra'ila suka kai ta ƙasa ya dagargaza gine-ginen yankin.

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin sun bar yankin ne domin sake ɗauro sabuwar damarar yaƙar Hamas a Khan Younis ɗin da Rafah, inda Falasɗinawa sama da miliyan ke gudun hijira.

  4. An kama wasu ƴan Najeriya kan zargin tilasta wa ɗan Australiya tura masu hotuna

    An kama mutum biyu a Najeriya saboda zarginsu da yunƙurin lalata da wani ɗalibi ɗan Australiya da ya halaka kansa.

    Ƴan sandan Australiya sun ce matashin da aka kashe ya yi musayar hotuna da wani mutum ta intanet kafin ya soma yin baraza da kuma neman kuɗi a hannunsa.

    Bayan wani bincike da aka yi, an gano mutanen biyu da ake zargi a Najeriya inda za su fuskanci shari'a.

    Ƴan sanda sun ce ɗabi'ar tilastawa mutum tura hotuna ta hanyar yin barazanar tona masa asiri musamman a tsakanin matasa na matuƙar ƙaruwa.

    Ba a fitar da bayanan yaron - shekarunsa da kuma inda yake zaune a New South Wales ba, an yi haka domin kare iyalinsa.

    Ƴan sanda a New South Wales sun ce waɗanda ake zargin suna tilasta tura masu hotunan jikin mutum ɗin matasa ne kuma sun ce sun yi barazanar tura hotunan matashin ga abokanai da kuma yan uwansa idan har ya ƙi biyansu dala 330.

    "Saƙonnin sun yi muni. Sun matsa wa yaron lamba ya biya kuɗin," in ji babban jami'in ɗan sanda da ke yaƙi da laifukan intanet, Mathew Craft, kamar yadda ya shaida wa jaridar Sydney Morning Herald.

    Yaron ya mutu ne ta hanyar kashe kansa a yammacin ranar da abin ya faru s shekarar da ta gabata.

    Ƴan sandan Australiya sun yi aiki tare da takwarorinsu a Afirka ta Kudu da Najeriya wajen zaƙulo mutanen da ake zargi da aika-aikar a Najeriya.

    An gano shaidar da ke nuna matasan biyu sun yi ƙoƙarin karɓar kuɗi a hannun mutane cikin wayoyinsu, a cewar jaridar ta SMH. An tuhume su da zargin tilasta wa yaron ɗan Australiya kwanciya da su amma ba mutuwarsa ba.

  5. Barka da Hantsi!

    Maraba da sake haɗuwa da ku a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Sai ku biyo mu domin sanin halin da duniya take ciki.