Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Girke-girken Ramadan 2024: Yadda ake haɗa kunun tapioca

    A yau Ummulkulsum wadda aka fi sani da Kulsum creations ta nuna mana yadda ake haɗa kunu ko lemun tapioca.

  3. Ba a ga watan sallah a Najeriya ba

    Kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ba a samu ganin jinjirin watan Shawwal ba a yau Litinin, 29 ga watan Ramadan.

    Wata sanarwa ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce Sarki Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya amince da rahoton kwamitin.

    Saboda haka ya yi matsaya cewa watan Ramadan zai cika kwanaki 30 kuma ranar Laraba 10 ga watan Afrilu, ita za ta kasance 1 ga watan shawwal kuma ranar sallah karama a Najeriya

    Ba wannan ne karon farko da ake yin Azumi talatin ba a Najeriya.

  4. Gwamnati ta ayyana Talata da Laraba ranakun hutun Sallah a Najeriya

    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba, wato 9 da kuma 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun ƙaramar Sallah a Najeriya.

    Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a wata sanarwa, inda ya yi wa Musulmi murnar kammala azumi da kuma zagayowar ranar Sallah ƙarama.

    Ya yi kira ga Musulmi da su kwaikwayi halayen Manzon Allah S.A.W da suka kunshi kyautatawa, nuna soyayya, hakuri da kuma zaman lafiya.

  5. Mutane uku sun mutu a wani harin kwantan bauna a Sudan ta Kudu

    Aƙalla mutane uku ne suka mutu sannan wasu biyar suka jikkata bayan da sojojin Sudan ta Kudu suka yi wa ayarin motocinsu kwanton ɓauna, kamar yadda jami’an yankin suka sanar.

    Nyinkwany Aguer Bol, mukaddashin ministan yaɗa labarai na yankin musamman na Abyei, ya bayyana harin da aka kai a Agok a ranar Lahadi, a matsayin "yunkurin kisa" da aka kaiwa wasu manyan jami'an gwamnatin Abyei.

    Ministan ƙananan hukumomi da hukumomin tabbatar da doka, da kwamishinan gundumar Rum-Amer na cikin ayarin motocin.

    Sojojin Sudan ta Kudu ba su amsa buƙatar BBC na neman jin ta bakinsu ba.

    Mista Aguer ya yi Allah wadai da lamarin kuma ya ce kasancewar sojojin Sudan ta Kudu a makarantu a Agok da kuma harin na ranar Lahadi alamu ne na shirin sojojin Sudan ta Kudu na hana wanzuwar gwamnatin Abyei.

    Sudan ta Kudu da Sudan ke gudanar da yankin Abyei, kuma dukkansu suna iƙirarin iko kan yankin a rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa tun bayan samun ƴancin kan Sudan ta kudu a shekarar 2011.

  6. NEMA ta raba wa masu buƙata ta musamman kayan masarufi a Abuja

    Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta raba wa masu buƙata ta musamman da ke zaune a Abuja kayan masarufi.

    Wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ta raba kayan ne bayan da wata gobara ta ƙona wani kauye a wajen birnin Abuja wanda yawanci masu buƙata ta musamman ne a wurin.

    Babbar darektar hukumar ce Zubaida Umar ta kaddamar da shirin raba kayan, inda ta ce sun yi haka ne domin rage wa waɗanda gobarar ta shafa raɗaɗi.

    Gobarar da ta auku a anguwar Karmojiji, ta lalata gidaje da dama tare da ɗaiɗaita mutanen yankin.

  7. Tsige ni karan tsaye ne ga dimokraɗiyya – Philip Shaibu

    Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo da aka tsige ya bayyana cewa ba a bi ƙa'ida ba a matakin da majalisar dokokin jihar ta ɗauka.

    A jawabin da ya yi ta bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X, Philip Shaibu ya yi tur da matakin inda ya ce barazana ne ga dimokradiyya.

    A cewarsa, an ɗauki matakin tsige shi saboda ƙudurinsa na son tsayawa takarar gwamna na jihar Edo a zaɓen 2024 ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

    Ya ce abin takaici ne yadda masu mulki ke murƙushe masu adawa ta hanyoyin da ba su kamata ba.

    Shaibu ya bayyana yadda duk da irin sadaukarwar da ya yi wa al'ummar jiharsa, ake masa bita da ƙullin siyasa.

    Ya kuma ce za su yi yaƙi da wannan matakin iya ƙarfinsu domin makomar al'ummar jihar Edo.

    Shaibu ya kuma ce yana da yaƙini cewa kotu za ta wanke shi tare da bankaɗo ƙarairayin da ya ce an yi masa.

  8. Isra'ila ta ce tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta kai wani muhimmin matsayi

    Isra'ila da Hamas sun bayyana ƙwarin guiwarsu bayan tattaunawr ƙarshe da aka yi da nufin tabbatar da tsagaita wuta a Gaza.

    Ministan harkokin wajen Isra'ila, Isra'ila Katz, ya ce tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira - wadda Masar da Qatar ke shiga tsakani - ta kai wani matsayi mai muhimmanci, kuma yana ƙara kyautata zaton cewa za a iya cimma nasara.

    Akwai yiyuwar cewa duk wata yarjejeniya za ta ga an sako mutanen da ake garkuwa da su a Gaza domin mayar da fursunonin Falasɗinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila.

    Duk da haka, har yanzu ba mu san ko an warware manyan abubuwan da ke kawo cikas ga yarjejeniyar ba.

    Hamas na son a tsagaita wuta na dindindin - wato a kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya- da kuma janyewar sojojin Isra'ila gaba ɗaya daga Gaza tare da barin mazauna yankin su koma yankin arewacin ƙasar.

    Ya zuwa yanzu dai mahukuntan Isra'ila sun yi watsi da waɗannan bukatu da cewa ba za a amince da su ba, suna masu cewa hakan zai bai wa Hamas damar sake farfaɗowa, sun dage kan buƙatar ƙaddamar da farmaki a Rafah domin ruguza wasu rundunonin Hamas huɗu da suke iƙirarin cewa suna riƙe birnin.

    Amma a cikin 'yan kwanakin nan sun nuna cewa za su iya sassautawa. Firayim Minista Netanyahu na fuskantar matsin lamba daga ƙasashen duniya na ganin an shawo kan rikicin, da kuma adawa da farmakin da ake shirin kaiwa a Rafah, inda Falasdinawa sama da miliyan ɗaya ke neman mafaka.

  9. Ba a ga watan sallah a Saudiyya ba

    Saudiyya ta sanar da cewa ba a ga watan Shawwal a yau Litinin ba.

    Hakan na nufin cewa Ƙaramar Sallah za ta kama ranar Laraba, 10 ga watan Afrilun 2024.

    Dama tawagar da ke duban watan ta taru don duban jaririn watan na Shawwal.

  10. Gwamnatin Nijar ta dage kan ficewar sojojin Amurka

    Hukumomin mulkin Nijar sun sake jaddada buƙatarsu na ganin cewa sojojin Amurka sun janye, lamarin da ke kawo cikas ga muradun tsaron Washington a yankin Sahel.

    A watan da ya gabata, shugaban mulkin sojan ƙasar Janar Abdourahamane Tiani ya umarci sojojin Amurka da su fice bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar soji.

    Aƙalla jami’an sojin Amurka 650 ne ke jibge a Nijar domin sa ido kan ayyukan masu iƙirarin jihadi. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata, gwamnatin Nijar ta ce ba su ci gajiyar yarjejeniyar da suka ƙulla da sojojin Amurka ba, don lamarin ya kasance 'sakiyar da babu ruwa'.

    Ta zargi Amurka da cin zarafin Nijar tare da yin katsalandan a harkokin cikin gidanta da kuma neman taka rawa a alaƙar ƙasashen waje.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka da ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon sun yi watsi da kin amincewar da Nijar ta yi na yarjejeniyar sojin, suna masu cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu.

    Da farko dai gwamnatin mulkin sojan Nijar tana da zamantakewa mai kyau da Amurka, amma ta koma Rasha bayan yanke hulda da Faransa a bara.

  11. Matsanancin zafi ya halaka fiye da mutum 100 a Mali

    Fiye da mutum 100 sun mutu a Mali saboda tsananin zafin da aka yi fama da shi a ƙasar a watan da ya gabata, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

    A makon da ya gabata ne, yanayin zafi ya kai maki 48.5 kan ma'aunin salshiyos a garin Kayes da ke kusu maso yammacin ƙasar.

    Rana ce mafi zafi a tarihin Afirka cikin watan Afrilu, a cewar masana yanayi.

    Asibitin Gabrile-Toure da ke Bamako, babban birnin ƙasar ya karbi marasa lafiya 102 da zafi ya shafe su waɗanda kuma suka mutu da isar su asibitin, in ji shafin labarai na RFI.

    Galibinsu shekarunsu ya haura 60 sannan suna fama da rashin lafiya, kamar yadda shugaban sashen allurar barci na asibitin, Djibo Mahamane Django ya shaida wa gidan rediyon Joliba.

    Wasu majiyoyi a garin sun ce sama da mutum 250 ne suka mutu cikin kwana uku.

    • Dalilin da ya sa zafi ya tsananta a wannan bazarar
    • Duniya na cikin barazanar fuskantar yanayin zafi mafi tsanani a 2024
  12. Kotu ta tura jami'in Binance gidan gyaran hali na Kuje

    Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da umarnin a tsare ɗaya daga cikin shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar ba da belinsa.

    Alƙali Emeka Nwite ne ya bayar da umarnin bayan da Gambaryan ya musanta tuhume-tuhumen halasta kuɗin haram da hukumar EFCC mai yaƙi da masuu yi wa arzikin ƙasa zangon ƙasa ke yi masa.

    An gurfanar da Gambaryan gaban alƙali Nwite kan zargin aikata laifuka biyar.

    Gambaryan ya kuma musanta tuhumar da aka yi cewa suna gudanar da harkokinsu ba tare da samun izini ba.

    An gurfanar da shi tare da kamfanin Binance da Nadeem Anjarwalla wanda ya tsere.

    Za dai a ci gaba da tsare shi har zuwa nan gaba a wannan watan na Afrilu. Ta kuma saka ranar 2 ga watan Matu domin ci gaba da shari'a.

    EFCC ta shigar da ƙarar ne kan kamfanin Binance da Gambaryan da Anjarwalla wanda ya tsere daga Najeriya ranar 22 ga watan Maris.

    • Mene ne shafin hada-hadar kudi na Binance?
  13. Gwamnati ta ƙaddamar da shirin rabon hatsi tan 42,000 a Sokoto

    Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin rarraba tan dubu 42 na hatsi ga mabuƙata a jihar Sokoto.

    Shirin wani ɓangare ne na umarnin shugaba Bola Tinubu na tallafa wa marasa galihu da abinci a halin matsin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.

    Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a shafinsa na X inda ya ce "na bi sahun gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu da abokan aikina, ministan noma da samar da abinci da ƙaramin minista Sabi Aliyu wajen ƙaddamar da rabon."

    Hukumar agaji ta ƙasar, Nema za ta sa ido kan rabon tare da taimakon hukumomin tsaro domin tabbatar da gaskiya.

    A cewar saƙon na ministan, kowace jiha a ƙasar za ta ci gajiyar shirin kuma "za mu tabbatar mun bayar da ƙarin bayani kan shirin."

    Tun farkon watan Maris ne shugaba Bola Tinubu ya bayar da amincewar a fara raba hatsin a faɗin jihohi 36 na ƙasar.

    • Wace dabara ta rage wa Tinubu game da tsadar rayuwa a Najeriya?
    • Ko shigar da abinci Najeriya zai samar da mafita ga tsadar rayuwa?
  14. Hotunan yadda daruruwan mutane suka shirya ganin kusufin rana

    Al'umma daga arewaci da kudancin Amurka da Mexico da Canada sun yi dafifi domin ganewa idanunsu yadda kusufin rana zai kasance yau Litinin.

    Kusufin rana na faruwa ne a lokacin da wata ya shiga ta cikin tsakiyar duniyar Earth ya kuma toshe duka hanyoyin hasken ranar da ke shiga kai-tsaye daga sararin saman Wata.

    Ga wasu hotuna da muka samu:

  15. Gwamna Obaseki ya zaɓi sabon mataimaki

    Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya naɗa Omobayo Marvellous Godwin a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

    Matakin ya zo bayan tsige Philip Shaibu da majalisar dokokin jihar ta yi a zaman ta na yau Litinin.

    Omobayo, mai shekara 38 ya yi karatu a fannin injiniya kuma yana da ƙwarewa a ɓangaren mai da iskar gas.

    Omobayo ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Labour a zaɓen 2023.

    Majalisar dokokin jihar ta tsige tsohon mataimakin gwamnan Edo ne saboda ƙin amsa gayyatar kwamitin mutum bakwai da ke bincikensa kan zarge-zargen aikata ba daidai ba.

  16. Likitocin Kenya sun yi watsi da kiran shugaba Ruto su janye yajin aiki

    Likitocin Kenya da ke aiki a asibitocin gwamnati sun yi alƙawarin ba za su koma bakin aiki ba duk da roƙon da shugaba William Ruto ya yi na su kawo ƙarshen yajin aikin da suka shafe makonni suna yi wanda ya jefa harkokin lafiya a ƙasar cikin wani yanayi.

    Gamayyar ƙungiyar likitocin ta tsunduma yajin aiki ranar 14 ga watan Maris saboda rashin biyansu albashinsu da ba a biya ba da kuma jan ƙafar da gwamnati take na ɗiban likitoci masu neman ƙwarewa da wasu buƙatun.

    A ranar Lahadi ne, shugaba Ruto ya yi kira ga likitocin da su sake duba matsayarsu yana mai cewa gwamnati ta gaza biyan buƙatunsu ne saboda tarin nauyin da ke kanta.

    Sai dai a martaninta, gamayyar ƙungiyar likitocin ta hannun babban sakatarenta, Davji Atellah, ya ce albashin likitoci na da muhimmanci kamar yadda albashin kowane ɗan Kenya ke da shi.

  17. CBN ya sake karya farashin dala

    Babban bankin Najeriya ya sanar da sayar da dala ga ƴan canji.

    Babban bankin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet ranar Litinin.

    Babban bankin ya ce ya shirya sayar da dala 10,000 ga kowanne kamfanin canji a kan N1101.

    Ya kuma umarci ƴan canjin da su sayar da dala kan karin da bai wuce kashi 1.5 cikin 100 kan farashin na CBN.

    Faɗuwar da darajar nairar ta dinga yi a makonnin da suka wuce ta jawo ɗaukar matakai daban-daban daga ɓangaren hukumomi ciki har da kama 'yan kasuwar canjin da jami'an tsaro suka yi a manyan birane kamar Kano, da Abuja, da Legas.

    • Ko sayar wa 'yan canji dala zai iya farfaɗo da darajar naira?
    • Wane tasiri kwamitin da Tinubu ya kafa zai yi kan matsalar tattalin arzikin Najeriya?
  18. Janyewar sojojinmu ba ta nufin yaƙi ya ƙare – Isra'ila

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana rage yawan dakarunta da aka girke a kudancin Gaza, inda ta bar runduna aya a yankin.

    Cikin wata sanarwa ranar Lahadi, rundunar ta jaddada cewa akwai wasu sojojin da za su ci gaba da gudanar da aiki a Gaza.

    Janye sojojin daga birnin da ke kudancin Gaza ya zo ne sakamakon yadda Isra'ila ke fuskantar matsin lamba daga asashen waje na ta tsagaita wuta sai dai janyewar ana gani kamar wata dabara ce a maimakon alama ta yaƙin ya zo karshe.

    Tun farko, kakakin rundunar IDF Leftenant Kanar Peter Lerner ya shaida wa BBC cewa sojojin za su fice daga yankin saboda sun kammala aiki a Khan Younis, wanda ya fuskanci hare-hare na tsawon watanni.

    "Yaƙin bai ƙare ba," kamar yadda ya ce. "Wannan raguwa ce ta dakaru amma akwai karin ayyukan da ya kamata a yi.

    "Dole mu ruguza ƙarfin Hamas a duk inda suke."

    • Halin da ake ciki a Gaza wata shida da fara yaƙi
    • BBC ta gano kurakuran rundunar sojin Isra'ila
  19. Majalisar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar

    Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu.

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito an tsige Shaibu a zaman da majalisar ta yi ranar Litinin a Benin, babban birnin Edo.

    Tsige Shaibu ya biyo amincewa da wani rahoton kwamitin mutum bakwai da alƙalin alƙalan jihar Daniel Okungbowa ya kafa domin yin bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa mataimakin gwamnan.

    A makon da ya gabata ne majalisar dokokin jihar ta Edo ta fara shirin tsige Shaibu. Ƴan majalisa 21 cikin 24 ne suka sa hannu kan takardar ƙorafin.

    Sun zargi Shaibu da yin ƙarya da kuma bayyana sirrikan gwamnatin jihar.

    A zaman da ta yi ranar Talatar da ta gabata, shugaban majalisar, Blessing Agbebaku ya shaida wa ƴan majalisa cewa wa'adin kwana bakwai da aka bai wa Shaibu ya mayar da martani ga takardar fara shirin tsige shi ya wuce.

    Tsige Shaibu na da nasaba da takun saƙar siyasa da ke tsakaninsa da ubangidansa Godwin Obaseki.

  20. Hotunan Falasɗinawa da ke komawa Khan Younis

    Sannu a hankali Falasɗinawa sun fara komawa gidajensu a Khan Younis, garin da aka ɗaiɗaita a kudancin Gaza bayan da Isra'ila ta sanar cewa ta soma janye sojojinta daga birnin.

    Ga wasu hotunan baya-bayan nan daga birnin: