Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    To jama'a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka shafe tsawon yinin yau muna kawo muku.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Shugaba Biden ya yi ƙarin bayani kan girgizar ƙasa a New York

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yi wa manema labarai karin bayani kan tattaunawar da ya yi da gwamnan jihar New Jersey bayan afkuwar girgizar kasa.

    “Yana ganin komai na karkashin kulawa, bai damu sosai kan abun ba,” in ji Biden, inda yake mayar da martani kan girgizar kasar.

    Kalamansa na zuwa ne yayin da yake shirin shiga jirgi zuwa Baltimore domin ganin tarkacen gadar Francis Scott Key wadda ta ruguje.

  3. Girke-girken Ramadan 2024: Yadda ake yin Farfesun Daddawa

    A yau Hafsat Usman wadda aka fi sani da muhafoven ta nuna mana yadda ake Farfesun Daddawa.

  4. Yadda ƴan sa kai suka addabi mazauna Maradun na jihar Zamfara

    Mazauna wasu garuruwa bakwai da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara sun zargi 'yan sa kai daga wani gari da suke makwabtaka da su da addabarsu inda suke tare su a kan hanya domin su yi musu sata ko kuma su kashe su.

    Sun ce duk kokarin da suka yi domin shawo kan matsalar ya ci -tura.

    Ga rahoton Raliya Zubairu.

  5. Girgizar ƙasa mai maki 4.8 ta afka wa birnin New York

    Girgizar kasa mai maki 4.7 ta afka wa yankuna arewacin Amurka.

    Girgizar kasar ta faru ne a birane da dama, wanda suka kunshi Boston, New York da kuma Philadelphia, a cewar hukumar lura da yanayi ta Amurka.

    Ta afku ne kilomita 64 da yamamcin birnin New York.

    An bayyana cewa rabon da a ga irin wannan girgizar kasa, an dauki kusan shekara 40.

  6. Ƴan sanda sun tarwatsa ƴan Shia a Kaduna

    An shiga ruɗani a Kaduna bayan da ƴan sanda suka yi kokarin tarwatsa mambobin kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Islamic Movement Of Nigeria da ke karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky, wadanda ke gudanar da tattakin nuna goyon baya ga al'umma Falasdinu a tsakiyar birnin.

    Bisa al'ada dai duk Juma'ar karshe ta watan Ramadan, 'yan uwa Musulmi na gudanar da tattakin domin nuna wa al'ummar Falasdinu goyon baya dangane da irin "zaluncin" suka ce kasar Isra'ila na yi musu.

    Mambobin kungiyar sun taru a kan shatale-talen Katsina da ke kan titin Ahmadu Bello Way kafin ‘yan sanda su yi kokarin tarwatsa su.

    Hakan ya janyo fargaba tsakanin mazauna birnin musamman ma wadanda suke da shaguna a kusa da hanyar.

    An ruwaito cewa da dama daga 'yan kasuwa sun rufe shagunansu domin gudun abin da zai faru.

    ‘Yan sanda a Kaduna sun ce tattakin mambobin ‘yan Shiar na yau yana a matsayin haramtacce.

    Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar ASP Mansir Hassan, ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa mambobin kungiyar sun fito da sanyin safiyar yau "rike da makamai, inda suka fara far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da sunan tattaki".

    Mansir ya ce "mambobin kungiyar sun far wa ‘yan sanda lokacin da suka yi kokarin tarwatsa su", inda ya ce har ta kai wasu daga cikin jami’ansu sun jikkata.

    Ya ce an kama wasu daga ciki da ake zargi da rike muggan makamai kuma za a gurfanar da su gaban kotu idan aka kammala bincike.

    To sai dai mabiya Sheikh Zakzaky sun musanta inda suke cewa 'yan sandan ne suka far musu da manufar hana su gudanar da tattakin nasu.

    Wanan dai ba shi ne karo na farko ba da ‘yan Shia ke gudanar da muzahara duk da haramta musu hakan da gwamnatin tarayya ta yi karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

  7. Idan aka rufe kofofin kai agaji, to na yunwa za su buɗu - Guterres

    Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce yana fatan Isra’ila za ta bunƙasa agajin da ake kai wa Gaza cikin sauri, inda ya kira yanayin da ake ciki a yankin bayan watanni shida da fara yaƙi a matsayin “bukatar agajin gaggawa”.

    “Idan ak rufe kofofin kai agaji, to kofofin yunwa ne za su buɗu. Sama da rabin al’ummar Gaza – cikin miliyan mutane – na fuskantar bala’in yunwa.

    “Ƙananan yara a Gaza na mutuwa a yau saboda karancin abinci da ruwa. Wannan abu ne da ya kamata mu kaucewa,” in ji Guterres.

    MDD ta ce aƙalla ma’aikatan agaji 196 ne aka kashe tun 7 ga watan Oktoba.

    “Muna son mu san me ya sa aka kashe su,” in ji Guterres.

  8. Wani jirgin ruwan shaƙatawa ya yi karo da jirgin dakon kaya a Afirka ta Kudu

    Wani jirgin ruwan yawon buɗe ido na kamfanin Ambassador Cruise Line na Birtaniya ya yi karo da wani jirgin ruwan dakon kaya a tashar ruwan Cape Town a Afirka ta Kudu.

    Kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa jirgin nasa da ake kira da Ambience ya sami wani hatsari da safiyar Juma'a, a cewar News24.

    Ambience ya ci karo da jirgin dakon kaya yayin da yake kokarin shiga wurin da ya ke dakowa.

    Wani mai magana da yawun kamfanin ya shaida wa News24 cewa "Ambience ya kasa jure tsananin iska mai karfi, sakamakon haka ya ci karo da jirgin ruwan dakon kayan".

    Dukkanin jiragen biyu sun samu ‘yan barna kuma babu wani ya samu rauni.

  9. Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan ƙarin kuɗin lantarki

  10. Almajirai sun dami Abidjan na ƙasar Ivory Coast

    Hukumomi a birnin Abidjan mafi girma a kasar Ivory Coast, sun sanar da haramta bara domin kokarin yaƙar abin da suka kira rikice-rikicen birane.

    Mataimakin gwamnan birnin, Vincent N'cho Kouaoh, ya ce barace-barace ta kowace fuska - an haramta su ne domin inganta rayuwar jama'a, da tabbatar da tsaron lafiyarsu da inganta zirga-zirgar ababen hawa.

    A shekarar 2013, ma'aikatar harkokin cikin gida ta hana bara a mahadar tituna, amma ta kasa daƙile wannan al'ada ta bara.

    Kokarin da aka yi a wasu biranen Afirka na hana bara bai sami nasara.

    Sabon haramcin ya biyo bayan korar jama'a da rusau a wasu unguwannin birnin.

    Babban birnin ƙasar Ivory Coast na ɗaya daga cikin biranen Afirka da ke da yawan jama'a kusan miliyan shida.

  11. Kotu ta samu Bobrisky da laifin wulaƙanta naira

    Babbar kotu tarayya da ke Legas ta samu Idris Olanrewaju Okuneye da aka fi sani da Bobrisky da laifin wulaƙanta naira.

    Alƙalin ya ajiye ranar yanke wa Bobrisky hukunci zuwa 9 ga watan Afrilu inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun EFCC.

    Kafin samun sa da laifi, Bobrisky ya shaida wa kotu cewa ba shi da masaniya kan dokar hana wulaƙanta naira.

    Alƙalin ya shaida masa cewa rashin sani ba hujja ba ne a doka.

    Bobrisky ya kuma nemi alƙali da ya sake ba shi dama ta yin amfani da shafinsa na sada zumunta wajen ilmantar da mabiyansa game da illar yin liƙi da kuɗi.

    "Ina da tarin mabiya fiye da miliyan biyar. Zan ɗora bidiyo a shafina kuma na faɗakar da mutane game da yin liƙi da kuɗi.

    "Ba zan sake yi ba, na yi da na sanin abubuwan da nayi."

    Bobrisky dai na iya fuskantar hukuncin wata shida a gidan yari ko biyan tarar naira dubu 50 ko ma ya yi duka biyun.

    A ranar Laraba ne hukumar EFCC ta kama Bobrisky kan zargin wulaƙanta naira.

  12. Janar Tchiani ya rushe ƙananan hukumomi a Nijar

    Ƙungiyoyin masu hamayya da gwamnatin soji a Nijar sun ce jagoran mulkin sojin ƙasar ya kawar da duk wani fata na komawa kan turbar dimokraɗiyya bayan da ya rushe ƙananan hukumomi.

    A ranar Alhamis ne Janar Abdourahamane Tchiani ya kori zaɓaɓɓun magadan gari da kansiloli a dukkanin yankuna 265 na jamhuriyar Nijar inda ya maye gurabensu da mutanen da ya zaɓa.

    A yau Juma'a ne kotu za ta saurari buƙatar neman a yaye labulen tuhuma kan mutumin da ya tilastawa barin kujerar mulki - Mohamed Bazoum.

    Tun bayan kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yulin bara, Janar Tchiani ya nesanta ƙasar da Faransa da Amurka inda ya ƙulla ƙawance da Rasha.

    A watan da ya gabata ne Janar Tchiani ya umarci sojojin Amurka su fice daga ƙasar inda suka shafe tsawon lokaci suna taya Nijar wajen fatattakar masu iƙirarin jihadi da ke yankin Sahel.

  13. An ci tarar kamfanin rarraba lantarki na Abuja naira miliyan 200

    Hukumar kula da wutar lantarki a Najeriya ta ɗauki matakin ladabtarwa kan kamfanin rarraba lantarki na Abuja, Aedc saboda rashin mutunta dokar ƙara kuɗin wuta.

    Hukumar ta ci kamfanin tarar naira miliyan 200 saboda yadda kamfanin ya chaji wasu abokan hulɗarsa da matakin ƙarin bai shafa ba.

    Matakin ya zo ne bayan ƙoken da abokan hulɗar kamfanin suka yi inda aka gano Aedc ya yi ƙarin kuɗin ne ga dukkan abokan hulɗarsa da ke kowane mataki saɓanin dokar ƙarin kuɗin da aka tsara ta domin tabbatar da adalci.

    Nerc ta ce dole ne Aedc ya mayar wa kwastamominsa da ke aji na biyu zuwa ƙasa kuɗaɗensu musamman waɗanda aka yi wa ƙarin kuɗin da bai shafe su ba.

    Sannan kuma kamfanin zai biya tarar ta nara miliyan 200 saboda saɓa dokokin hukumar.

    Sanarwar da Nerc ta wallafa a shafinta na Tuwita ya nemi kamfanin na Aedc da ya gabatar wa hukumar shaidar mutunta umarnin da ta ba shi nan da 12 ga watan Afrilu.

    Nerc ta ce ta ɗauki matakin ne domin cika alƙawarin kare haƙƙoƙin abokan hulɗa da tabbatar da adalci a ɓangaren wutar lantarkin Najeriya.

    • Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku
    • Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?
  14. IDF ta kori manyan sojinta masu hannu a hari kan ma'aikatan agaji

    Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da korar manyan jami'anta biyu daga sashen da ke da hannu a harin da aka kai kan ma'aikatan agaji a Gaza.

    A ranar Litinin ne wani hari da Isra'ila ta kai ya faɗa kan wasu ma'aikatan agaji bakwai da ke aiki ƙarƙashin ƙungiyar World Central Kitchen.

    IDF ta ƙara da cewa an tura wasu bayanai ga hukumar sojin domin gano ko an aikata babban laifi.

    Binciken da aka gudanar kan harin ya gano wasu ma'aikata sun tsira daga harin da aka kai da farko amma aka kashe su da aka kai hari kan mota ta uku.

  15. Bobrisky ya bayyana a kotu kan zargin halasta kuɗin haram

    A ranar Juma'a ne, Okuneye Idris Olarenwaju, da ake kira Bobrisky da ya yi fice a shafukan sada zumunta ya isa babbar kotun tarayya da ke Legas kan tuhumar da ake masa.

    Bobrisky ya isa kotun ne cikin wata farar bas ta hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

    Alƙalin kotun, Mai shari'a Abimbola Awogboro ne zai sauraron ƙarar da aka shigar kan Bobrisky.

    Hukumar EFCC ce ta kama Bobrisky ranar Laraba kuma yana fuskantar tuhume-tuhume shida na zargin wulaƙanta naira da kuma halasta kuɗin haram.

    Za mu kawo maku ƙarin bayani game da zaman shari'ar nan gaba.

  16. Akwai buƙatar Isra'ila ta sauya salon yaƙinta a Gaza – Jeremy Hunt

    Sakataren baitul malin Birtaniya, Jeremy Hunt ya yi kira ga Isra'ila da ta sauya salon yaƙinta a Gaza.

    "Muna son Isra'ila ta sauya tsarin da take aiwatar da wannan yaƙin domin rage mutuwar farar hula don mu kai agaji tare da ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su," ya faɗa wa manema labarai.

    Ya ce gwamnatin Birtaniya na daga cikin gwamnatocin farko-farko a duniya da suka yi magana ta nuna goyon bayan cewa Isra'ila na da ikon kare kanta."

    "Amma muna kuma cewa ya kamata su yi hakan ta yadda za a kaucewa kashe farar hular da ba su ji ba su gani ba kamar yadda muka gani a ƴan kwanakin baya-bayan nan," ya kara da cewa.

    Gwamnati na fuskantar matsin lamba har daga ƴan jam'iyyar Conservative na a dakatar da sayar wa isra'ila makamai sakamakon harin da aka kai wa jami'an agaji ranar Litinin har mutum bakwai suka mutu, a cikinsu ƴan Birtaniya uku.

  17. An yankewa mutum shekara 30 a kurkuku kan taimaka wa mai iƙirarin jihadi a Faransa

    An yankewa wani mutum hukuncin shekara 30 a gidan yari saboda taimaka wa wani mai iƙirarin jihadi da ya kashe mutum biyar a wata kasuwar kayan kirsimeti a disambar 2018.

    An sami Audrey Mondjehi mai shekara 42 da laifin mallakar bindigar da Cherif Chekatt ya yi amfani da ita wajen harbin mutane a Strasbourg da ke arewa maso gabashin Faransa.

    Mutanen biyu sun taɓa zaman gidan yari tare kamar yadda aka shaida a shari'ar.

    Sauran mutanen biyu, an yanke masu hukunci ne kan taimaka wa Chekatt. An kuma wanke mutum na huɗu.

    Mutum biyar aka kashe lokacin da Chekatt ya buɗe wuta kan jama'a a kasuwar. Sai dai kwana biyu bayan nan ne ƴan sanda suka harbe shi.

    A ranar 29 ga watan Fabarairu, Mondjehi da sauran mutanen da ake zargi da taimaka masa kafin kai harin suka fuskanci shari'ah a wata kotu da ke Paris.

    Arnaud Friedrich, wani lauya da ke wakiltar iyalan wasu daga cikin waɗanda aka kashe, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "lokaci ne mai muhimmanci" ga mutanen da yake karewa.

    Ba a sami Mondjehi da laifin aikata ta'addanci ba saboda kotun ta ce bai san abin da Chekatt ya ƙudiri aniyar yi ba da makamin.

    A cewar AFP, Mondjehi a kotun ya ce "Ina tunani mai zurfi kuma ina jin takaici kan abin da faru da mutanen. Tsawon rayuwata, zan ci gaba da yin da na sanin abin da ya faru.

  18. Shan ƙwaya ta zama matsala mai buƙatar matakin gaggawa a Saliyo

    Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ta ayyana shan miyagun wayoyi a matsayin matsalar da ya kamata a tunkare ta cikin gaggawa a asar inda kuma ya jero wasu matakai na magance wata fitacciyar ƙwaya da matasa ke amfani da ita.

    Kush, wani haɗin ƙwayoyi da ke kama da tabar wiwi da tramadol, ƙwaya ce da ta zama ruwan dare a ƙasar tsawon shekaru musamman a cikin birane.

    "Ƙasarmu a yanzu tana fama da barazana saboda mummunan tasirin ƙwayoyi da shan su, musamman ƙwayar kush," kamar yadda shugaba Bio ya faɗa a jawabin da ya yi wa ƴan ƙasar ranar Alhamis.

    "Wannan ƙwayar ta kush na matuƙar illa ga al'umominmu."

    Ya ce gwamnatinsa tana aiki domin wargatsa cibiyoyin ta'amali da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Ƙwayar wadda aka sani a K2 - an fi saurin samun ta a tsakanin matasan da ba sa aiki da ke neman kaucewa talauci da shiga ruɗin rayuwa.

    Ƙwararru a fannin kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa ƙwayar Kush na iya yin illar har abada ga ƙwaƙwalwa da kuma ɗaukan matakin kisan kai.

    A Fabarairu, gwamnatin Saliyo ta kafa cibiyar kula da waɗanda suka tsinci kan su a harkar ta'amuli da miyagun ƙwayoyi tare da kafa kwamitin kar-ta-kwana domin maganin matsalar.

    Ƙasashe masu maƙwabaka da Saliyo - Guinea da Liberiya suma suna yaƙi da yadda kush ke bazuwa.

    • Mun sha kama 'yan siyasa da ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi - Buba Marwa
    • Saudiyya ta kama mutum 16 da fataucin miyagun kwayoyi
  19. Masu fama da kansar mafitsara za su ninka a duniya – Rahoto

    Cikin shekaru 20 masu zuwa, za a a samu ƙaruwar masu fama da ciwon dajin mafitsara a faɗin duniya.

    Wannan na ƙunshe cikin rahoton mujallar lafiya ta Lancet. Masu fama da ciwon dajin mafitsara za su ƙaru daga dubu 500 zuwa miliyan 3 a shekarar 2040.

    Masu binciken sun ce za a fuskanci ƙaruwar ce daga rukunan mazan da suka manyanta.

    Binciken ya kuma ce za a samu ƙaruwar waɗanda cutar ke ajali a kowacce shekara da kashi 85 cikin ɗari musamman daga iyalai masu matsakaicin arziki da matalauta a ƙasashe masu tasowa.

    A ƙarshe rahoton ya buƙaci a faɗakar da maza kan cutar kansar mafitsarar, da yin gwaji, da fara shan magani tun cutar na matakin farko.

    • Masana sun samo hanyar gano kansar mafitsara cikin sauri
    • Me ya sa ake haihuwar jarirai da tawaya?
  20. An kafa kwamatocin bincikar gwamnatin Ganduje kan tuhumar almubazzaranci

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamatocin bincike biyu domin duba batun wadaƙa da kuɗin al'umma da rikicin siyasa da ɓatan mutane tsakanin 2015 da 2023 a tsukin zamanin mulkin mutumin da ya gada, Abdullahi Ganduje.

    Yayin ƙaddamar da kwamatocin ranar Alhamis, gwamna Yusuf ya buƙaci mambobin da su yi aiki domin hukunta wanda yake da hannuu.

    Gwamnan ya ce gudanar da bincike kan almubazzaranci da kuɗaɗen al'umma wani ɓangare ne na alƙawarin da ya ɗauka a lokacin da ya sha rantsuwar kama aiki na bankaɗowa tare da gurfanar da mutanen da ke da hannu a rikice-rikicen siyasa da suka farua jihar.

    Ya bayyana yadda tashin hankali sakamakon rikicin siyasa ke janyo koma-baya ga dimokraɗiyya a faɗin duniya da kuma janyo asarar rayuka da rashin yarda a ɓangaren mutane da kuma waɗanda ke jagoranci.

    Gwamnan ya ce bai kamata a ƙyale munanan rikice-rikicen siyasar da aka gani musamman a 2023 su wuce ba don a hana afkuwar haka a gaba.

    Kwamitin farko, ƙarƙashin Zuwaira Yusuf zai duba rikicin siyasa da mutanen da suka ɓata daga 2015 zuwa 2023.

    "Muna fatan a zaƙulo mutanen da ke da hannu tare da bayyana waɗanda suka tallafa domin su fuskanci hukunc a kuma gano dalilai da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da 2013". in ji gwamnan.

    Kwamiti na biyu, bisa jagorancin Mai shari'a Faruk Lawan, ya samu umarnin gwamna Yusuf da ya duba ƙararrakin da suka shafi almubazzaranci da dukiyar al'umma da kadarorin gwamnati.

    Gwamnan ya buƙaci mai shari'a Lawan da mambobin kwamitin da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen gano almubazzarancin da aka yi musamman a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata.

    A zaɓen da ya gabata ne aka kama, ɗan majalisar wakilai Alhassan Doguwa saboda zargin hannu a kisan da aka yi wa wasu da kuma tayar da rikici.

    Sai dai daga bisani an ba da belinsa.

    • Binciken gwamnatin Kano ya wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kai