Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Aisha Bappa da Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida, Ahmad Tijjani Bawage and Aisha Shariff Bappa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Aisha Bappa da Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
A yau Sady Taheer ta nuna mana yadda ake yin haɗin bula ko tuwon ruwa wanda Sakwatawa ke matukar son ci.

Asalin hoton, Bobrisky/IG
A yau Alhamis ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky, kan wasu tuhume-tuhume guda shida.
Bobrisky zai gurfana gaban mai shari’a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Juma'a.
Yayin da tuhume-tuhume hudu na farko suka ta'allaka kan wulaƙanta takardar naira, biyu na baya-bayan nan dai na da alaka da halasta kuɗaɗen haram.b
A cikin karar da mai shigar da kara na EFCC Rotimi Oyedepo ya gabatar, da kuma wasu lauyoyi bakwai, sun tuhumi Bobrisky da laifin liƙi kuɗi da suka mkai naira N400,000 a wasu tarukan sharholiya a IMAX,Circle Mall, Lekki, da kuma Lagos.
Sun ce ya aikata laifin ranar 24 ga watan Maris ɗin da muke ciki, kuma hakan ya saɓa wa sashe na 21(1) na dokar babban bankin Najeriya na 2007.

Gwamnatin jihar Legas ta sake buɗe babbar gadar Third Mainland Bridge bayan kammala aikin sake gyara shi.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana sake bude gadar ga masu ababen hawa yau Alhamis a wani sako da ya wallafa a shafin X, bayan shafe kusan makonni huɗu ana aikin gyara a gadar.
Gwamna Sanwo-Olu ya gode wa shugaba Bola Tinubu da kuma ministan ayyuka na Najeriya Dave Umahi saboda kokarinsu wajen ganin an kammala aiki a gadar.
"Ina farin cikin sanar da cewa an sake bude gadar Third Mainland Bridge bayan kammala aikin gyara da aka yi don tabbatar da lafiyar gadar da kuma mazauna garin. Hakurin da kuka nuna na wadannan tsawon makonni suna da muhimmanci wajen kara karfafa tattalin arzikin birnin mu,” in ji Sanwo-Olu.
An yi aikin gyara gadar ta Third Mainland, wadda ta kasance ɗaya daga cikin mafiya tsawo a Afrika na tsawon makonni, abin da ya janyo cunkuson ababen hawa da kuma sauran masu amfani da hanyar.
Cikin aikin da ak yi a gadar sun haɗa da saka sabon kwalta, fitulun hasken rana, kyamarorin tsaro da sauransu.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Mahukunta a Abidjan, birni mafi girma a Ivory Coast, sun sanar da haramta bara a birnin a kokarin da suke yi na dakile rashin bin doka a cikin birnin.
Mataimakin gwamnan birnin,Vincent N'cho Kouaoh, ya ce an haramta kowane irrin bara ciki har da dakon kaya domin a inganta jin daɗi da kuma walwalar al'ummar birnin.
Gwamnan ya ce an kuma ɗauki matakin ne domin a tabbatar da tsaron mutane.
A 2013, ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta haramta bara a kan tituna, to amma mutane suka ki bin dokar.
Yunkurin makamancin wannan da wasu biranen ƙasashen Afirka suka yi ma bai samu nasara ba.
Wasu mazauna garuruwa bakwai da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara sun yi zargin cewa ƴan sa kai daga wani gari da ke makwabtaka da su na addabarsu, inda suke tare su a kan hanya don yi musu sata har ma da kashe su.
Sun ce duk ƙoƙarin da suka yi domin shawo kan matsalar ya ci -tura.
Ga rahoton Raliya Zubairu.

Asalin hoton, Fredrick Nwabufo/X
Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta shawo kan matsalar taɓarɓarewar tattalin arziki da kasar ke fama da shi, ciki har da sauko da hauhawar farashin kayayyaki.
Ya ce duk da cewa shi ba na daban bane, amma kada ‘yan Najeriya su damu saboda yana da zimmar kawo karshen hauhawar farashi.
Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a wajen buɗe-baki a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, inda ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don sauko da farashin kayayyaki.
“Wannan alkawari ne mai wahala da kuka yi wa al’ummar Najeriya lokacin da kuke min yakin neman zaɓe, dole ne na yi aiki don tabbatar da haka.
“Na yi kamfe kan fata mai kyau, dole ne na ɗabbaka wannan fata da kuma fatan ganin kowaye cikinmu ya ji daɗi. Tattalin arzikinmu na kan turba mai kyau. Kada ku damu kan haka,” in ji Tinubu.
Ya ce Najeriya na fama da matsalar hauhawar farashi kuma a shirye gwamnatinsa take wajen magance ta.
“Muna sake fasalin harkokin kuɗir shigarmu, kuma muna samun nasara kan haka, kuma muna dawo da tagomashinmu a faɗin duniya,” in ji shugaban Najeriyar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Togo ta dage zaben 'yan majalisar dokokin da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga Afrilu zuwa ranar da ba a bayyana ba don ba da damar yin shawarwari.
Shafin yaɗa labarai na Afreepress mai zaman kansa ya ruwaito cewa an yanke wannan shawarar ne a jiya yayin wata ganawa tsakanin shugaba Faure Gnassingbe da 'yan majalisar dokokin kasar.
Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce "Wannan shawarar ta samo asali ne daga bukatar shiga tattaunawa mai zurfi da kuma sauraren dukkan masu ruwa da tsaki a sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar."
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin Togo a ranar 25 ga watan Maris ta amince da sauye-sauyen da ake tafkawa a kundin tsarin mulkin kasar da zai maye tsarin shugabancin kasar da na majalisar dokoki.

Asalin hoton, AFP
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya bukaci bangarorin da ke cikin yarjejeniyar zaman lafiya da aka sake farfado da su a shekarar 2018 da su ci gaba da tattaunawa kan babban zaben watan Disamba na shekarar 2024.
Kiir ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta zartar da wasu kudirorin da suka shafi gudanar da zaben, kamar yadda gidan rediyon Eye mai zaman kansa ya ruwaito jiya.
"A bar jam'iyyun su ci gaba da tattaunawa don cimma matsaya kan gudanar da zaben kamar yadda aka tsara," in ji Kiir yayin da yake sake buɗe majalisar dokokin kasar ta wucin gadi jiya.
Ya kuma bukaci jama’a su kuma shirya kaɗa ƙuri'a a zaben, ya kuma ce gwamnatinsa ta dukufa wajen tunkarar kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.
Babbar kungiyar 'yan adawar Sudan ta SPLM-IO, ta yi barazanar ƙauracewa zaɓen, tana mai cewa ba a aiwatar da wasu tanadi na yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ba.
Jagoran SPLM-IO kuma mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar ya goyi bayan tattaunawa don warware rikicin zaɓe

Asalin hoton, Getty Images
Shari’ar kin biyan haraji da ta shafi hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC da dandalin musayar kudaden intanet, Binance da shugabanninta guda biyu ta sami tsaiko, a ranar Alhamis.
Wannan ya biyo bayan gazawar hukumar haraji ta Najeriya, FIRS, ta yi na bayyana tuhuma-tuhuman da ake yi wa waɗanda ake zargi.
A babbar kotun tarayya da ke Abuja, daya daga cikin shugabannin Binance Tigran Gambaryan ne kawai ya gurfana a gaban mai shari’a Emeka Nwite, yayin da Nadeem Anjarwalla ba ya nan, inda har ya zuwa yanzu ba a san inda yake ba, bayan ya tsere daga tsarewar da aka yi masa bisa wasu sharudda da ba a tabbatar ba.
Lauyan Gambaryan ya shaida wa kotun cewa ba za a iya gurfanar da wanda yake karewa ba saboda ba a gurfanar da shi a tuhumar FIRS ba.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa lauyan Gambaryan ya shaida wa kotu cewa ba za a iya gurfanar da wanda yake karewa ba saboda ba a tuhume shi da laifin komai ba.
Daga bisani alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Afrilu.
A watan da ya gabata ne dai, hukumar tattara harajin cikin gida ta ƙasar ta shigar da tuhumar kin biyan haraji a kan dandalin Binance kuma ta sanya sunan Anjarwalla da Gambaryan a cikin wadanda suka amsa.
A ranar Laraba ne Binance ya fitar da wata sanarwa inda ta buƙaci a saki Tigran Gambaryan wanda suka ce a baya ya hada kai da hukumomin Najeriya wajen yaki da miyagun laifuka da garkuwa da mutane da kuma kwace kadarorin da suka kai kimanin dala 400,000.
A halin da ake ciki, hukumomin Najeriya sun ce suna aiki tare da ƴan sandan ƙasa da ƙasa domin bayar da sammacin ƙasashen duniya na kama Mista Anjarwalla.
Hukumar harajin Najeriya ta zargi Binance da ƙin biyan harajin da ake sawa kan kayayyaki da harajin samun kuɗin shiga na kamfani da gazawar shigar da bayanan haraji, da kuma haɗa kai wajen taimaka wa abokan ciniki su guje wa haraji ta hanyar Binance.
Babban bankin Najeriya ya kuma bayyana cewa kusan dala biliyan 26 ne aka yi hada-hadar kasuwanci a Binance Nigeria tare da wasu majiyoyi da ba a gano su ba.

Asalin hoton, Getty Images
A jiya ne shugaban ƙasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ya bayyana cewa, kasar za ta buƙaci dalar Amurka biliyan 2 don hana yunwa yayin da suke fama da bala'in fari a ƙasar da makwaftan ƙasashen kudancin Afirka.
Yayin da yake ayyana yanayin bala'i na farin da suke fama da shi, Mnangagwa ya ƙiyasta cewa kashi 80 ciki 100 na Zimbabwe sun samu ruwan sama ƙasa da yadda aka saba, wanda ya shafi noman masara da hatsi a kakar 2023 da 2024.
Kwamitin tantance rayuwar jama'a na Zimbabwe ya ce mutane miliyan 2.7 na fama da karancin abinci tsakanin Afrilu 2023 da Maris 2024.
Shafin intanet na Newsday mai zaman kansa ya bayyana cewa, Zimbabwe za ta yi gwagwarmayar tara kudade daga wajen masu ba da taimako a yayin da ake fama da fari a makwabciyarta Zambia da Malawi, da ma sauran ƙalubalen duniya.
Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya fada a watan da ya gabata cewa ƙasarsa za ta bukaci dala miliyan 200 domin dakile fari.
Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce adadin mutanen da aka kashe a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba ya ƙaru zuwa 33,037.
Adadin wadanda suka mutu ya hada da mutuwar mutane 62 a cikin awanni 24 da suka gabata.
Sanarwar ma'aikatar ta ƙara da cewa adadin mutanen da suka jikkata tun ranar 7 ga Oktoba ya kai 75,668.
Sojojin Isra'ila sun fara kai farmakin ne bayan harin na ranar 7 ga watan Oktoba da mayaƙan Hamas suka kai inda suka kashe kimanin mutanen Isra'ila 1,200.
Mutum uku sun rasa rayukansu a garin Takum da ke jihar Taraba sakamakon wata guguwa da ta faru sau biyu cikin kwana biyu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mazaunin garin Mallam Maiwada Takum na cewa guguwar ta soma faruwa ne da yammacin ranar Talata inda ta yi gagarumar ɓarna ga gidaje da makarantu da ofisoshi.
Takum ya ƙara da cewa da farko an yi mamakon ruwan sama daga bisani kuma aka yi guguwa mai ƙarfi da ta shafe fiye da sa'a ɗaya da rabi tana zagawa.
Shi ma wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya bayyana cewa guguwar ta yi matuƙar ɓarna inda ta salwantar da gidaje da rayuka.
Babban mai bai wa gwamnan jihar shawara kan yaɗa labarai, Emmanuel Bello ya ce gwamna Agbu Kefas ya higa garin domin duba irin ɓarnar da guguwar ta yi.
An kuma bayar da rahoton mutuwar mutum ɗaya da jikkatar wasu da dama sakamakon tashin guguwa da ta lalata gidaje fiye da 100 a yankin Agbashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nassarawa.
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, John Bako-Ari ne ya tabbatar da lamarin inda ya ce guguwar ta tashi ne ranar Talata da yamma.

Asalin hoton, Bobrisky/IG
Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa ta kama Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky saboda zargin sa da wulaƙanta takardar naira.
EFCC ta wallafa a shafinta na fesbuk cewa ta gayyaci Bobrisky bayan ɓullar wani bidiyo da ke nuna yadda mai shekara 31 a duniyar ke yin liƙi da sabbin damman takardun naira a bikin nuna wani fim da aka yi ranar 24 ga watan Maris a jihar Legas.
A baya ma an samu Bobrisky da aikata laifin da ake zargi a wasu tarukan sharholiya, kamar yadda EFCC ta ce bincike ya nuna.
A cewar hukumar, Bobrisky na ofishinta na Legas domin amsa tambayoyi.
EFCC ta ce ba da daɗewa ba za a gurfanar da Bobrisky a gaban kotu.

Asalin hoton, EFCC/Fb

Asalin hoton, Abba El-Mustapha1/Fb
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da matakin haramta shirya fina-finan da ke nuna faɗan daba da harkar daudu.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya sanar da matakin ranar Laraba bayan ganawa da manyan ma'aikatan hukumar tace fina-finai na jihar da wasu wakilai daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood.
Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da jami'in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya sanyawa hannu.
El-Mustapha ya bayyana cewa hukumar tana da sahhalewar doka ta dakatar da duk wani fim da take ganin zai ci karo da tarbiyya da al'adar al'ummar jihar Kano.
Shugaban hukumar ya kuma bai wa masu shirya fina-finai nan da wata ɗaya da su gyara ayyukansu kafin dokar ta soma aiki.
A cewarsa, lokaci ya wuce da za a naɗe hannu kan fina-finan da ke gurɓata tarbiyyar al'umma.

Asalin hoton, @ubasanius/X
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yankuna 551 a sassan ƙananan hukumomi 12 ne hare-haren ƴan bindiga suka shafa lamarin da ya ɗaiɗaita mutum 289,375.
Dakta Usman Hayatu Mazadu, babban sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar ne ya bayyana haka lokacin rarraba kayan taallafi a Maraban Kajuru.
Ya ce a yankin Chikun, yankuna 134 lamarin ya shafa sannan mutum 26,345 ne suka rasa gidajensu.
"A Birnin Gwari, hare-haren sun shafi yankuna 84 sai 70,893 da suka ɗaiɗaita." kamar yadda jami'in ya bayyana.
Dakta Mazadu ya jaddada buƙatar a samar wa mutanen da lamarin ya shafa tallafi inda ya bayyana mummunan tasirin da hare-haren suka yi wa yankunan.
Kaduna na cikin jihohin da suke fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane don kuɗin fansa inda ko a baya-bayan nan an sace gomman ɗalibai tare da malaminsu a yankin Kuriga.
Sai dai jami'an tsaro sun kuɓutar da su bayan kwanaki a hannun ƴan bindigar da suka yi awon gaba da su.

Asalin hoton, Reuters
Tsofaffin alƙalan kotun ƙoli sun bi sahun masana shari'a fiye da 600 wajen kira ga gwamnatin Birtaniya ta daina sayar wa Isra'ila makamai.
Cikin wata takarda zuwa ga firaiminista Rishi Sunak, tsofaffin alƙalan sun ce dole ne a kawo ƙarshen fitar da makamai saboda Birtaniya na cikin haɗarin karya dokokin duniya.
Tuni dai mista Sunak yake fuskantar matsin lamba bayan sojojin Isra'ila sun kashe wasu ma'aikatan agaji bakwai.
A ranar Talata ne, firaiministan ya ce Birtaniya tana da wani tsari na kaffa-kaffa game da lasisin makamai.
Tsohuwar shugabar kotun ƙoli, Lady Hale na cikin masana sama da 600 da suka sa hannu kan takardar mai shafuka 17.
Takardar ta ce akwai buƙatar a ɗauki mataki na gaske domin hana Birtaniya faɗawa matsalar karya dokokin ƙasa da ƙasa har da yiwuwar saɓa yarjejeniyar da ta shafi dokokin kisan kiyashi.
Sauran mutanen da suka sa hannu kan takardar sun haɗa da tsofaffin alƙalan kotun ƙoli Lord Sumption da Lord Wilson tare da wasu alƙalai tara da manyan lauyoyi 69.

Ministocin harkokin wajen ƙasashen Nato, za su taru a birnin Brussels domin ƙwarya-ƙwaryar bikin cika shekara 75 da kafuwar ƙungiyar.
A shekarar 1949 ne ƙasashe 13 suka fara kafa kungiyar a matsayin martani kan barazanar tarayyar Soviet.
A yanzu Nato na da mambobi 32, sakamakon shigar Finland da Sweden a baya-bayan nan.
Da ya ke jawabi a daren jiya, sakatare janar na ƙungiyar, Jens Stoltenberg ya ce mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine shekaru biyu da suka gabata, na nufin Turai ta sake faɗawa yaƙi kamar yadda aka gani shekaru 75 da suka wuce.
Masu bibiyar wannan shafi na kai tsaye da BBC Hausa ke kawo maku a kowace rana, barka da safiya.
Muna addu'ar Allah ya karɓi ibadunmu a wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan abubuwan da ke faruwa a duniya musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.
Kuna iya zuwa shafukanmu na sada zumunta inda a nan ma akwai abubuwan da muka wallafa da za ku ƙaru da su.