Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mukhtar Adamu Bawa, Nabeela Mukhtar Uba and A'isha Babangida

  1. Yarinyar da ta auri ɗan shekara 63 a Ghana ta kusa 16 – minista

    Ministan harkokin masarautu da harkokin addini na Ghana ya bayyana cewa yarinyar da ta auri wani jagoran addinin gargajiya mai shekara 63 da aka ruwaito shekararta 12, a zahiri ministan ya ce shekararta 15.

    Minista Stephen Asamoah Boateng ya bayyana haka a wata hira da gidan rediyon Citi FM cewa yarinyar za ta cika shekara 16 a watan Yuli.

    Duk da saɓanin shekarun da aka samu, ministan ya jaddada cewa yarinya ce, kuma ya ce za a yi ƙoƙarin kare haƙƙinta tare da haɗin gwiwar wasu hukumomi.

    Sabanin bayanin da ministan ya yi, basaraken al’ummar Nungua, inda aka gudanar da bikin, ya shaida wa Citi FM cewa yarinyar tana shekara 13 ne kacal.

    Mafi ƙarancin shekarun aure a dokar Ghana shi ne shekara 18.

    Bayyanar shekarun yarinyar na gaskiya ya janyo cece-ku-ce a tsakanin jama'a sakamakon yaɗa faifan bidiyon ɗaurin auren nasu a ranar Asabar a shafukan sada zumunta.

    A ranar Litinin ne ‘yan sanda suka sanar da cewa sun gano yarinyar kuma za su tabbatar da tsaronta yayin da suke gudanar da bincike a kan auren da ya janyo cece-kuce.

    A halin da ake ciki, ofishin jagoran addinin gargajiya ya kare bikin, yana mai bayyana shi a matsayin baiko tare da tabbatar da cewa yarinyar ba za ta fara sauke nauye-nauyen aure ba a wannan lokaci.

    Dangane da lamarin, mataimakiyar babban mai shari’a Diana Asonaba Dapaah ta umurci ‘yan sanda da su gudanar da cikakken bincike inda ta bayyana cewa aure ko wane iri na ƙaramar yarinyar da ba ta kai shekara 18 ba ya saɓawa dokar ƙasar kuma akwai hukunci.

    • Auren wuri haramun ne - Save the Children
    • 'Babu wani aibu a auren wuri'
  2. Yadda harin ƴan bindiga ya tilasta wa ƴan Najeriya yin ƙaura zuwa Nijar

    Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a cikin ƙasa da mako guda mutum 1,400 ne suka tserewa hare-haren ƴan bindiga daga Najeriya zuwa yankin Maraɗi na jamhuriyar Nijar da ke iyaka da ƙasar.

    Hukumar ta ce wannan shi ne adadi mafi yawa da aka ga ƴan gudun hijira a wannan shekarar, lamarin da ke buƙatar agajin gaggawa a yankin.

    Ga ƙarin bayani cikin rahoton wakiliyar BBC, Tchima Illa Issoufou.

  3. Abin da ya kamata ku sani game da girgizar ƙasar Taiwan

    • Gwamnatin Taiwan ta ce aƙalla mutum bakwai ne suka mutu, wasu 711 kuma suka ji rauni
    • Ƙarfinta ya ka maki 7.4 wadda ita ce mafi ƙarfi da ta taɓa afkuwa a yankin cikin shekara 25
    • Gine-gine a Taipei, babban birnin yankin da yankunan da ke maƙwabtaka sun girgiza kuma ana fargabar mutane da dama sun maƙale cikin ɓuraguzai a Hualien kusa da cibiyar girgizar ƙasar
    • An yi gargaɗin faruwar ambaliyar Tsunami a tsibiran Japan da ke maƙwabtaka sannan an rage tekun Philippines da ke arewaci
    • Japan da China sun kai wa Taiwan agaji
    • Shugaba Tsai Ing-wen ya ce za a tura rundunar sojin Taiwan domin aikin agaji
  4. An kama mai sayar da yalo kan zargin yi wa yaro fyaɗe a Bauchi

    Jami'an ƴan sandan jihar Bauchi da ke aiki ƙarƙashin rundunar maido da zaman lafiya sun kama matashi mai shekara 23 da ake zargin ya yi wa wani yaro ɗan shekara goma fyaɗe.

    Matashin da ake zargi ya yaudari yaron da naira 30 da alawa inda ya nemi yaron ya raka shi wani kango da ke bayan wani gidan mai a kan titin Kofar Ran domin ya yi bahaya.

    Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar ta ce bayan ya yi bahayar ne kuma, matashin ya buƙaci yaron da ya tuɓe wandonsa ya duba ko ya yi tsarki.

    A cewar sanarwar, bayan da yaron ya cire wandonsa ne kuma, matashin ya cakumo yaron ta baya inda kuma ya yi masa fyaɗe.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "nan ne yaron ya ruga wajen shugaban gidan man tare da sanar da shi abin da matashin ya yi masa."

    Rundunar ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa matashin da ake zargi ya fito daga ƙauyen Jingino da ke ƙaramar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

    Ya je jihar Bauchi shekara biyu baya inda yake sana'ar sayar da ɗata a gidan man da ke kan titin Kofar Ran, in ji sanarwar.

    Rundunar ta ce an gano cewa matashin mai sayar da ɗata ya yi amfani da yanayin yaron da yake da matsalar ƙwaƙwalwa wajen yi masa aika-aikar ta fyaɗe.

    Ƴan sanda sun ce an garzaya da yaron zuwa asibitin koyarwa na Bauchi tare da matashin da ake zargi inda aka gudanar da gwaje-gwaje domin duba lafiyarsa.

    Ana ci gaba da yin bincike kuma da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban kotu.

    • Yadda fasto ya hada baki da matarsa don yi wa wata yarinya 'fyade'
    • An samu tsohuwar hedimasta da laifin yi wa ɗalibai fyade
  5. An naɗa Ousmane Sonko a matsayin firaiministan Senegal

    Sabon shugaban ƙasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya naɗa shugaban babbar jam'iyyar adawa, Ousmane Sonko a matsayin firaiministan ƙasar.

    Ousmane Sonko dai shi ne ubangidan shugaba Faye a harkokin siyasa kuma an ɗaure su a gidan yari daf da zaɓen na watan Maris.

    Amma daga bisani tsohon shugaban ƙasar Macky Sall ya yi masu afuwa, tare da wasu fursunonin siyasa.

    Bayan ƴan sa'o'i kaɗan da hawansa mulki a matsayin shugaban ƙasar Senegal ne shugaba Faye ya naɗa Sonko a matsayin firaiminista," fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na X.

    Tun da farko dai an bayyana Sonko a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa amma bayan an kama shi ne sai aka yanke masa hukuncin cewa bai cancanci tsayawa takara ba - matakin da ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

    A jawabinsa na rantsar da shi a ranar Talata, shugaba Faye ya ce Senegal za ta zama ƙasa mai babban fata tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya.

    • Abubuwan da suka kamata ku sani kan madugun ƴan adawar Senegal Ousmane Sonko
    • Daga kurkuku ya zamo shugaba mafi ƙarancin shekaru a Afirka
  6. Mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Taiwan sun kai bakwai

    Hukumomi a Taiwan sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.4 da ta afku a yankin sun ƙaru zuwa bakwai.

    Hukumar kashe gobara ta yankin, ta ce mutum 711 ne suka ji rauni yayin da wasu 77 kuma suka maƙale cikin ɓuraguzai.

    Bidiyo daga shaidu ya nuna girman ɓarnar da girgizar ƙasar ta yi a Hualien kusa da cibiyar da lamarin ya faru inda wasu gine-gine suka tanƙwara gefe.

    Zuwa yanzu dai jami'ai sun duƙufa da agaji domin zaƙulo waɗanda suke da sauran numfashi da suka maƙale a ɓuraguzai.

    Girgizar ƙasar ita ce mafi ƙarfi da aka taba gani a yankin Taiwan cikin shekara 25.

    • Darussan da Japan ta koya daga girgizar ƙasa
    • Abin da ya kamata ku yi yayin da girgizar ƙasa ke faruwa
  7. Barka da Hantsi!

    Muna yi maku barka da wannan lokaci.

    Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma wasu sassan duniya.

    Idan kuma kuka leƙa shafukanmu na sada zumunta, za ku ga wasu ƙarin labarai har ma da bidito da za ku iya kalla.