Mahaukaciyar guguwa ta afka arewacin Madagascar
Wata mahaukaciyar guguwa da ta afka arewacin Madagascar ta janyo mutuwra mutum aƙalla shida tare da raba 2,000 da gidajensu.
Jaridun ƙasar sun ce ambaliyar ruwa ta yi gagarumar ɓarna da ta shafi tituna da gadoji.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito hukumar kula da annoba ta ƙasa data bayyana mutuwar mutum 11 sakamakon guguwar ta Gamane.
Hukumar ta ce mutum shida sun nutse, sauran kuma sun mutu sakamakon bishiyoyi da suka faɗa musu da kuma gidaje da suka ruguje.
"Ba kasafai ake ganin irin wannan guguwa ba," in ji Janar Elack Andriakaja, babban daraktan hukumar.
- Mahaukaciyar guguwa da ta shafe fiye da wata ɗaya tana ɓarna
- 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'