Wani kamfanin da ke samar da nafkin a Japan ya sanar da cewa zai daina samar da nafkin din yara a ƙasar, a maimakon haka zai mayar da kai wajen samar da nafkin din manya.
Kamfanin Oji Holdings, shi ne kamfani na baya bayannan da ya yi wannan sanarwa a ƙasar da tsofaffi suka fi yawa saboda rashin haihuwa.
Cinikin da ake a kan nafkin din manya ya fi na yara a ƙasar tsawon shekaru fiye da goma.
Adadin jariran da aka haifa a 2023 a Japan da suka kai 758,631, ya yi ƙasa da kashi 5.1 idan aka kwatanta da shekarun baya.
Kuma a shekarar barar ne aka samu raguwar haihuwa sosai a ƙasar tun ƙarni na 19.
Cikin wata sanarwar, kamfanin Oji Holdings, ya ce yanayin cinikin da ya ke samu a kan nafkin din yara na raguwa tun shekarar 2001.
A 2001 ne, babban kamfanin da ke samar da nafkin a Japan Unicharm, ya ce cinikin da ya ke samu a nafkin din manya ya fi na yara sosai.
A yanzu haka Japan na cikin ƙasashen da suka fi yawan tsofaffi a duniya inda kashi 30 cikin 100 na tsofaffin na tsakanin shekarun 65 zuwa sama.
Kamfanin Oji Holdings, ya ce yanzu zai mayar da hankali wajen samar wa ƙasashen Malaysia da Indonesia nafkin din yara domin a nan ne aka yawan buƙatarta saboda ana haihuwar jarirai akai-akai.
Rashin haihuwa a Japan ya zamo babban abin damuwa a Japan, wadda tana ɗaya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
To amma ƙoƙarin da gwamnatin ƙasar ke yi wajen ganin an shawo kan matsalar a yanzu ana samun nasara.
ƙwararru sun ce dalilan da suka janyo rashin haihuwa a ƙasar na da dama ciki har da rashin aure sannan kuma mata da dama sun shiga aikin ɗamara.
-
Yadda ƙasashen Asiya ke kashe maƙudan kuɗi don bunƙasa haihuwa
-
Halin da jaririyar da ta zama mutum na biliyan ɗaya a Indiya ke ciki