Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Shaguna '180' sun ƙone a gobarar babbar kasuwar Sokoto

    Wata gobara da ta tashi a babbar kasuwar jihar Sokoto da safiyar yau Litinin ta yi sanadin ƙonewar shaguna da dama a ɓangaren masu sayar da babura da kekuna.

    Garba Muhammad Gwazi, shugaban ƴan mashin reshen jihar ya shaida wa BBC cewa gobarar ta laƙume shaguna '180' na masu sayar da mashin.

    A cewarsa, har yanzu ba a san abin da ya janyo tashin gobarar ba da ta janyo asarar dukiya ta miliyoyin naira. Sai dai ya ce gobarar ta soma ne daga wata shara da aka tara.

    Ya bayyana cewa gobarar ba ta kai ga asarar rai ko jikkata ba.

    Gwazi ya kuma yi kira ga gwamnati ta kai masu ɗauki domin "kasuwancinmu ya miƙe ya ci gaba." in ji shi.

    Shi ma Honarabul Ibrahim Muhammad Giɗaɗo, mai bai wa gwamna shawara kan babbar kasuwar ya ce wutar ta tashi da sanyin safiyar yau.

    Ya ce "ɓangaren da ya ƙone sosai a cikin kasuwar shi ne na ƴan mashin da kekuna, ana iya samun shago guda ɗauke da mashin fiye da 200 ko 100, shagunan gaba ɗaya sun ƙone,"

    "Waɗannan mashina akwai waɗanda suka haura miliyan, akwai asara mai yawa." ya ƙara da cewa.

    Giɗaɗo ya ƙara da cewa jami'an kashe gobara sun kashe kashi 80 cikin 100 na gobarar da ke ci

    • Gobara ta ƙona kimanin shaguna 50 a kasuwar Singa
    • Me yake jawo gobara a kasuwannin Najeriya kuma yaya za a magance ta?
  2. 'Yan bindiga sun kashe farar hula fiye da 100 a gabashin Burkina Faso

    Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe farar hula fiye da 100 a hare-hare daban-daban da suka kai ƙauyukan lardin Kompienga da ke gabashin Burkina Faso, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta La Kompienga en Temps Reel mai zaman kanta ta ruwaito.

    Rahoton ya ce, an yi kisan kiyashi kan fararen hula na Kpadiari da Nadiagou da Tindangou a jiya 16 ga Maris” inda rahoton ya ƙara da cewa an samu labarin mutuwar mutane aƙalla 130.

    Masu amfani da intanet sun ce waɗanda abin ya shafa da suka haɗa da mata da ƙananan yara, ana zarginsu da alaƙa da ƙungiyoyin ƴan bindiga.

    A baya-bayan nan dai ƙasar Burkina Faso ta sha fama da kashe ɗaruruwan fararen hula da ake zargin wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga ne.

    Ana kuma zargin jami'an tsaron da aikata kisan gilla kan mutane da dama.

    • 'Rashin haɗin kan gwamnatoci dama ce ga 'yan bindiga'
    • al-Shabab: 'Yan bindiga sun tarwatsa taron siyasa a Somaliya
  3. An rufe makarantu a Sudan ta Kudu saboda matsanancin zafi, Daga Nichola Mandil, BBC News, Juba

    An rufe daukacin makarantu a Sudan ta Kudu, sakamakon tsananin zafin da kasar ke fama da shi cikin makonni biyu.

    Ma'aikatar lafiya da ilimi sun bai wa iyaye shawarar kar su bari ƴaƴansu su fita, sakamakon hasashen tsananin zafin ka iya kai wa maki 45 a ma'aunin selshiyos.

    Ma'aikatun sun ce, ana bibiyar yanayin sau da ƙafa, sai dai babu ranar buɗe makarantun.

    Sun ce duk makarantar da aka samu a buɗe, za ta rasa lasisinta, kamar yadda hukumomin suka yi gargaɗi.

    A makon da ya gabata ne, aka ba da rahoton mutuwar kimanin yara 15 sakamakon sanƙarau da wasu cututtukan da zafi ke haddasawa, in ji ma'aikatar lafiya ta ƙasar.

    • Matsanancin zafi na ci gaba da gallabar kasashen Turai
    • An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China
  4. Isra'ila ta ƙaddamar da hari kan asibitin al-Shifa a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun sanar da ƙaddamar da hari kan asibitin al-Shifa da ke Gaza.

    Mai magana da yawun sojin Isra'ilar, Rear Admiral Daniel Hagari, ya ce sojoji sun gano matattarar Hamas da sake shiri ta amfani da asibitin domin kai musu hari.

    Hagari ya ce "muna kira ga 'yan ta'addar Hamas da ke ɓuya a asibitoci, su mika wuya ba tare da ɓata lokaci ba, asibitoci ba wurin aikata ta'addanci ba ne".

    Wani bidiyo da aka aike wa BBC ya nuna ɗaruruwan farar hula na ficewa daga asibitin, cikin tsananin duhu suna amfani da hasken wayar salula domin haska hanya.

    Wata sanarwa daga ma'aikatar lafiyar Hamas ta kira harin a matsayin take dokar jin ƙai ta ƙasa da ƙasa".

    Ɗaruruwan Falasɗinawa da suka ɗaiɗaita ne ke samun mafaka a asibitin da sojojin Isra'ila suka kai wa samame a farkon soma yaƙin.

    Al-Shifa shi ne babban asibitin Gaza kafin yaƙin amma ayyukansa sun fuskanci cikas bayan shafe watanni ana gumurzu.

    • Ina ne Ƙudus kuma me ya sa ake taƙaddama kan shi?
    • Isra'ila ta hana shigar da abinci Gaza - MDD
  5. EU da Masar sun ƙulla yarjejeniyar dala biliyan 8 don daƙile ƙaura

    Kungiyar Tarayyar Turai da Masar sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta dala biliyan 8 da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin kasuwanci da tsaro, da kuma ƙoƙarin daƙile kwararar baƙin haure zuwa Turai.

    Yarjejeniyar dai ta inganta dangantakar Tarayyar Turai da Masar.

    Ana sa ran za a ba da tallafi da lamuni da sauran kuɗade nan da shekaru uku masu zuwa don tallafa wa tattalin arzikin Masar da ya taɓarɓare.

    Rikicin taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar da ake fama da shi ya sa yawan ƴan ƙasar Masar ke ƙoƙarin tsallakawa zuwa Turai musamman ta ƙasar Libya, tun bayan da mahukuntan ƙasar suka rufe hanyar da ta fito daga gaɓar tekun arewacin Masar.

    Masar ta ƙuduri aniyar daƙile masu yin ƙaura zuwa Turai ba bisa ƙa'ida ba.

    Shugaban Masar Abd el-Fattah al-Sisi ya ce "Wannan zai ƙunshi magance tushen abubuwan da suke haifar da yawan ƙaura ta hanyar samar da hanyoyin ci gaba da inganta hanyoyin hijira na yau da kullum."

    A baya dai ƙungiyar ta Tarayyar Turai ta ƙulla irin wannan yarjeniyoyin da sauran ƙasashen Afirka da ke zama a matsayin shahararrun hanyoyin yin hijira zuwa Turai da suka haɗa da Tunisiya da Libya da kuma Mauritania.

    • Ƙaura mai hatsari da ba a cika dawo ba
    • Yadda ƴan ci-rani ke jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen tsallaka teku
  6. Tinubu ya yi alƙawarin hukunta makisan sojoji a kudancin Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

    Manyan jami’an soji huɗu da sojoji 12 aka kashe a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya bayan rikicin da ya faru a yankin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli a jihar Delta.

    “Hedikwatar tsaro da babban hafsan sojin ƙasa na ƙasar sun samu amincewa ta hukunta duk wanda aka samu da hannu a mummunan aika-aikar da aka yi kan al’ummar Najeriya.” In ji Shugaba Tinubu.

    Tinubu ya yi magana ne sa’oi bayan da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa wasu ɓata-gari sun cinna wuta kan gidaje da dama a yankin na Okuama yayin da mazauna wurinsuka tsere saboda fargabar harin ramuwar gayya.

    Kakakin rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau ya shaida wa BBC cewa ba shi da masaniya game da harin na ɓata-gari kan yankin na Okuama. Sai dai ya jaddada cewa dole ne sojoji su ƙwato makaman da aka sace daga sojojin da aka kashe.

    Wasu yankuna da ba sa ga maciji da juna game da mallakar fili sun sha tafka hatsaniya a makonnin baya-bayan nan lamarin da ya janyo mutuwar gomman mutane kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka sanar.

    • Ƴanbindiga sun sake sace mutum 61 a Kaduna
    • Aikinmu kare mutane ne ba kashe 'yan ƙasa ba - Babban hafsan tsaron Najeriya
  7. Salam Alaikum!

    Masu bin mu a wannan shafi na Kai Tsaye da BBC Hausa ke kawo muku a kowace rana, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo maku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a duniya – musamman a Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Za ku iya garzayawa shafukanmu na sada zumunta – Fesbuk da Tuwita da kuma Instagram inda a nan ma muka wallafa ƙarin labarai da bidiyo.

    Sai ku kasance tare da mu.