Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, Haruna Kakangi and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Haruna Kakangi da Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Dole sai an zakulo waɗanda suka kashe jami'an mu - Lagbaja

    Shugaban hafsan sojojin ƙasa Taoreed Lagbaja, ya ce dole sai an zakulo waɗanda suka kashe jami'ansu.

    Rundunar sojin Najeriyar ta kuma zargi al’ummar yankin Okuama da ke jihar Delta da ya kasance wurin da aka kashe sojojinsu, da cewa sun koma farfaganda maimakon tsayawa a yi bincike.

    Sojojin sun ce kisan da aka yi wa jami’nsu a jihar ta Delta abu ne da aka shirya shi.

    Wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na sojojin Najeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce maimakon al’umman yankin su taimaka wa sojoji da bayanai da za su kai ga kama waɗanda suka kashe jami’ansu, sun koma yaɗa fargagandar karya da wofi.

    Onyeama ya ce abin da suke yi ya nuna cewa kisan sojojin da aka yi wani abu ne da aka shirya tun farko kan dakarun.

    Sanarwar ta ce “Kisan wasu sojojin bataliya ta 181ta Amphobious yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya, bayan samun rahoton rikici tsakanin kabilu a yankin Okuama da kuma Okoloba da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu na jihar Delta abin Allah-wadai ne matuka.

    Sojoji 16 ne ake zargin wasu matasa sun kashe a jihar ta Delta.

    Manjo-Janar Onyeama Nwachukwu ya ce babu wata farfaganda da za ta hana kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

    Don haka, Onyeama ya buƙaci al’umma da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba, inda ya tabbatar musu da cewa babu wani harin ramuwar gayya da sojoji za su kai wa al’ummomin yankin.

  3. Mutum takwas sun mutu a ruftawar gini a Indiya

    Wani bene mai hawa da yawa ya ruguje a ranar Lahadi da tsakar dare a birnin Kolkata, da ke yammacin ƙasar Indiya.

    Magajin garin ya umurci jami’an da su zakulo duk wasu haramtattun gine-gine da aka yi a cikin babban birnin tare da ɗaukar mataki a kansu.

    A halin yanzu, adadin waɗanda suka mutu a laamrin ya karu zuwa takwas.

    Gwamnati ta sanar da biyan diyyar dala miliyan biyar ga iyalan waɗanda suka mutu da kuma dala dubu ɗaya ga waɗanda suka jikkata.

    Babban minista a yankin, Mamata Banerjee ya ziyarci wurin inda daga bisani ya je asibiti sannan ya gana da waɗanda suka jikkata.

  4. Biden da Netanyahu sun tattauna kan buƙatar ƙara kai agaji Gaza

    Shugaban Amurka Joe Biden da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun tattauna ta wayar tarho game da halin da ake ciki a Isra'ila da Gaza, in ji fadar White House - karo na farko da suka yi hakan cikin sama da wata ɗaya.

    "Shugaba Biden ya yi magana da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila don tattauna sabbin abubuwan da ke faruwa a Isra'ila da Gaza, ciki har da halin da ake ciki a Rafah da kuma kokarin kara kai agaji ga Gaza," in ji kakakin fadar White House.

    Sun ƙara da cewa cikakken bayani kan tattaunawar tasu zai zo nan ba da jimawa ba.

    Amurka ta kasance abokiyar kawancen Isra'ila kuma babbar mai ba da agajin soji, amma alaƙa na ƙara tsami tsakanin Biden da Netanyahu kan yaƙin Gaza, inda yanzu har ta kai bainar jama'a.

  5. Yadda ake haɗa kunun gyaɗa tare da AishaZkitchen

    A filinmu na girke-girken Ramadan 2024, Aisha Umar wadda aka fi sani da AishazKitchen ta koya mana yadda ake haɗa kunun gyaɗa.

  6. Gwamnan Sokoto ya kai ziyara wuraren ciyarwa na Ramadan

    Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya nuna farin cikinsa kan irin abinci mai inganci da ake bai wa mutane a cibiyoyin ciyarwa na Ramadan.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, bayan ziyara da ya kai ɗaya daga cibiyoyin a ranar Lahadi.

    Ya ce sun ɓullo da shirin na ciyarwa domin saukakawa mutane a wannan lokaci na azumi ganin irin tsadar rayuwa da ake ciki.

    "Na yi farin ciki kan irin abinci mai inganci da ake dafa wa a cibiyoyin da muka tanada domin ciyarwa a Ramadan," in ji gwamnan.

    Ya kuma hori shugabannin cibiyoyin da su guji aikata wani abu na ba daidai ba.

    Ya ce kofa a buɗe take domin karɓar shawarwari da za su kawowa jihar Sokoto ci gaba.

    Kafin fara azumin watan Ramadan ne, gwamnan Ahmed Aliyu ya ware kuɗi naira biliyan 6.7 domin ciyar da jama'a.

  7. Mun damu matuka kan halin da asibitin al-Shifa ke ciki a Gaza - WHO

    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce tana cikin "matsanancin damuwa" kan abin da ke faruwa a asibitin al-Shifa da ke Gaza.

    A wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta, shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce al'amarin da ke faruwa a asibitin na kuma sanya rayukan jami'an lafiya, masu jinya da kuma fararen hula cikin haɗari.

    Ya ce ba a jima ba da komawa aiki a asibitin, inda ya ce duk wani farmaki na soji, zai ƙara saka ayyukan lafiya, damar samun motar lafiya da kuma samar da magunguna cikin barazana.

    "Asibitoci ba za su zama wuraren daga ba, ya kamata a kare su a kuma tsagaita wuta," in ji shi.

  8. Ƙasashen Yamma sun yi Alla-wadai da zaɓen Rasha

    Kasashen Yammacin duniya sun yi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar Rasha.

    Josep Borrell, babban jami'in kula da harkokin waje na ƙungiyar Tarayyat Turai, ya bayyana a madadin ƙungiyar cewa, an gudanar da zaɓen ne cikin wani tsari na danniya.

    Ƙasashen Turai da dama da suka haɗa da Faransa da Jamus sun ce ba za su taya shugaba Putin murna ba.

    Don haka, Putin zai duba gaba da Turai idan yana son jin kalaman yabo ga gagarumin nasarar da Kremlin ta ce ya samu a zaɓen.

    Beijing ta taya Putin murna tun da farko. Shugaban China Xi Jinping ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cikakken goyon baya da al'ummar Rasha ke bai wa Putin.

    Shugabanin ƙasashen Iran da Belarus sun bayyana nasarar da Putin ya samu a matsayin nasara tabbatacciya kuma mai kayatarwa.

    Hakazalika shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro da na Cuba Miguel Diaz-Canel sun taya Putin murna.

    Dukkan shugabannin ƙasashen tsakiyar Asiya da Rasha ke da alaka ta kusa da su, sun taya shugaba Putin murnar lashe zaɓe.

  9. An kai samame kan mutanen da suka kawo tsaiko a taron shugaba Ruto

    Hukumomin a Kenya sun kaddamar da farmaki kan mutanen da suka kawo tsaiko a tarukan siyasar shugaba William Ruto a yammacin ƙasar a karshen mako.

    Hakan ya biyo bayan al’amura biyu inda ‘yan baranda suka tarwatsa tarukan shugaba Ruto a kananan hukumomin Bomet da Kericho.

    Shugaban ya je yankin Rift Valley, inda yake da karfi a siyasance, domin ƙaddamar da ayyuka da dama, a lokacin da aka kawo tarnaki ga ziyarar ta sa.

    Shugaban dai ya fusata inda ya ce shugabannin da ke tada irin wannan hargitsi suna shafar ayyukan ci gaba a yankin, inda ya kwatanta kawo cikas ɗin a matsayin wauta.

    Ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki a ranar Litinin ya umurci ‘yan sanda da su gaggauta daƙile wadanda suka aikata wannan ta’asa.

    Ministan ya gana da shugabannin tsaro na yankin inda ya ɗora musu alhakin kammala bincike tare da kamo ɓata-garin da waɗanda ke samar musu kuɗi.

  10. Ethiopia: Matsalar intanet ta bai wa mutane damar cire miliyoyi a banki

    Babban bankin kasuwanci na ƙasar Habasha na ƙoƙarin ƙwato miliyoyin daloli da abokan huldarsa suka cire bayan wani lamari da ya bayyana a matsayin wata matsala ta na'ura.

    An sace sama da dala miliyan 40 daga bankin ko kuma an tura su zuwa wasu bankuna, lokacin da abokan cinikin suka gano za su iya cirar tsabar kudi fiye da yadda suke da su a asusunsu.

    An dauki sa'o'i da yawa kafin bankin ya dakatar da duk wata hada-hadar bankin.

    Ana tunanin hare-hare ta intanet ne musabbabin matsalar da aka samu.

    Shaidu sun shaida wa BBC cewa an tsare wasu ɗalibai a harabar jami'o'i, inda akasarin cire kudaden ya faru.

  11. Falasɗinawa na neman agaji ido rufe a Gaza cikin hotuna

    Mun samu wasu hotuna na Falasɗinawa da suka yi cincirindo wajen karɓar agaji a wajen wani rumbun ajiya na hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai agazawa Falasɗinawa a birnin Gaza.

    Lamarin ya zo ne sakamakon wani sabon rahoto da MDD ta goyi baya kan cewa ana tsammanin fuskantar matsalar ƙarancin abinci daga yanzu zuwa Mayu a arewacin Gaza, kuma a farkon watan nan, MDD ta bayar da rahoton mutuwar yara 10 saboda yunwa.

    Ga wasu hotuna:

  12. 'Yan bindiga sun sake sace mutane masu yawa a jihar Kaduna

    Rahotanni na daga jihar Kaduna na cewa wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutum fiye da 80 a garin Kajuru a wani sabon hari da suka kai garin ranar Lahadi.

    Harwayau, 'yan bindigar sun fasa shaguna inda suka saci kayan abinci da sauran muhimman kayayyaki kamar yadda wani shaida ya fada wa BBC.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Mansur Hassan ya tabbatar da sace mutanen ga BBC sai dai bai fadi yawan adadin da kafafen watsa labarai ke ambatawa ba.

    Hassan ya ce nan ba da jimawa ba za su sanarwa da manema labarai da jama'a iya adadin mutanen da aka sace kasancewar har yanzu ana tantancewa.

    "Eh, gaskiya mun samu wannan labari na masu garkuwa da mutane sun sake sace mutane da dama, amma har yanzu ba a san iya adadin mutanen da aka sace ba saboda daji ne gurin." in ji Hassan

    "Shiyasa kullum muke kira ga jama'a da cewa duk lokacin da suka ga gittawar waɗannan mutanen, ba sai laile sun kai hari ba, a yi ƙoƙari a sanar da mu saboda irin waɗannen wurare daji ne sosai"

    "Saboda kusan yaƙin da ake yi da waɗannan ƴan ta'adda da kusan jama'an gari ake yi.

    Hassan ya ce rundunar jihar ta tura ƙarin jami'an tsaro don bin sawun mutanen da aka ƙara sacewa.

    Harin dai na zuwa ne ƙasa da kwana biyu bayan an sace wasu mata fiya mata 15 tare da wani namiji ɗaya a ƙauyen Dogon Nama duk dai a ƙaramar hukumar ta Kajuru.

    • Wane zabi ya rage wa Najeriya wajen ceto daliban Kuriga?
    • Halin da ake ciki a Kuriga bayan sace 'yan makaranta 287
  13. 'Ana fargabar ɓarkewar yunwa a arewacin Gaza'

    Wani sabon rahoto da ya samu goyon baya daga Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce ana fargabar yunwa daga yanzu zuwa watan Mayu a Arewacin zirin Gaza.

    Rahoton ya kuma ƙara da cewa kusan rabin al'ummar Gaza na fuskantar bala'in yunwa.

    Kafin shirin inganta samar da abinci na IPC ya ayyana yunwa, sai an samu aƙalla kashi 20 na al'umma na fama da ƙarancin abinci sannan kowanne ɗaya cikin yara uku na fama da rashin abinci mai gina jiki.

    An fidda sabon gargaɗin ne yayin da ake sa rai shugaban hukumar Leken Asirin Isra'ila zai gana da masu shiga tsakani daga ƙasashen Qatar da Masar nan gaba a yau Litinin game da yiwuwar tsagaita wuta da sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Kakakin dakarun Isra'ila Daniel Hagari ya ke cewa: Yaƙi ne kan Hamas ba a kan mutanen Gaza ba, ba ma neman cutar da fararen hular da Hamas take ɓoyewa.

    Shi ya sa zamu kai wannan farmaki da taka-tsan-tsan da kulawa tare da tabbatar da cewa asibin ya ci gaba da aikin sa.

  14. Hotunan yadda BUK ta kasance bayan fara yajin aikin ma'aikatan jami'a

  15. Satar agogunan alfarma na ƙaruwa a duniya

    Wata babbar ƙungiyar tattara bayanai kan agoguna ta ce darajar agogon alfarma da aka sace ya haura a shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan tara.

    Kungiyar Watch Register da ke Landan ta ce bayananta na agogunan da suka ɓata da kuma aka sace ya ninka fiye da sau uku cikin watanni goma sha biyu da suka gabata.

    Manajan darakta, Katya Hills, ta ce agogunan alfarma ya zama kudi ga masu aikata laifi, wadanda galibi suna cinikin su a fadin nahiyoyi.

    Ta ce daya daga cikin manyan bayanai na duniya zai taimaka wa 'yan sanda da sauran su gano agogon da aka sace tare da bai wa 'yan kasuwa damar siye da siyarwa da kwarin gwiwa.

    • An fara hada agogon da zai yi aiki shekaru aru-aru
    • Satar motoci masu tsada tana karuwa
  16. Me soke yarjejeniyar sojin Amurka da Nijar ta yi ke nufi?

  17. Ma'aikatan jami'o'in Najeriya sun fara yajin aikin saboda hana su albashi

    Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da ƙungiyar da ba malamai ba (NASU) sun soma yajin aikin gama-gari a fadin kasar domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka dauka a matsayin rashin adalci da kuma sabani na biyan albashi da gwamnatin tarayya ke yi.

    Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, ya tabbatar da fara yajin aikin a cikin shirin “The Morning Brief” na gidan Talabijin na Channels, inda ya bayyana cewa ma’aikata a sassan jami’o’i daban-daban sun shiga yajin aikin.

    Ya kuma jaddada cewa wannan mataki zai ci gaba har tsawon kwanaki bakwai masu zuwa matukar gwamnati ba ta magance kokensu ba.

    Ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin samun hanyar sadarwa a hukumance daga wakilan gwamnati.

    Ya bayyana damuwarsa game da yiwuwar masu zagon kasa a cikin gwamnati, yana mai tambayar dalilin da ya sa wasu jami’ai ba su cika umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na biyan alawus-alawus na 2022 ga mambobin kungiyar jami’o’i ba.

    Ibrahim ya soki Ministan Kwadago, Nkiruka Onyejeocha bisa gazawa wajen tuntuɓan kungiyoyin kwadagon duk da ya samu sanarwar kwana bakwai da aka bayar a ranar Litinin da ta gabata.

    Ya kwatanta hakan da martanin tsohon ministan kwadago Chris Ngige.

    Idan har gwamnati ta yi watsi da bukatunsu bayan yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai, Ibrahim ya yi gargadin cewa SSANU da NASU za su koma taro domin sanin matakin da za su dauka na gaba.

    • 'Yajin aikin ASUU ya zame mana masifa'
    • Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin ƙwadago daga shiga yajin aiki a Najeriya
  18. Sojojin Habasha ‘sun kashe’ mayaƙan sa kai sama da 150 a Amhara

    Rundunar sojin Habasha ta bayar da rahoton cewa, sojojin ƙasar sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan Fano suka kai a Tis Abay, kusa da babban birnin yankin Amhara, Bahir Dar, wanda ya yi sanadin mutuwar mayakan sa kai sama da 150.

    A sakon da rundunar ta wallafa a shafin Facebook ta bayyana harin a matsayin takamaimai, wanda ya tilastawa mayakan ja da baya tare da yin watsi da gawawwakinsu da makamai.

    Kafin wannan matakin na rundunar, Fano ya tabbatar da iko da Tis Abay a ranar 16 ga watan Maris.

    Sai dai fadan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da mayaƙan Fano a yankin Amhara ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula, kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasar suka ruwaito, lamarin da ke nuni da rikicin da aka dade an fama da shi a yankin.

    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
    • Rikicin Habasha: MDD ta yi kira a tsagaita wuta
  19. 'Yan majalisar dokokin Gambia za su yi muhawara kan sauya kudirin dokar hana kaciyar mata

    A ranar Litinin ne majalisar dokokin Gambia za ta tattauna kan ko za ta yi nazari ko kuma ta yi watsi da wani ƙudirin doka da ke neman sauya dokar haramta kaciyar mata.

    Idan ‘yan majalisar sun amince su yi la’akari da shi, za a yi amfani da kudirin ta hannun wani kwamiti don ci gaba da bincike.

    Wani ɗan majalisa mai zaman kansa Almammeh Gibba ne ya gabatar da kudirin a gaban majalisar a farkon wannan watan, wanda ya ce ya yi ƙoƙarin kiyaye tsaftar addini da kiyaye ka'idoji da dabi'u.

    Ko da yake an ayyana kaciyar mata a Gambiya a matsayin laifi a shekarar 2015, wasu na neman soke haramcin da suka yi da'awar cewa ya keta 'yancin addini kuma ya sabawa al'adun kasar.

    Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da na ƙasashen waje sun yi kira ga 'yan majalisar da kada su yi la'akari da kudirin, suna masu cewa amincewa da kaciyar mata zai jefa 'yan mata da mata cikin hadari.

    Sama da kashi 73 cikin 100 na mata da 'yan mata masu shekaru tsakanin 15-49 ne aka yi musu kaciyar mata a Gambiya, wanda ke cikin manyan ƙasashe 10 na Afirka da kaciyar mata ke yaduwa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

    Yawan kaciyar mata ya ragu zuwa kashi 46 cikin 100 a tsakanin 'yan mata masu shekaru 14 zuwa ƙasa a cewar Unicef.

    Laifuka kan kaciyar mata guda biyu ne kawai aka gurfanar da su, sannan kuma aka yi wa guda ɗaya hukunci tun bayan haramta kaciyar mata a Gambia a shekarar 2015, in ji kungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International.

    • Mece ce kaciyar mata, a ina ake yi kuma me ya sa?
    • Wata likita na son a halatta kaciyar Mata
  20. Najeriya na son nazarin dokokin duniya don kare wayoyin ƙarƙashin teku

    Gwamnatin Najeriya na neman sake nazarin dokokin duniya domin kare wayoyin ƙarƙashin teku inda ta ce za ta tattauna da ƙasashe domin hanzarta yunƙurin.

    Ministan yaɗa labarai na ƙasar, Bosun Tijjani ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

    Tun ranar Alhamis ne, abokanan hulɗar kamfanonin sadarwa da bankuna suka fuskanci matsalar sadarwar intanet saboda katsewar wayoyin ƙarƙashin tekun Atalantik da ke Cote D'Ivoire ta gaɓar tekun yammacin Afirka, lamarin da ya gurgunta harkokin cinikayya ta intanet da sadarwar intanet.

    Kamfanin wayoyin ƙarƙashin teku na MainOne ya ce zai ɗauki kusan mako biyu kafin gyara matsalar da ta lalata intanet a Najeriya da Ghana da Cote D'Ivoire da Senegal da wasu ƙasashen yammacin Afirka da na gabashin yankin a kwanaki huɗun da suka gabata.

    Kamfanin ya danganta matsalar ga ayyukan masunta da girgizar ƙasa da zaizayewar laka da kuma tangarɗar na'ura.

    Ministan a saƙon nasa ya ce matsalar da aka samu za ta taimaka wajen samar da hanyoyin inganta sadarwa a Najeriya.

    Ya kuma yaba da shugabancin kamfanin na MainOne da sauran kamfanonin sadarwa a ƙoƙarinsu na taƙaita tasirin katsewar.

    Ya kuma bai wa mutanen da ke ci gaba da fuskantar matsala tabbacin cewa hukumar sadarwar Najeriya NCC tana aiki da muhimman masu ruwa da tsaki domin warware matsalar a ƙanƙanin lokaci.

    • Ƙirƙirarriyar basira za ta shafi kashi 40 na ayyukan yi a duniya, cewar IMF
    • Shawarwari bakwai kan yadda za ku yi amfani da wayarku