Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Habiba Adamu, Usman Minjibir and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Ƴansanda sun kama jami'in da ya harbi wani mutum a kasuwar Wuse

    Rundunar ƴansanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kama wani jami’in gidan gyaran hali da ake zargi da harbe wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya a kasuwar Wuse da ke tsakiyar birnin.

    Kisan mutumin dai ya janyo hatsaniya a kasuwar da yammacin ranar Talata, lamarin da ya janwo asarar dukiya.

    A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴansanda a Abuja, Josephine Adeh ta turo wa BBC, ta ce jami'in ya harbe Yahaya ne a lokacin da yake yunƙurin tserewa bayan da rundunar tsaftace Abuja ta Taskforce ta kama shi ta kuma gurfanar da shi a gaban wata kotun tafi da gidanka da ke Kasuwar Wuse, inda aka yanke masa hukunci.

    Sanarwar ta ƙara da cewa yanzu haka rundunar tana tsare da jami'in inda take gudanar da bincike.

    • Rikicin Filato: 'Na ga gawawwaki yashe a kan titi'
    • 'Sai mun sayar da rai muke zuwa binne matattu a Sudan'
  2. 'Ana amfani da yunwa a matsayin makami a Gaza'

    Ana amfani da yunwa a matsayin wani makami a yaƙin da ake yi a Gaza, a cewar shugaban manufofin ƙasashen waje na ƙungiyar tarayyar Turai.

    Josep Borrell ya bayyana yadda shigar da kayan agaji cikin zirin ya gagara, a matsayin "bala'in da bil'adama" ya haddasa.

    Wani jirgin ruwa na ƙasar Spaniya ya kai wasu kayan abincin da ake matuƙar ɓuƙata Gaza daga Cyprus, amma Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ba zai iya maye gurbin agajin da ake shigarwa ta ƙasa ba.

    Hanya mafi tasiri kuma mafi sauri ta shigar da kayan agaji zuwa Gaza ita ce ta ƙasa, sai dai ƙungiyoyin agaji sun ce hanin da Isra'ila ta yi ya sa ƙalilan ne daga cikin abubuwan da ake buƙata ake iya shigarwa zirin.

    Amma hankali ya karkata kan wasu hanyoyin, kamar ta ruwa da kuma jefawa ta sama.

    A karon farko cikin makonni, a ranar Talata hukumar Abinci ta Duniya ta samu shigar da kayan agaji arewacin Gaza.

    Shugaban kai agaji yankin Falasɗinawa da aka mamamye na MƊD, Jamie McGoldrick, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, manyan motoci sun yi amfani da titin Isra'ila da ke gefen shingen zirin wajen shigar da agajin.

    Isra'ila ta ce ba za a ɗora mata laifin ƙarancin abinci a Gaza ba, saboda tana bari ana shigar da agajin ta hanyoyi biyu ta kudanci.

    Sai dai yayin da yake jawabi ga kwamitin sulhu na MƊD a birnin New York, a ranar Talata, mista Borrell ya ce matsalar ƙarancin abinci da ake fuskanta a Gaza saboda rashin hanyoyi ne.

    Hakan na zuwa ne a yayin da Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci- gaba da kai hare-hare kudancin Gaza.

    • Isra'ila ta hana shigar da abinci Gaza - MDD
    • Ina ne Ƙudus kuma me ya sa ake taƙaddama kan shi?
  3. Habasha ta ce a shirye ta ke ta tattauna kan neman damar shiga teku

    Gwamnatin kasar Habasha ta ce a shirye take ta shiga tattaunawa kan neman damar shiga teku kamar kamfanin dillancin labaran kasar (EPA) ya rawaito.

    Ministan harkokin wajen ƙasar Taye Atske-Selassie ya ce "a halin yanzu kasashen duniya sun fahimci burin Habasha na shiga teku bayan da aka yi huldar diflomasiyya a kan batun," in ji EPA.

    Ya kara da cewa, "Samun damar shiga teku lamari ne da ya shafi zaman lafiyarmu da tsaron kasa, shi ya sa muke neman tashoshin ruwa a hukumance."

    "Habasha ba ta da tarihin rungumar umarni da ka'idoji na kasashen waje, amma za ta yi shawarwari a wasu lokuta don amfanin kowa."

    Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da ake takaddama tsakanin Habasha da Somaliya kan yarjejeniyar bai wa sojojin ruwa na Addis Ababa damar shiga jamhuriyar da ta ayyana kanta a gabar tekun Somaliland.

    • An kashe kuɗin da ba a taɓa ɓatarwa ba a yaƙi a duniya a 2022 - Rahoto
    • Murnar samun 'yancin kai a Somaliland
  4. Biden da Trump sun samu nasarar lashe zaɓukan fidda gwani takarar shugabancin Amurka

    Shugaban Amurka, Joe Biden da wanda ya gada kuma abokin hamayyarsa, Donald Trump sun yi nasara a zaben fitar da gwani bayan sun tsallake matakin wakilan jam'iyyunsu.

    An gudanar da zaɓen fitar da gwanin ne a jihohi hudu na Amurkar, da wani yanki da ke ƙarƙashin mulkin ƙasar da kuma 'ƴan jam’iyyar Democrats da ke ƙasashen waje da suka gudanar da nasu zaɓen.

    Dukkan 'yan takarar biyu sun yi nasara da isassun kuri'u a sauran jihohin da suka rage musu a ranar Talata.

    Nasarar 'yan takarar biyu, ita ce irinta ta farko a Amurkar cikin kusan shekaru 70.

    Nasarar shugaban Biden da Trump na nufin Amurka za ta sake maimaita abin da ya faru a zaben shekarar 2020, inda Donald Trump da Joe Biden za su fafata a babban zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwambar wannan shekarar.

    A nan gaba ne ake sa ran jam'iyyun za su tabbatar da takararsu a hukumance.

    • Biden da Trump sun lashe zaɓen fitar da gwani a Michigan
    • Shugaba Biden na Amurka ya caccaki Donald Trump
  5. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, BBC Hausa, barkan mu da safiya. Da fatan muna lafiya.

    A yau Laraba, kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu domin karanta wainar da ake toyawa a duniya. Akwai sauran shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Intagram inda za ku iya zuwa domin karanta karin labarai da kallon bidiyo.