Kwana guda bayan zazzafar muhawara a majalisar dattawan Najeriya - da ta haddasa dakatar da sanata Abdul Ningi, wanda shi ne shugaban ƙungiyar sanatocin arewacin Najeriya - sanatocin kudancin kasar sun farfaɗo da ƙungiyarsu tare da zaɓar shugabanni.
Ƙungiyar sanatocin kudancin ƙasar ta zaɓi sanata, Adetokunbo Abiru mai wakiltar Legas ta gabas a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.
A baya dai shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan ƙasar, Senator Opeyemi Bamidele ne ke jagorantar ƙungiyar.
Sanatoci 51 ne daga jihohin kudancin ƙasar 17 suka taro domin farfado da ƙungiyar, wata tara bayan ƙaddamar da majalisar ta 10.
Sanata Bamidele ya ce ƙungiyar ba sabuwa ba ce domin kuwa tana nan tun lokacin majalisa ta tara, yana mai cewa ayyukan ƙungiyar sun dakata ne sakamakon samun sabon muƙamin shugaban masu rinjaye na majalisar da ya samu.
Hakan na zuwa ne kwana guda da Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun 'zubar da ƙimar majalisar.'
A wani zama mai cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da ya yi da sashen Hausa na BBC.
Kalaman na sanata Ningi dai da ya yi a BBC Hausa da ma ba su yi wa fadar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu daɗi ba, inda mai magana da yawunsa ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya musanta kalaman sanatan.
Haka nan lamarin ya janyo cece-ku-ce a faɗin ƙasar, saboda ana ganin hakan a matsayin wata fallasa ta badaƙala da ke gudana a ƙarƙashin ƙasa.
Wata takarda mai dauke da sa-hannun sanata Abdul Ningi wanda shi ne shugaban kungiyar sanatocin arewacin Najeriya ta 'Northern Senators Forum', ta nuna yadda sanata Ningi ya yi murabus daga shugabancin kungiyar.
"Na ajiye aikin shugabancin kungiyar sakamakon abubuwan da suka biyo bayan takaddamar da ta wakana a zauren majalisar dattawa."