Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Habiba Adamu, Usman Minjibir and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Shugaban Rwanda zai gana da shugaban DR Congo kan rikicin ƙasashen biyu

    Shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame ya amince da ganawa da takwaransa na jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo domin ƙokarin kawo ƙarshen rikici tsakanin ƙasashen biyu, kamar yadda tashar Rediyo Okapi da Majalisar Dinkin Duniya ke daukar nauyi ta ruwaito

    Sanarwar ta biyo bayan ganawar da Kagame da shugaban Angola Joao Lourenco suka yi a birnin Luanda, wanda ƙungiyar Tarayyar Afirka ta buƙaci sasantawa tsakanin Rwanda da DR Congo.

    Fadar shugaban kasar Rwanda ta fada a shafin X cewa Kagame da Lourenco "sun amince da muhimman matakai don magance tushen rikice-rikice a gabashin DR Congo da kuma buƙatar kiyaye matakan Luanda da Nairobi don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin rikicin yankunan”.

    A watan Fabrairu ne Lourenco ya gana da Tshisekedi domin tattauna halin da ake ciki a gabashin DR Congo yayin da Angola ke ƙara kaimi a fannin diflomasiyya don kawo ƙarshen faɗa tsakanin sojojin Kongo da kungiyar 'yan tawayen M23, wadda ake zargin Rwanda ce ke marawa baya.

    A cewar ministan harkokin wajen Angola, shugaban DR Congo ya kuma amince da yin shawarwari da Kagame, amma babu tabbacin hakan daga Kinshasa.

    A nasa ɓangaren, kakakin gwamnatin Rwanda a jiya ya yi Allah wadai da zargi "marasa mutunci" da ministan harkokin wajen DR Congo Christophe Lutundula ya yi na cewa Rwanda na amfani da kisan kiyashin da aka yi wa 'yan ƙabilar Tutsi a shekarar 1994 a matsayin wani "tsabar ciniki ta siyasa".

    Ana zaman ɗar-ɗar tsakanin ƙasashen biyu dake makwabtaka da juna bisa zargin goyon bayan 'yan tawayen juna.

    • Rwanda: An kashe 'yan tawayen Hutu 19
    • Yadda aka ƙona motum 20 har lahira ciki har da marasa lafiya a Kongo
  2. Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan waɗanda ake zargi da bai wa al-Shabab kuɗi

    Ma'aikatar kuɗin Amurka ta kakaba takunkumi kan hukumomi 16 da wasu mutane bisa zarginsu da bai wa ƙungiyar al-Shabab ta Somaliya da ke da alaka da al-Qaeda kuɗi.

    “Waɗannan mutane sun hada da ’yan kasuwa masu fada a ji a yankin da ke bayar da tallafin kudi ga kungiyar al-Shabab, kungiyar da ke da alhakin kai munanan hare-hare a gabashin Afrika,” in ji gwamnatin Amurka a ranar 11 ga Maris.

    Takunkumin dai na da nufin tallafa wa ƙoƙarin da gwamnatin Somaliya keyi na yaƙi da ƙungiyar al-Shabab a fannin tattalin arziki.

    Mutanen da kuma hukumomin da aka ƙaƙabawa takunkumin suna cikin yankin Kahon Afirka da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da kuma Cyprus.

    Wannan dai ba shi ne karon farko da ma'aikatar kuɗin Amurka ta kakaba takunkumi ga mutanen da ake zargi da tallafa wa kungiyar al-Shabab ba, waɗanda aka ce suna samun sama da dala miliyan 100 a duk shekara ta hanyar karban kudade da tallafi daga wasu 'yan kasuwa masu alaka.

    • Dalilin da ya sa dakarun Amurka suka koma Somalia don yaƙar masu ikirarin kishin Musulunci
    • Harin bam ya kashe mutum tara ƴan gida ɗaya
  3. Birtaniya na fuskantar ƙarancin ayaba

    An fara fuskantar ƙarancin ayaba a manyan kantunan Birtaniya saboda matsalolin sauyin yanayi da ke tarnaki ga samar da ayabar.

    Kwararu sun ce masu son cin Ayaba na fama da tsadarta sakamakon yadda sauyin yanayi ke tasiri kan nomanta a sassan duniya.

    Wani mai sharhi kan sha'anin tattalin arzikin ayaba a Majalisar Ɗinkin Duniya, Pascal Liu, ya shaida wa BBC sauyin yanayi na janyo tsaiko da yaɗa cututtukan da ke lalata amfanin gona.

    Tun a makon da ya wuce ake fuskantar ƙaranci ko rashin ayabar a wasu kantina na ƙasar, bayan guguwar da ta faɗa a tekun Atlantika da ta janyo tsaikon dakon Ayabar ta jirgin ruwa.

    Ƙwararru za su yi taro a birnin Rom, domin tattaunawa kan wannan matsala ta ɗaya daga cikin abin da aka fi ciniki da kawo bunƙasar tattalin arziki.

    • Shin ko cin ayaba fiye 6 zai iya hallaka ka?
    • An jefi Richarlison da ayaba a wasan Brazil a Faransa
  4. 'Dakarun Isra'ila sun lakaɗa wa likitoci duka a Gaza'

    Falasɗinawa ma'aikatan lafiya a Gaza sun shaida wa BBC cewa dakarun Isra'ila sun rufe musu idanu da kyallaye, an tsare su kuma an tilasta musu tuɓe kayansu, yayin da aka yi ta lakaɗa musu duka a lokacin da sojin suka kai samame asibitin da suke aiki a watan Fabrairun da ya wuce.

    Ahmed Abu Sabha, wani likita ne a asibitin Nasser, ya bayyana yadda sojin Isra'ilan suka tsare shi na tsawon mako guda, aka cinna mishi karnunka kuma suka karya masa hannu.

    Abin da ya faru gare shi ya zo daidai da wasu likitocin biyu waɗanda suka nemi a sakaya sunayensu saboda tsoron ɗaukar matakan ramuwar gayya a kansu.

    Sun shaida wa BBC cewa an muzanta su sun dake su, sun kwara musu ruwan sanyi kuma sun sanya su tsuguno mara daɗi na tsawon lokaci.

    Haka kuma sun ce an tsare su na tsawon kwanaki kafin a sake su.

    BBC ta bayyana wa ma'aikatar tsaron Isra'ila zarge-zargensu, amma bata mayar da martani kai tsaye kan tambayoyin da aka yi mata ba game da abubuwan da suka ce an yi musu, haka zalika bata musanta azaftarwar ba a ɗaiɗai kunsu, amma ta musanta cutar da wani jami'in lafiya a yaƙin da take yi.

    Sun ce "duk wani cin zarafi na waɗanda ake tsare da su ya saɓawa umarnin ma'aikatar tsaron ta IDF, kuma don haka an haramta hakan".

    • Me ke faruwa a Asibitin Al-Shifa na Zirin Gaza?
    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
  5. Ƙasar Chadi za ta samar da ruwa da wutar lantarki kyauta ga gidaje

    A baya-bayan nan ne gwamnatin kasar Chadi ta fitar da wani shiri na samar da ƙarin ruwan sha da na wutar lantarki ga gidaje har zuwa karshen shekara.

    A karkashin wannan yunƙurin, gidaje za su sami ruwan sha da wutar lantarki kyauta a kowane wata.

    Bugu da kari, gwamnatin ƙasar ta yi alkawarin biyan bashin kudaden ruwa da na wutar lantarki da ke kan mazauna yankin.

    A wani yunkuri na rage radadin kudi, gwamnatin ta kuma sanar da rage harajin sufuri, wanda zai iya rage kudaden da ake kashewa wajen sufuri.

    Wannan shawarar ta zo ne a matsayin martani ga hauhawar farashin man fetur a baya-bayan nan, wanda ya haifar da ƙarin farashin sufuri.

    Manufar, wacce shugaban mulkin sojan Chadi kuma shugaban rikon kwarya Mahamat Deby ya amince da shi, na da nufin tallafa wa gidaje a lokutan wahala.

    Sai dai wasu 'yan kasar Chadi na kallon wannan mataki a matsayin dabarun siyasa na samun goyon bayan masu kaɗa kuri'a, yayin da Mahamat Deby ke shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓukan dake tafe tsakanin watan Mayu da Yuni.

    Duk da kokarin da gwamnatin kasar ta yi, har yanzu akwai rashin gamsuwa a tsakanin mazauna yankin, musamman a yankunan kamar babban birnin kasar, N'Djamena, inda aka shafe makonni biyu ana ɗauke wutar lantarki.

    Sai dai kuma, 'yan kasar Chadi da dama na maraba da shirin a matsayin agajin da ake bukata a cikin mawuyacin halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

    • Hanyar amfani da shara domin samar da tsaftataccen ruwan sha
    • An kashe mutum 50 a zanga-zangar Chadi
  6. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, BBC Hausa, barkan mu da safiya. Da fatan muna lafiya.

    A yau Talata, kamar kullum, za mu kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Sai ku kasance tare da mu domin karanta wainar da ake toyawa a duniya. Akwai sauran shafukanmu na sada zumunta - Fesbuk da X da Intagram inda za ku iya zuwa domin karanta karin labarai da kallon bidiyo.