Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Habiba Adamu, Usman Minjibir and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Rufewa

    Duka-duka a nan muka kawo karshen kawo muku labaran kai tsaye. Da fatan za ku kasance tare da mu da safiyar Laraba 13 ga watan Maris. Kafin nan kuma za ku iya ci gaba da karanta labaran namu a shafinmu na bbchausa.com da kuma sauran shafukanmu na soshiyal midiya. A madadin Nabeela Abubakar da Usman Minjibir muke yi muku fatan an sha ruwa lafiya.

  2. An kaddamar da cibiyar tabbatar da ingancin abinci a Najeriya

    Ƙungiyar cinikayya ta duniya WTO ta ƙaddamar da wata cibiyar haɓaka kasuwanci a Najeriya domin tabbatar da ingancin abinci.

    Cibiyar wani shiri ne na duniya da ke neman haɓaka hanyoyin inganta abinci da dabbobi da lafiyar tsirrai a ƙasashe masu tasowa ta hanyar ƙarfafa gwiwar amfani da tsare-tsare managarta.

    Da take magana a taron ranar Talata, daraktar gudanarwar WTO, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ta yi bayani cewa duk da Najeriya tana da ƙwarewa wajen samarwa da kuma fitar da wake da riɗi, rashin amincewa da abubuwan biyu na ci gaba da zama babban ƙalubale saboda rashin kyawun sufuri da alkinta albarkatun gona zuwa sauran sassan duniya.

    Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi samar da riɗi a Afirka inda ta samar da metric tan 500 a 2022 da fiye da metric tan fiye da miliyan 5.2 na busasshen wake da ake samarwa duk shekara.

    A cewar Iweala, cibiyar za ta ƙarfafa gwiwar manoman Najeriya wajen samar da albarkatun gona da za su yi daidai da yadda ake samar da su a ƙasashen duniya.

  3. Ƴan sanda sun kama gungun miyagu a jihar Anambra

    Jami'an ƴan sanda sun kama wani gungun masu aikata miyagun laifuka a ƙaramar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra.

    Ƴan sandan na rangadi ne tare da ƴan sintiri lokacin da suka gamu da miyagun riƙe da muggan makamai.

    Tawagar jami'an tsaron sun bi gungun har sai da motar da miyagun ke ciki ta faɗa wani rami.

    Bayanin hakan na cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar inda ta ƙara da cewa biyu daga cikin miyagun sun shiga hannu bayan musayar wutar da aka yi.

    A cewar sanarwar, an gano bindigogi ƙirar AK47 guda huɗu da mota ƙirar Toyota SUV.

    Rundunar ta kuma ce ta kama wata mota ƙirar Toyota Venza a ƙaramar hukumar Anaocha sai dai matuƙin motar ya tsere bayan da ya hangi jami'an tsaron.

    Binciken da suka gudanar ya kai ga gano gidan harsasai cikin motar.

    Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Aderemi Adeoye ya yaba wa jami'an da suka gudanar da aikin inda kuma ya umarci tawagar ko-ta-kwana a yankin Awkuzu su gudanar da bincike kan lamarin.

  4. Yara biyu sun mutu a gobarar da ta tashi a sansanin ƴangudun hijirar Borno

    Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta tabbatar da gobarar da ta tashi a sansanin ƴan gudun hijra a yankin Muna, lamarinda ya janyo asarar rayuka da kuma dukiya.

    Lamarain, a cewar kakakin rundunar, ASP Nahum Daso Kenneth ya faru ne da safiyar yau da ƙarfe 10.

    Ya bayyana cewa lamarin ya ritsa da yara ƙanana biyu - namiji da mace.

    ASP Kenneth, ya ce ba a kai ga sanin musabbabin tashin wutar ba amma ana ci gaba da gudanar da bincike a kai.

    Ya ƙara da cewa za su sanar da mutane abin da bincikensu ya gano game da tashin gobarar inda ya ƙaryata raɗe-raɗin da ake cewa nakiya ce da ta tashi ta haddasa gobarar.

    Jihar Borno dai na fama da rikicin masu ikirarin Jihadi fiye da shekara 10 ke nan lamarin da ya janyo asarar mutane da dama tare da ɗaiɗaita wasu.

  5. Dalilin da ya sa majalisa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi

  6. Yadda aka yi ƙone-ƙone a hatsaniyar Kasuwar Wuse da ke Abuja

    Wata hatsaniya da ta faru tsakanin rundunar tsaftace Abuja ta 'Taskforce' da ƴan kasuwar Wuse da ke Abuja ta janyo ƙone-ƙonen shaguna da mutuwar wani matashi da yammacin ranar Talata.

    Lamarin ya faru ne bayan jami'an sun kama mutanen da suke zargi da saɓa doka domin gurfanar da su a gaban kotu.

  7. Sojin Sudan sun sake ƙwace hedikwatar kafar yaɗa labaran ƙasar daga RSF

    Sojoji daga rundunar sojin Sudan sun sake ƙwace babban ofishin kafar yaɗa labaran ƙasar da ke Omdurman, birnin da ke tsallaken kogin Nilu daga Khartoum, babban birnin ƙasar, kamar yadda rundunar sojin ta sanar.

    Wannan wata gagarumar nasara ce ga sojojin a yaƙin wata 11 da dakarun RSF.

    Dakarun RSF sun ƙwace hedikwatar tun lokacin da faɗan ya ɓarke.

    Yaƙin da ake a Sudan ya janyo mutum miliyan takwas sun tsere daga gidajensu sannan kuma akwai gargaɗi kan ƙaruwar matsalar yunwa.

    Hotunan bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta sun nuna sojojin suna murna a wajen kafar yada labaran ƙasar da ke Omdurman.

    Cikin wata sanarwa, rundunar ta kira lamarin "gagarumar nasara."

    Sai dai duk da ƙwace ginin a watan Afrilu, RSF ba ta iya yaɗa shirye-shirye ba kuma gidan talabijin ɗin ƙasar ya ci gaba da nuna labaran goyon baya ga sojoji da ake yaɗawa daga wani wajen a ƙasar.

    • 'Yadda aka bar ni da gawar mahaifiyata a tsakiyar daji'
    • 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
  8. Kungiyoyin mayaƙa na Rasha a Ukraine sun yi ikirarin kai samame Rasha

    Wasu kungiyoyin sa kai na Rasha guda uku da ke Ukraine sun ce sun tsallaka zuwa Rasha inda suka fafata da sojojin gwamnati a can.

    Rundunar 'Yancin Rasha Legion (FRL) da Bataliya ta Siberiya (SB) sun wallafa faifan bidiyo da ke nuna mayaƙansu a yankunan Belgorod da Kursk na Rasha.

    Wani ɗan siyasar Rasha da ke gudun hijira ya yi iƙirarin cewa ƙauyuka biyu ne ke ƙarƙashin ikon "dakaru masu 'yanci".

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce an daƙile yunkƙurin da aka yi na samun nasara.

    Sojojin Ukraine dai sun musanta hannu a hare-haren da aka kai a ranar Talata.

    Andriy Yusov, mai magana da yawun hukumar tattara bayanan sirrin sojin ƙasar, ya ce ƙungiyoyin 'yan ta'adda "kungiyoyi ne masu zaman kansu" na 'yan ƙasar Rasha, don haka suna aiki "a gida".

    A wani labarin kuma, Rasha ta ce Ukraine ta harba jiragen sama marasa matuƙa guda 25 kan wasu wurare a faɗin Rasha, amma an daƙile harin.

  9. Yadda 'kisan' matashi ya janyo ƙone-ƙone a kasuwar Wuse

    Wata hatsaniya da ta faru a yammacin ranar Talata a kasuwar Wuse da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta janyo ƙone-ƙonen shaguna da mutuwar wani matashi.

    Lamarin ya faru ne bayan da jami'an kwamitin kula da tsarin kasuwa da masu sana'a suka kama mutanen da suke zargi da saɓa doka domin gurfanar da su a gaban kotu.

    Zuwa yanzu dai, an rufe kasuwar sakamakon ɓarkewar hatsaniyar.

    Wakilin BBC ya ruwaito cewa cikin mutanen da jami'an suka kama har da wani matashi da aka sa masa ankwa wanda ya yi yunƙurin guduwa sai dai jami'an sun bi shi tare da harbe shi.

    Lamarin dai ya fusata ƴan kasuwar da suka shiga zanga-zanga tare da farfasa motocin jami'an kwamitin.

    Jami'an dai sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da suke nuna fushinsu.

    Wasu yan kasuwar da wakilinmu ya yi magana da su sun ce kashe matashin ne ya sa aka soma ƙone-ƙone lamarin da ya haddasa gobara.

    Gobarar ta shafi shagunan sayar da atamfofi da labulai da zinare da jakunkunan mata.

  10. Atiku Abubakar ya musanta ficewa daga PDP

    Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Atiku Abubakar, ya bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da rahoton da ke cewa ya fice daga jam'iyyar.

    Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alkawarin ci gaba da marawa jam'iyyar ta PDP baya yayin da yake bayar da shawarar a gaggauta hadewar jam'iyyun adawa.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce “Na sha kiraye-kirayen ‘yan jam’iyyarmu da magoya bayanmu, da kuma ‘yan Najeriya da suka damu, dangane da labarin da aka buga da ke nuna ficewata daga jam'iyyar PDP."

    "Wannan tsantsar karya ce. Ina kara jaddada biyayyata ga jam’iyyar PDP yayin da nake ba da shawarar a gaggauta hadewar jam’iyyun adawa." In ji Atiku Abubakar.

  11. Yaƙin Gaza: Jirgin kayan agaji na farko ya bar Cyprus

    Jirgin ruwa mai ɗauke da kusan tan 200 na kayan abinci da za a kai Gaza ya bar Cyprus a ranar Talata, a wani shiri na gwaji da aka buɗe wata sabuwar hanya a teku don kai agaji ga al'ummar da ke gab da faɗawa cikin yunwa.

    An ga jirgin na Open Arms na barin tashar jiragen ruwa ta Larnaca a Cyprus, yana jaye da wani abin ɗaukar kaya da fulawa da shinkafa da kuma kayan abinci masu gina jiki a kansa.

    Sai dai ba a bayyana takamaiman inda jirgin zai tsaya ba, idan ya isa Gaza.

    Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ce ta ɗauki nauyin mafi yawan abin da ya shafi shirin kai agajin wanda wata ƙungiyar agaji da ke zaune a Amurka, World Central Kitchen (WCK) ta harhaɗa, yayin da ita kuma ƙungiyar agaji ta Spaniyar ke kai kayayyakin.

    Ƙungiyoyin agajin na da zummar kai kayayyakin kai tsaye zuwa Gaza, wanda aka raba da sauran duniya tun bayan da Isra'ila ta fara kai farmaki sakamakon harin da Hamas ta kai Isra'ilar a ranar 7 ga watan Oktobar bara.

    Ganin cewa babu wani tanadi na sauke kaya daga jiragen ruwa a Gaza, ƙungiyar ta ce za ta gina wata gada da tarkacen baraguzan gine-ginen da aka lalata a Gaza don sauke kayan.

    Ƙungiyar ta kuma ce akwai wasu tan 500 na kayan abinci a Cyprus waɗanda zata aika Gaza.

    • Yadda jefa abinci ta sama ya janyo cece-ku-ce a Gaza
    • Isra’ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar kai agaji Gaza
  12. An dakatar da sanata Ningi daga Majalisar Dattijan Najeriya

    Majalisar Dattijan Najeriya ta dakatar da sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi daga majalisar na tsawon wata uku bayan zargin shi da furta kalaman da ake ganin sun 'zubar da ƙimar majalisar.'

    A wani zama cike da hatsaniya, majalisar ta bai wa sanatocin damar yin bayani ɗaya bayan ɗaya, inda kusan dukkanin su suka nuna rashin jin daɗi kan kalaman sanata Ningi a wata tattaunawa da kafar yaɗa labaru ta BBC.

    Tattaunawar da Sanatan yayi da BBC Hausa ta tayar da ƙura a faɗin ƙasar, bayan da ya furta cewa akwai kasafin kuɗin ƙasar kala biyu da ke da su a yanzu.

    Ya ce "Bajet (budget) ɗin da aka yi, bayan wanda majalisa ta yi a fili an koma an yi wani bajet a ƙarƙashin ƙasa,"

    Ya ƙara da cewa "abubuwan da muka gani sabbi ba mu taɓa jin labarin su, amma har yanzu ƙararru na fannin kuɗi da muka ɗauka suna kawo mana bayanan yadda abubuwan suke faruwa,"

    "Misali, an yi bajet na tiriliyan 28 amma mu da muka kididdige sai muka ga bajet ɗinnan kusan tiriliyan 25 ne, ka ga akwai tiriliyan uku, a ina suke?"

    Sanata Ningi ya bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan lamarin kuma idan suka kamalla za su kai har wurin shugaban ƙasa domin tambayar sa ko yana da masaniya kan abun.

    Waɗannan kalamai dai ba su yi wa fadar shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu daɗi ba, inda mai magana da yawunsa ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya musanta kalaman sanatan.

    Haka nan lamarin ya janyo cece-ku-ce a faɗin ƙasar, saboda ana ganin hakan a matsayin wata fallasa ta badaƙala da ke gudana a ƙarƙashin ƙasa.

    A lokacin zaman majalisar na yau Talata an bai wa Sanata Ningi damar yin nasa bayanin, inda ya bayyana cewa bayanin da ake yaɗawa "ya sha bamban da abin da ya faɗa a cikin tattaunawarsa da BBC."

    Da farko dai an gabatar da buƙatar dakatar da sanatan na tsawon shekara ɗaya, sai dai daga bisani, sanata Garba Maidoki daga jihar Kebbi ya buƙaci a rage hukuncin zuwa dakatarwa na wata uku, tare da bai wa Ningi damar rubuta takardar neman afuwa.

    A ƙarshe majalisar ta cimma matsaya, inda ta yanke wa sanata Ningi dakatarwa ta tsawon wata uku.

  13. Shugaban sojojin Gabon na shirin tattaunawa kan miƙa mulkin ƙasar

    Shugaban sojojin Gabon, Brice Oligui Nguema, ya kaddamar da shirin tattaunawa da nufin magance lokacin mika mulki da kuma tsara makomar kasar, kamar yadda wani shafin intanet na labarai na aLibreville mai zaman kansa ya ruwaito, a ranar 11 ga Maris.

    Nguema ya hau ƙaragar mulki bayan hamɓarar da shugaba Ali Bongo a watan Agustan 2023.

    Taron wanda aka tsara zai gudana ne a babban birnin ƙasar Libreville daga ranar 2 zuwa 30 ga watan Afrilu, tattaunawar za ta kunshi halartar jam'iyyun siyasa daban-daban.

    Archbishop Jean Patrick Iba-Ba shine Jagoran tattaunawar.

    Tattaunawar na da nufin tantance tsawon lokacin mika mulki da kuma gabatar da sauye-sauye na siyasa da na tattalin arziki da na zamantakewa ga al'ummar ƙasar bayan samun nasarar juyin mulkin, kamar yadda bayanai suka nuna daga wata sanarwa da shugaban sojojin ya fitar.

    Bugu da kari, gwamnatin da sojoji ke jagoranta ta fitar da shirin aiwatar da sabon kundin tsarin mulki ta hanyar zaben raba gardama zuwa karshen shekarar 2024.

    Nguema ya kasance yana tuntubar jami'an siyasa na cikin gida da cibiyoyin yanki, amma ya kau da kai daga ɗaukar kwararan alkawura kan ci gaba da mulki.

  14. Laberiya ta kori wasu jami'an tashar jiragen ruwa kan cin hanci da rashawa

    Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta ƙasar Laberiya (NPA) ta kori wasu manyan jami'ai 10 bayan an zarge su da cin hanci da rashawa.

    Sekou Hussein Dukuly, Manajan Darakta na NPA, ya ce mutanen suna da hannu wajen aikata "almundahana".

    Ya ce an samu mutanen da laifi ne "bayan bincike cikin gida da aka gudanar".

    Mista Dukuly ya kuma ce an aika da ƙara zuwa ga ‘yan sanda domin gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kuliya.

    Sai dai wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna shirin ɗaukar matakin shari'a a kan hukumar ta NPA.

    "Na samu wasikar kora daga hukumar ne kawai, amma lauyoyina sun ce kada in yi tsokaci kan zarge-zargen," Pewu Flomoku, daya daga cikin wadanda ake tuhumar, ya shaida wa BBC.

    Tsohon manajan tashar jiragen ruwa na Buchannan, Civicus Barsi-Giah ya kira matakin a matsayin siyasa kuma ya ce bai sami takardar dakatarwa a hukumance ba kuma ya ce ba a sanar da shi wani bincike na cikin gida ba.

    Hukumar ta NPA ta kuma bayar da rahoton wasu jami’an tashar ruwa guda bakwai bisa zargin haɗa baki wajen sace manyan motoci 20 na shinkafa a tashar, a makon jiya.

    Matakin na NPA ya zo daidai da sanarwar da shugaban ƙasar Joseph Boakai ya bayar inda ya ce yana kafa wata rundunar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.

  15. Ruɗani a Majalisar Dattijan Najeriya kan zargin cushe a kasafin kuɗi

    Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattijai yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar, wanda shugaban ƙungiyar sanatocin arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.

    Tun da farko shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Sen. Olamilekan Adeola daga jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da sashen Hausa na BBC.

    Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi kan cewa ana amfani da kasafin kuɗi iri biyu a ƙasar.

    Sanata Adeola ya ce wannan tamkar cin zarafi ne da kuma ƙazafi.

    Ya bayyana cewa kalaman sanata Ningi ba gaskiya ba ne, kasancewar tun asali babu kuɗin da aka ware a wasu ma'aikatu a cikin kasafin kuɗin da majalisar ta amince da shi.

    Sai dai Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya yi adalci wajen jin tabakin Sanata Ningi kan kalamansa a hirarsa da BBC Hausa.

    A lokacin da ya yi sa'ilin muhawarar, Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara ce.

    • Majalisar dattijan Najeriya za ta iya adawa da bukatar CBN ta dala
    • Wane ne Godswill Akpabio, sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya?
  16. Giwa ta tattake wani jagorar yawon buɗe ido a Afirka ta Kudu

    Masu rajin kare haƙƙin bil'adama na jimamin rasuwar wani jagorar yawon buɗe ido ɗan kasar Zimbabwe da wata giwa ta tattake har ya mutu a wani gandun daji na Gondwana da ke Afirka ta Kudu.

    David Kandela, mai shekaru 36, yana jagorantar gungun masu yawon bude ido ne a yammacin Lahadin da ta gabata, lokacin da bala'in ya faru, in ji masu kula da gandun dajin a cikin wata sanarwa da kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.

    Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne yayin da tawagar giwaye ke wucewa ta sansanin Eco na Gondwana.

    Sanarwar ta kara da cewa, "Tawagar giwayen sun kusa wucewa ta sansanin lokacin da Kandela ya ci karo da giwa ta karshe da ta rage kafin afkuwar lamarin."

    Abokan jagororin yawon buɗe ido da masu gudanar da yawon shakatawa sun bayyana Kandela a matsayin ƙwararre mai jagora wanda ke da sha’awar aikinsa.

    Sun ce ba kasafai irin wannan lamarin ke faruwa ba.

    Giwaye dai sun kasance babbar abun sha'awar gani a lokacin yawon bude ido a kudancin Afirka.

    • Giwar da shaƙuwarta da mutane ta zama bala'i a Indiya
    • Dabbobin da ke takarar kayatattun hotuna na namun daji na 2020
  17. An rage tsawon lokacin aiki a Jigawa da Sokoto saboda azumin Ramadan

    Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki a jihar da sa’o’i biyu ga ma'aikatan gwamnatin jihar a cikin watan Ramadan.

    Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri.

    Sanarwar ta ce a yanzu ma’aikatan za su fara aiki da ƙarfe 9 na safe kuma za su kammala da ƙarfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis sabanin ƙarfe 5 na yamma da aka saba rufewa.

    A ranar Juma'a kuma, ma'aikata za su fara da ƙarfe 9 na safe kuma za su rufe da ƙarfe 1 na rana kamar yadda aka tsara.

    Kazalika a jihar Sokoto, gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, shima ya amince da rage sa'o'in aikin ma'aikatan gwamnati saboda azumi.

    Abubakar Bawa, sakataren yaɗa labarai na Gwamnan jihar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa.

    Ya ce ma'aikata a jihar za su kammala aiki da karfe 2:30 a maimakon 4:00 daga ranar Litinin zuwa Alhamis, inda kuma a ranar Juma'a, za su rufe aiki da karfe 12 na rana.

    Jihohin biyu sun ce hakan na da nufin bai wa ma'aikatan isasshen lokaci don yin shirin buɗe baki na azumi tare da ba da damar haɓaka ayyukan ibada a cikin wannan wata mai alfarma.

    Jihohin sun kuma shawarci ma’aikatan da za su yi amfani da lokacin azumin watan Ramadan wajen yi wa jihohin biyu addu'ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki da ma Najeriya baki daya".

    • Abin da masu amfani da soshiyal midiya za su ƙaurace wa lokacin azumi
    • Yadda za ku kula da kanku lokacin azumin Ramadan
  18. Firaiministan Haiti Ariel Henry ya yi murabus

    Firaiministan Haiti, Ariel Henry ya yi murabus sakamakon matsin lamba na kwanaki da kuma karuwar tashin hankali a kasar.

    Hakan na zuwa bayan da shugabannin ƙasashen yankin Karibiyan suka gana a Jamaica domin tattauna halin da ake ciki a Haiti.

    Mista Henry ya kasa komawa gida saboda barazanar ƙungiyoyin ƴan daba, wadanda suka mamaye babban birnin ƙasar kuma a yanzu haka yana samun mafaka a kasar Puerto Rico.

    A wani jawabi da ya gabatar ta bidiyo, Mista Henry ya buƙaci ƴan ƙasar ta Haiti su kwantar da hankalinsu.

    "Na yi murabus ba tare da ɓata lokaci ba kuma za a naɗa gwamnatin riƙon ƙwarya," in ji Mista Henry.

    Henry, wanda ya jagoranci ƙasar na rikon ƙwarya tun daga watan Yulin 2021 bayan kashe tsohon shugaban kasar Jovenel Moïse, ya jinkirta zaɓe sau da dama inda ya ce sai tsaro ya inginta kafin a yi zaɓen.

    • Haiti : An bankaɗo wanda ya bada umarnin kisan shugaban ƙasar
    • Dalilai uku da ke hana shugabannin jam'iyyu ɗorewa a Najeriya
  19. 'Tsananin zafi ya haddasa ƙarancin ruwan sha a Johannesburg'

    A birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, mahukunta sun ɗora laifin ƙarancin ruwa da ake fuskanta a birnin kan tsananin zafin da ake fama da shi, lamarin da ya sa magudanan ruwa suka bushe a wasu sassan birnin na tsawon makonni.

    Hukumar Kula da Yanayi ta Afirka ta Kudu ta yi gargaɗi a jiya Litinin kan tsananin zafi da ya wuce kima.

    Hukumar samar da ruwan sha ta gwamnati ta ce karuwar yawan ruwan da mutane ke amfani da shi da kuma ƙafewar wuraren tara ruwa na ƙara ta'azzara matsalar.

    Ƙarancin ruwa ya zama ruwan dare a Johannesburg, kuma ya haifar da zanga-zanga a baya.

    Matsalar ruwan da ake fama da ita a halin yanzu ta fara ne a karshen shekarar da ta gabata amma ta kara ƙamari a 'yan makonnin nan.

    Katsewar ruwan ba gidaje kadai ya shafa ba har ma da ma'aikatun gwamnati.

    A makon da ya gabata, gidaje da dama ciki har da asibitoci, an tilasta musu sayen ruwa daga tankunan ruwa bayan da tsawa ta lalata wata babbar tashar tace ruwa, lamarin da ya janyo katsewar samar da ruwan sha na tsawon kwanaki.

    • Rashin lantarki ya jefa ƴan Afrika ta kudu cikin ƙaracin ruwa
    • Ko Afirka ta Kudu za ta rungumi fasahar makamashin hasken rana?
  20. Babu sahalewar Buhari a yawancin kuɗaɗen da CBN ya fitar - Fadar shugaban ƙasa

    Fadar shugaban Najeriya ta ce yawancin kuɗaɗen da aka fitar daga Babban bankin ƙasar (CBN) ƙarƙashin shugabancin Godwin Emefiele, an fitar da su ne ba tare da sa hannun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.

    Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi a shirin With Chude na Chude Jideonwo wanda aka watsa a gidan talabijin na Channels.

    Ngelale ya ce dole ne gwamnatin da ta gabata ta ɗauki alhakin wasu abubuwan da suka faru a babban bankin ƙarƙashin jagorancin Emefiele.

    Ngelale ya jaddada cewa, yayin da Buhari ya samu nasarori a wasu fannonin samar da ababen more rayuwa, rashin sanya ido kan al’amuran Babban bankin ya taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar.

    Duk da cewa ya amince cewar Bola Tinubu ya bai wa gwamnati tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari goyon baya, Ngelale ya ce a yanzu Tinubu na ƙoƙarin ganin ya magance matsalolin da suka haifar da taɓarɓarewar tattalin arzikin kasar da ta faru a zamanin gwamnatin Buhari.

    Ngelale ya yi nuni da cewa Buhari ne ya yanke shawara dangane da tsawaita wa’adin mulkin Emefiele, duk kuwa da cewa shugaban bai san al’amuran da ke gudana a Babban Bankin ba.

    Ngelale ya bayar da misali da yadda Babban Bankin ya fitar da kuɗi dalar Amurka miliyan 6.2 ga masu sa ido kan zaɓuka daga ƙasashen waje, wanda aka ce da sa hannun Buhari ne, inda daga baya aka yi zargin jabu ne.

    Emefiele, wanda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya naɗa tun farko, ya ci gaba da zama gwamnan CBN a gwamnatin Buhari.

    Sai dai kuma ya fuskanci shari’a a watan Yunin da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa da suka hada da na sa hannun bogi da kuma karbar kudi ta hanyar ƙarya.

    • Dalilin da ya sa tattalin arziƙin Najeriya ya shiga mummunan hali
    • Yadda sabbin ƙa’idojin CBN za su shafi kasuwar canjin kuɗi