Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.

    Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da rundunar ƴan sa kai

    Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da sabuwar rundunar ƴan sa kai a jihar.

    Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya jagoranci kaddamar da rundunar ta ƴan sa kai, inda ya ce sun kafa rundunar ce domin ta taimaka wajen yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da shi a jihar.

    Ya ce an zaɓo ƴan sa kai ɗin ne bisa cancanta, kuma an zaɓo su ne domin taimakawa jami’an tsaro wurin magance matsalar tsaro.

    Gwamnan ya yi kira ga jami’an rundunar da su tsaya wajen aiki tukuru, inda ya tabbatar wa al’umma cewa zai cika dukkan alkawuran da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe da suka haɗa da samar da tsaro, ilimi, noma da sauransu.

    Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda aka ɗaiɗaita dubban mutane da tilasata musu tserewa gidajensu, abin da ya kwatanta hakan da barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da kuma tattalin arzikin ƙasa.

    Haka nan, gwamnatin jihar ta samar musu da motoci da kuma babura don samun nasarar ayyukansu.

    Yayin kaddamar da rundunar, gwamnonin jihohin arewa maso yamma, sun yi alkawarin aiki tare da kuma samar da tsari guda wajen ganin an magance matsalolin tsaro da yankin ke fama da su.

    Da yake magana, gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katina, ya ce haɗin kai daga jihohin zai taimaka ainun wajen shawo kan matsalar tsaro da kuma tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a yankin.

    A don haka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo wa jihohin ɗauki ta hanyar mara wa tsarinsu don kawo karshen rashin tsaro.

    Mutanen da suka samu halartar bikin sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar, gwamnonin jihohin Kano, Bauchi, Benue, Filato da kuma Janar Aliyu Gusau mai ritaya, inda suka yaba wa gwamnan bisa wannan kokari na kafa rundunar tsaro da nufin magance matsalar tsaro.

    Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da ayyukan ƴan bindiga, garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da kuma fashi da makami.

    A baya-bayan nan ma, jihohin Katsina da Zamfara suka kaddamar da sabbin rundunonin tsaron, waɗanda suka ce za su ba da gudummawa wajen yaƙi da ayyukan ƴan bindiga da suka addabi jihohin.

  3. Mun ɗau alwashin ceto mata da kuma ɗalibai da ƴan bindiga suka sace - Gwamnatin Tarayya

    Gwamnatin tarayya ta sha alwashin hada karfi da karfe don ganin an kuɓutar da ɗaliban makarantar Sakandaren Gwamnati ta Kuriga da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna da kuma ‘yan gudun hijira a unguwar Wurge da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su.

    Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce gwamnati ba za ta lamunci sace mutane ba, kuma ya saɓa wa ɗabi’u na ɗan Adam.

    Ya ce gwamnati tana Alla-wadai da duk wani nau'i na tashin hankali ko afka wa jama'a da ba su ji ba ba su gani ba, musamman marasa galihu.

    Idris ya bayyana cewa yara sun cancanci neman ilimi a yanayin da babu cutarwa, kuma duk wata barazana da za ta iya kawo musu cikas a karatu, to barazana ce ga zaman lafiyar ƙasar.

    Yayin da yake jajantawa iyalai da kuma al’ummar da abin ya shafa, Idris ya ce shugaban Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta ganin an ceto dukkan waɗanda aka sace, tare da kamo waɗanda suka yi wannan aika-aika.

    A cewarsa, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yi wa waɗanda abin ya shafa adalci da kuma tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata laifin bisa tsari na doka.

    Ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu amma su rika sa ido, sannan su bai wa jami'an tsaro bayanai da suka dace waɗanda za su taimaka musu.

    "Aiki tare da haɗin kai na da matukar muhimmanci idan har muna son a yaki matsalar ‘yan fashi, ta-da kayar baya da kuma rashin tsaro a ƙasarmu yadda ya kamata."

    “Bugu da kari, gwamnati na sake jaddada kudurinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa, kuma za ta ci gaba da yin aiki tukuru don ganin ta kawo karshen ɓata-gari," in ji sanarwar.

  4. Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci a fara duban watan azumi daga gobe Lahadi

    Kwamitin duban wata na Najeriya ya umarci ƴan kasar da su fara duban jaririn watan azumin Ramadan daga ranar Lahadi.

    Wata sanarwa da kwamtin ya fitar, ta ce Lahadi ce 29 ga watan Sha'aban, rana kuma ta farko da za a duban watan na azumi.

    Don haka ne, Kwamitin duban watan (NMSC), ya umarci duk wanda ya ga jaririn watan na azumi da ya yi kokarin sanar da ita ta hanyoyi da aka saba.

    A ranar Litinin ne, ake sa ran al'ummar Musulmi a faɗin duniya za su tashi da azumi idan har aka ga wata a gobe Lahadi.

  5. Ƴan bindiga sun kashe masallata biyu a Kaduna

    Ƴan bindiga sun kai hari kan wani masallaci a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, tare da kashe wasu masallata guda biyu.

    Hukumomin ƴansanda a jihar sun tabbatar da afkuwar lamarin.

    Wani shugaban al'umma a karamar hukumar, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ƴan bindigar sun afka wa masallacin ne a anguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa da misalin karfe 2 ranar Juma'a, inda suka buɗe wuta kan masallatan.

    Ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.

    A cewarsa, ƴan bindigar sun isa masallacin ne lokacin masu salla ke kai raka'a ta biyu, inda wasu daga cikin suka tsere.

    Harin na ranar Juma'a na zuwa ne kwana guda bayan da ƴan bindiga suka sace ɗalibai 287 a wata makarantar sakandare a Kuriga da ke karamar hukumar Chikun na jihar ta Kaduna.

  6. Sweden da Canada sun koma kai agaji a Gaza

    Sweden da Canada sun ce za su koma biyan kuɗaɗen ga ƙungiyar agaji ta Falasɗinawa.

    Suna cikin ƙasashe 16 da suka dakatar da kai agaji Gaza, bayan da Isra'ila ta zargi ma'aikatan ƙungiyar agajin ta UNRWA 12 da hannu a harin ranar 7 ga Oktoba da aka kai Isra'ila.

    Majalisar Ɗinkin Duniya na bincike, sannan ministan harkokin wajen Faransa na jagorantar yin duba kan batun.

    A ranar Asabar, Sweden ta ce za ta aika kuɗi $19m wanda ta yi niyyar bayar wa tun da farko, bayan da UNRWA ta amince ta yi bincike kan kuɗaɗen da take kashewa da kuma kan jami'anta.

    "Gwamnati ta ware $39m domin bayar wa a matsayin agaji a shekara ta 2024. Za mu fara bayar da $19m a farko," in ji wata sanarwa da ƙasar ta fitar.

    Hakan na zuwa ne bayan da Canada ta bayyana a ranar Juma'a cewa za ta sake komawa bayar da kuɗaɗen agaji ga ƙungiyar agaji ta Falasɗinawa a Gaza yayin da za a ci gaba da bincike kan jami'anta.

    A ranar 7 ga Oktoba, mayakan Hamas suka kaddamar da hari kan Isra'ila, tare da kashe mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da sama da 250.

    Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kaddamar da jerin hare-hare ta sama da kuma ƙasa a faɗin Zirin Gaza.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce sama da mutum 30,900 ne aka kashe a Gaza, kuma yawan agaji da ke isa ga fararen hula ya yi ƙasa sosai.

  7. 'Rashin tsaro ya ɗaiɗaita ƴan Najeriya sama da miliyan shida'

    Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira da Masu Ƙaura ta ce ƴan Najeriya sama da miliyan shida ne suka rasa muhallansu sakamakon rashin tsaro da kuma afkuwar bala'o'i.

    Shugaban hukumar ta NCFRMI, Tijjani Aliyu, shi ya bayyana haka lokacin da ya kai wa gwamnan jihar Katisna Dikko Radda ziyara a ranar Juma'a.

    Ya ce zuwa 2022, hukumar tana da mutum sama da miliyan uku waɗanda ambaliya da bala'o'i suka ɗaiɗaita, inda ya ce a yanzu an samu ƙaruwar mutanen da suka ɗaiɗaita da kashi 100.

    "A yau zan iya cewa, muna da ƴan Najeriya da ba su kasa miliyan 6.1 waɗanda suka rasa gidajensu.

    "Ya kamata a nemo hanyar koyawa waɗannan mutane sana'o'i da kuma ba su horo, saboda su dogara da kansu nan gaba, domin gwamnati ba za iya ci gaba da kula da dukkansu ba," in ji Aliyu.

    Ya ƙara da cewa hukumar tana yunkurin kafa cibiyoyi guda uku na koyon sana'o'i a faɗin arewa maso gabas.

    Ya ce ya kai ziyarar ce domin raba abinci ga mutane sama da 700 waɗanda aka ɗaiɗaita a jihar ta Katsina.

    Ya kuma ce sun horar da mutum 120, da kuma bai wa iyayensu da suka kai 70 kayakin yin sana'o'i domin kyautata rayuwarsu.

    Har ila yau, ya ce sun gina gidaje a yankunan da sansanonin ƴan gudun hijira suke, musamman ga waɗanda ba su da ra'ayin komawa garuruwansu na asali.

    Da yake mayar da martani, gwamna Dikko Radda, ya yaba wa hukumar da irin wannan kokari, inda ya ce nauyi da ya rataya kan wuyan gwamnatin jiha da kuma ta tarayya wajen ganin ta kula da walwala da kuma lafiyar ƴan gudun hijirar.

    Kamfanin dillancin labaran Najeirya (NAN) ya ruwaito cewa daga baya babban kwamishinan hukumar ya jagoranci sauran jami'ai wajen kaddamar da shirin raba abincin ga ƴan gudun hijirar.

  8. 'Yan bindiga sun sace daliban tsangaya 15 a Sokoto

    Wasu 'yan bindiya dauke da makamai sun kai hari kauyen Gidan Bakuso da ke yankin karamar hukumar Gada a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, tare da sace daliban wata tsangaya.

    Dan majalisar tarayyar mai wakiltar yankin, Honarabul Bashir Usman Gorou ya tabbatar wa BBC faruwar harin, inda ya ce kimanin dalibai 15 ne 'yan bindigar suka sace, da wasu mata hudu.

    Ya ce maharan sun far wa garin ne da tsakar daren ranar Juma'a lokacin da daliban ke barci.

    Honarabul Gorou ya ce daliban almajirai ne da ke karatu a makarantar Allo wadanda shekarun suka kama daga takwas zuwa 14.

    ''Baya ga daliban tsangayar, dan majalisar ya ce a yanzu haka akwai fiye da mutum 63 a yankin da ke hannun 'yan bindiga, to amma wannan shi ne karo na farko da ake sace kananan almajirai a yankin'', in ji dan majalisar.

    Kakain rundunar 'yan sandan hihar, ASP Ahmad Rufa’i, ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu rundunar ba ta samun labarin ba, amma ta aike da jami'ata zuwa yankin don tabbatar da ainihin abin da ya faru.

    Yana mai cewa zai tuntube mu da zarar ya kammala tattara bayanai daga wurin jami'ansu da ke yankin.

    Harin dai na zuwa ne a yayin da yau da rana wamnatin jihar ta kaddamar da jami'an sa kai na tsaro don magance matsalar tsaron a jihar.

    A baya-bayan nan 'yan bindiga sun zafafa kai hare-hare tare da sace mutane masu yawa a wasu yankunan arewacin Najeriya.

    Ko a ranar Alhamis da ta gabata ma wasu 'yan bindiga dauke da makamai suka kai hari makarantar furame da karamar sakandiren Kuriga a jihar Kaduna, tare da sace daliban makarantar kimanin 287.

    Haka ma makon da ya gabata wasu mahara suka sace wasu mutane mazauna sansanin 'yan gudun hijira fiye da 100 galibinsu mata da kananan yara a lokacin da suke neman itacen girki a garin Gambouro Ngala a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar

  9. Afirka ta Kudu na gina katangar kankare don dakile barayi daga makwabtan kasashe

    Hukumomin Afirka ta Kudu sun ce suna gina katangar kankare tsakanin kasar da Mozambigue don dakile barayin da ke shiga kasar don sace ko sumagal motoci.

    An ware dala miliyan 2.7 don aikin gina katandar da ta kunshi bangarori uku.

    Katangar za ta taimaka wajen dakile ayyukan bata-gari da ke kwarara kasar daga makwabtan kasashe don aikata miyagun laifuka da suka hada da satar motoci da sauran ayyuka, kamar yadda wata sanarwar hukummomin kasar ta bayyana.

    Shafin rundunar sojin Afirka ta Kudu ya ce akwai kamfanonin soji 15 da ke aikin tsaron kan iyakokin kasar, musamman kan iyakokin Mozambique da Zimbabwe da Lethoso da suka fi matsalar.

  10. Lafiya Zinariya: Alakar matsalar kiba da rashin haihuwa

  11. Rashin isassun jami'an tsaro ne ke haifar da karuwar hare-hare a Kaduna - Uba Sani

    Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce babu isassun jami'an tsaro a yankunan da ke fama da hare-hare a jihar, lamarin da ya ce shi ne babban dalilin karuwar garkuwa da mutane a yankunan.

    Gwamnan ya shaida wa BBC cewa kusan daliban makarantar Kuriga da aka sace 28 ne suka kubuta daga hannaun 'yan bindigar da suka sace su.

    Tuni dai sojojin Najeriye karkashin kulawar babban hafsan sojin kasa ke ci gaba da neman sauran yaran tare da hadin gwiwar 'yan sanda da mafarauta a dazukan Kaduna da jihohin Zamfara da Katsina masu makwabtaka.

    Su ma a nasu bangaren iyayen yaran da aka sacen sun kafa kungiyoyin 'yan sa kai tare da neman agajin gaururuwan da ke makwabtaka da Kuriga ko za su samu labarin inda 'ya'yan nasu suke.

    Nan gaba a yau ne ake sa ran mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima zai kai ziyara jihar don ganawa da gwamnan, bisa umarnin shugaban kasa na kubutar da yaran.

    Ana ci gaba da samun karuwar fargaba daga bangaren iyayen yara a yankin arewacin Najeriya, kan tsaron lafiyarsu a makarantun.

  12. Ra'ayi Riga: Kan Ranar Mata ta Duniya

  13. Gwamnatin Katsina za ta raba shinkafa ga gajiyayyu da masu bukata ta musamman

    Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta raba shinkafa ga tsofaffi da masu bukata ta musamman da ma gajiyayyu kimanin 33,000 a fain jihar.

    Cikin wani sako da gwamnan jihar Dikko Umaru Radda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a kokaruin da gwamnatinsa ke yi magance matsin rayuwa da tsadar hatsi, gwamnatin jihar za ta raba hatsi a kan farashi mai rahusa da za a sayar kan kudi naira 20,000 kowane buhu, don agaza wa masu karamin karfi a jihar.

    ''Hatsin da za a sayar kan wannan farashin su ne masara, gero, da dawa'', in ji sanarwar.

    Gwamnan ya ce kowane dan jihar na da damar sayen mudu (tiya) goma na hatsin kuma kowace tiya daya, za a sayar da ita kan kudi naira 500, idan aka kwatanta da farashin kasuwa a yanzu da ake sayarwa kusan naira 1,500, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

    Gwamna Radda ya kuma ce gwamnati za ta rika daukar nauyin dafa abinci a kowace rana cikin watan azumin Ramadan a fadin duka mazabun jihar 361 domin rage wahalhalun da tsadar rayuwa da al’ummar kasa ke fuskanta.

    ''Bugu da kari, za a yi kokarin tallafa wa manoma da karfafa aikin noma domin rage dogaro da hanyoyin samar da abinci daga waje'', in ji gwamnan.

    Tun bayan cire tallafin man fetur a shekarar da ta gabata dai shugaban kasar Bola Tinubu ya bukaci gwamnonin jihohin kasar su rika bullo da sabbin hanyoyin tallafa wa talakawan kasar don rage musu radadi.

  14. Tinubu bai fahimci mulkin Najeriya ba

    A Najeriya wasu 'yan hammaya a Majalisar Dattijan kasar, sun ce alamu sun nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu bai fahimci mulkin Najeriya ba.

    Shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Abdul Ahmed Ningi wanda ɗan jam’iyyar hammaya ta PDP ne na cikin masu bayyana hakan.

    A cikin filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon sanatan ya kuma bayanan ra'ayinsa a kan sauye-sauyen da za a yi wa wasu ma'aikatun gwamnatin kasar

  15. Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta kuɓutar da ɗaliban Kuriga

    Shugaban kungiyar Sanatocin arewacin Najeriya, Sanata Abdul Ningi ya ce yana mamakin yadda har yanzu gwamnati ta kasa kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna ta zarce zuwa Kano.

    Cikin wata tattaunawa da BBC sanatan ya ce a lokacin kasafin kudin shekarar 2014 da aka sanya makudan kudade lokacin mulkin shugaba Jonathan, amma aka yi biris da aikin.

    Ya ce ya auka a lokacin da Buhari ya zo, za a kammala aiki, amma sai ga shi tsohon shugaban ya kammala wa'adin shekarunsa takwas ba tare da kammala aikin ba.

    ''Irin wannan hanyar ta Abuja zuwa Kano a ce an kasa yinta sai ka ce an yi wa mutane baki, wanda wannan hanyar ita ce kusan ran matafiya ta motoci a yankin arewacin kasar nan', in ji sanatan dan jam'iyyar hamayya ta PDP

  16. Jirgin ruwa makare da kayan agaji ya nufi Gaza daga Cyprus

    A karshen makon nan ne ake sa ran wani jirgin ruwan dakon kaya makare da kayan agaji da ake tsananin bukata Gaza zai kama hanya zuwa yankin.

    Jirgin dakon kayan zai tashi ne daga kasar Cyprus – kasar Turai maf kusa da Gaza – inda ake sa ran zai bi ta sabbin hanyoyin jiragen ruwa da aka bude.

    To sai dai a yayin da babu tahar jiragen ruwa da ke aiki a yanki, ba a san inda jirgin zai tsaya bai dan ya isa Gaza.

    MDD ta ce kashi Daya bisa uku na al.’ummar Gaza na cikin hatsarin kamuwa da yunwa, yayin da yara kananan ke mutuwa saboda yunwa.

    Ana sa ran jirgin zai isa Gaza nan da kwanaki biyu zuwa uku masu zuwa.

    Jirgin dakon na dauke da tan 200 na abinci da wata gidauniyar Amurka mai suna, World Central Kitchen ta samar.

  17. 'Ina takaicin yadda aka kasa kammala hanyar Abuja zuwa Kano'

    Shugaban kungiyar Sanatocin arewacin Najeriya, Sanata Abdul Ningi ya ce yana mamakin yadda har yanzu gwamnati ta kasa kammala aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna ta zarce zuwa Kano.

    Cikin wata tattaunawa da BBC sanatan ya ce a lokacin kasafin kudin shekarar 2014 da aka sanya makudan kudade lokacin mulkin shugaba Jonathan, amma aka yi biris da aikin.

    Ya ce ya auka a lokacin da Buhari ya zo, za a kammala aiki, amma sai ga shi tsohon shugaban ya kammala wa'adin shekarunsa takwas ba tare da kammala aikin ba.

    ''Irin wannan hanyar ta Abuja zuwa Kano a ce an kasa yinta sai ka ce an yi wa mutane baki, wanda wannan hanyar ita ce kusan ran matafiya ta motoci a yankin arewacin kasar nan', in ji sanatan dan jam'iyyar hamayya ta PDP.

  18. Anthony Joshua ya doke Francis Ngannou

    Fitaccen ɗan wasan damben Birtaniyar nan, Anthony Joshua ya doke an wasan damben na an asalin Kamaru,Francis Ngannou a fafatawar da suka a ƙasar Sadiyya.

    Joshua, mai shekara 34, ya doke Francis Ngannou a turmin farko da na biyu da suka fafata ranar Juma'a.

    Dan wasan na Kamaru mai shekara 37 ya sha kashi ne a lokacin karawar tasu, inda har ya buƙaci kulawar lafiya.

    Karawar Joshua da Ngannou dai wani zakaran gwajin dafi ne kan abin da zai faru tsakanin sa da Fury, kuma nasarar da Joshuan ya samu wata manuniya ce ta fatan ƙara tabbata gwarzo a wasan damben Birtaniya.

    A watan Disamba Joshua ya doke Otta Wallin, ɗan ƙasar Sweden ɗin da ya zamo wa Tyson Fury ƙarfen ƙafa a tsawon shekara huɗu.

    Za a ɗauki lokaci mai tsawo duniyar damben zamani ba ta manta da gwarazan da suka fafata a fagen daga kamar Tyson Fury da Anthony Joshua ba, musamman ta la'akari da yadda sunayen su suka zamo tamkar wani suna ne na wasan damben.

  19. Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da rabon abinci don rage wa al'umma raɗaɗi

    Gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci ga mabuƙata a faɗin jihar a wani mataki na rage wa al'ummar jihar raɗadin tsadar rayuwa da ake fama da shi.

    Cikin wata sanarwar da Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwal D Sankara ya wallafava ashafinsa na Facebook, ya ce an ƙaddamar da rabon kayan abincin ne don tallafa wa al'umar jihar musamman a lokacin azumin watan Ramadan.

    Kayayyakin da aka raba sun haɗa da buhunan shinkafa da na masara da taliya. ''An zaɓo waɗannan kayayyakin abinci ne domin biyan buƙatun al'umarmu na abinci da kuma girmamasu a wannan lokacin azumi mai ƙaratowa'', in ji sanarwar.

    Kwamishinan ya ce don tabbatar da ingancin rabon kayan masarufin, gwamnatin jihar ta bi hanyar da za a kai ɗauki ga gidaje 8,000 da ba su gaza mutum uku a kowane gida ba a kowace ƙaramar hukuma.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan jihar, Umar A. Namadi, ya ce gwamnati za ta samar da cibiyoyi biyu a kowace mazaɓa da za a riƙa ciyar da mutane a binci a lokacin azumin, don tallafa wa al'ummar jihar musamman a wanna lokaci na matsin rayuwa.

    Tun dai bayan matakin cire tallafin man fetur da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya sanar cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, gwamnatoci a matakai daban-daban suka sha alwashin ɓullo da matakan rage wa al'ummar raɗaɗin rayuwa da cire tallafin man ya jefa su.

  20. Canada za ta sake dawo tallafin da take bai wa UNRWA

    Kasar Kanada ta ce za ta sake dawo da tsarin tallafa wa hukumar kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira da ta dakatar makoni shida da suka gabata.

    Ministan raya ƙasashen duniya na Kanada, Ahmed Hussein ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda mummunan halin jin kai da ake fama da shi a Gaza.

    Kasashe 16 masu bayar da tallafi da suka haɗa da Amurka da Birtaniya da Japan sun dakatar da kuɗin da suke bai wa hukumar ta UNRWA a watan Janairun da ya gabata bayan Israila ta zargi wasu ma'aikantan hukumar da hannu a hare haren da mayaƙan Hamas suka kai mata, wanda ya haddasa yaƙin da ake yi a yanzu.