Anthony Joshua ya shirya karawa da Francis Ngannou a Saudiyya

An wallafa

Ku na goyon bayan 'Gypsy King' ne, ko kuwa kuna gefen 'AJ'?

Tambayar da ta karaɗe tattaunawar wasan dambe a tsawon lokaci ke nan.

Za a ɗauki lokaci mai tsawo duniyar damben zamani ba ta manta da gwarazan da suka fafata a fagen kamar Tyson Fury da Anthony Joshua ba, musamman ta la'akari da yadda sunayen su suka zamo tamkar wani suna ne na wasan damben.

Amma a yanzu za a ci gaba da hasashe ne a kan gwabzawar da ake matuƙar jira ta faru tsakanin gwarazan, kuma tuni fitaccen mai yayata wasan dambe, Eddie Hearn ya yi hasashen cewa karawar za ta zamo mafi ƙayatarwa a tarihin wannan wasa. A yanzu dai hasashe kawai ake yi game da wanda zai yi nasara tsakanin su.

A watan Disamba Joshua ya doke Otta Wallin, ɗan ƙasar Sweden ɗin da ya zamo wa Fury ƙarfen ƙafa a tsawon shekara huɗu. Ya doke shi ne a zagaye na shida.

Wallin ya shaida wa BBC cewa "Na daɗe ina ganin cewa Fury zai doke Joshua a duk lokacin da suka kara, amma yanzu da na ɗandana yadda Joshua yake ina ganin karawar tasu sai dai yadda hali ya yi"

Joshua zai sake komawa Saudiyya domin karawa da Francis Ngannou a birnin Riyadh, a ranar juma'a. Shi dai Fury yana gefe yana jiran yadda fafatawar za ta kasance yayin da yake shirya haɗuwarsa da Joshua nan gaba.

Karawar Joshua da Ngannou dai wani zakaran gwajin dafi ne kan abin da zai faru tsakanin sa da Fury, kuma idan ya iya yin nasarar ba-zata akwai alamar zai ƙara tabbata gwarzo a wasan damben Birtaniya.

'Nasara kan Ngannou za ta ƙarfafa gwiwar Joshua domin karawa da Fury'

Duk da cewa Fury yana da wata dama ta ɗan damben farko da ya lashe gasar ajin masu nauyi har sau huɗu, Joshua ma zai iya samun damar ƙara wa kansa ƙwarin gwiwa idan har ya doke Ngannou.

A karawar da Fury ya yi da Ngannou dai, da ƙyar gwarzon ɗan damben ya yi nasara.

"Ko ta wace irin hanya Joshua ya samu nasara a kan Ngannou a karawar ranar jum'a, sai an fi ganin ƙoƙarin Joshua fiye da abin da ya faru da Tyson Fury," inji Hearn.

Makusantan Fury ne kaɗai za su iya bayyana irin shirin da ya yi kafin fuskantar Ngannou, amma Joshua wanda a baya ya bayyana damben Fury da Ngannou a matsayin wani wasan kwaikwayo na neman jan hankali, yana sane da hatsarin da ke tattare da yin sakaci da abokin karawar na shi.

"Ina ganin duk muna sane da cewa sakaci da abokin karawa yana jefa ka a cikin hatsari ne," inji Joshua.

Ya ƙara da cewa "Wannan karawa wani babban ƙalubale ne a tarihin wasan dambe. Ba za ta zo da sauki ba"

Madaddalar magoya bayan Anthony Joshua a Najeriya

Dambe a cikin jinin Anthony Joshua ya ke, inji ɗan uwansa, Raymond Ajakaye, wanda ke zaune a garin Sagamu asalin iyalan Joshua.

Harkoki za su tsaya cak a garin ranar juma'a, lokacin da ɗaruruwan mutane za su taru domin kallon karawar ɗan damben Birtaniyan da takwaransa na Kamaru, Francis Ngannou da kuma ƙarfafa gwiwar mutumin da suke wa kallon ɗaya daga cikin su.

Ajakaye ya shaida wa BBC cewa "A jinin mu yake, mu mutane ne masu jajircewa, daga kakana zuwa kawuna da kuma mahaifin Anthony Joshua,"

"Mun yi gwagwarmaya sosai da ƙalubale, kuma ina zaton daga inda ya samo baiwarsa ta dambe ke nan."

Garin Sagamu da ke kusa da Legas a yankin kudu maso yammacin Najeriya yana da mutanen da yawan su ya kai rabin miliyan.

Kamar dai yadda take a sauran sassan ƙasar, garin Sagamu yana da dimbin matasa masu kallon Joshua a matsayin abin koyi.

An haifi Anthony Oluwafemi Olaseni Joshua ne a Birtaniya a cikin watan Oktoban 989 kuma iyayensa suna da asali daga Najeriya.

Duk da cewa yana wasan dambensa ne da sunan ƙasar Birtaniya, Joshua ya shafe wani ɓangare na ƙuruciyarsa a Najeriya inda ya halarci makarantar kwana a ƙasar.

Joshua yana da zanen taswirar Afirka a kafaɗarsa, inda aka fitar da alamar kan iyakar Najeriya ƙarara. Yayin da kuma fitattun mawaƙan Najeriya, Burna Boy da Femi Kuti suka zamo ƴan rakiyarsa a lokuta da dama idan zai shiga fagen daga.

Ana taruwa a fadar basaraken Akarigbo na Sagamu domin kallon damben Joshua, a wasu manyan talabijin da ake ajiyewa a wajen.

Karawar Joshua da Ngannou za ta farfaɗo da tsohuwar hamayyar da ke tsakanin Najeriya da Kamaru a fagen wasanni.

Amma ga al'ummar wannan ɓangare na Najeriya, ba su da wani fata da ya zarce ɗansu ya yi nasara a wannan karawa.