Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge
Niger, Mali da Burkina Faso za su samar da dakarun ƙawance don yaƙar masu ikirarin jihadi
Ƙasashen Niger, Mali da Burkina Faso sun ce za su kafa wata rundunar haɗin gwiwa don yaƙar masu iƙirarin jihadi da ke yi wa ƙasashen barazana.
Shugaban dakarun sojin Nijar, Moussa Salaou Barmou ya ce nan ba da jimawa ba rundunar za ta fara aiki, to sai dai bai yi cikakken bayanin girman rundunar ba.
Moussa Salaou Barmou na jawabin ne ta gidan talabijin ranar Laraba, jim kaɗan bayan taron da ƙasashen suka yi game da batun a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.
ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da al-Qaeda sun kashe dubban mutane a yankin cikin shekarar da ta gabata.
A 'yan watannin baya-bayan nan shugabannin sojin da ke mulkin ƙasashen uku na ƙara zama manyan aminan juna.
A watan Satumban shekarar da ta gabata, suka kafa ƙungiyar Hadin kan Ƙasashen Yankin Sahel (AES), inda suka fice daga ƙungiyoyin ƙawancen 'international force' da G5 da aka kafa don yaƙar masu ikirarin jihadi a yankin.
A shekarun baya-bayan nan matsalar tsaro na ƙara ta'azzara a yankin Sahel da ke Yammacin Afirka, duk kuwa da alƙawuran magance matsalar da sojojin da ke mulkin ƙasahen suka sha yi.
Ƙasashen uku dai sun yanke alaƙarsu da Faransa, tsohuwar uwar gijiyarsu, wadda dakarunta suka kwashe shekaru da dama suna aiki a ƙasashen.
Amurka ta zargi 'yan Houthi da kashe mutum biyu a harin tekun Aden
Amurka ta ce za ta ci gaba da ɗora alhaki a kan ‘yan Houthi bayan da aka kashe akalla mutum biyu lokacin da wani makami mai linzami ya fada kan wani jirgin ruwa na Girka a gabas tekun Aden.
‘Yan kungiyar Houthi da ke Yemen sun ce matukan jirgin ruwan sun yi watsi da gargaɗin da suka yi musu ne.
Harin wanda ya raunata aƙalla mutum shida bayan waɗanda suka mutu, ya faru ne a wajen da ke da nisan kusan kilomita 100 kudu maso yammacin tashar jirgin ruwa ta Aden da ke Yemen.
Wannan shi ne hari na farko da ya haddasa mutuwa tun bayan da ‚yan HOuthi suka fara kai hari kann jiragen ruwa na kasashen duniya a watan Nuwamba da ya gabata, abin da suke yi da cewa martani ne na nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a Gaza.
Masu wannan jirgin ruwa na dakon kaya da aka ka iwa harin sun ce a na kai musu harin ne a dab da mashigar tekun Maliya, kuma a yanzu jirgin na tangal-tangal a ruwa kuma ya kama wuta.
Sauran ma’aikatan jirgin da suka tsallake rijiya da baya sun tsira ne da ‚yan kananan jiragen ruwa na ko-ta-kwana ko fito.
'Yan Houthin suna ta kai hari a kan jiragen ruwa na kasuwanci da ke dakon kaya wadanda suke bi ta tekun Malaiya da kuma gabar tekun Aden na Yemen.
MDD ta yi Allah-wadai da sace 'yan gudun hijira a Najeriya
Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da sace 'yan gudun hijira masu yawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotonni sun ce kusan 'yan gudun hijira 200 ne galibinsu mata da ƙananan yara da 'yan mata mayaƙan Boko Haram suka yi garkuwa da su a ƙarshen mako, kodayake har yanzu a hukumance ba a tabbatar da aadin mutanen ba.
Mayaƙan sun saki wasu tsoffin mata da ƙananna yara 'yan kasa da shekara 10.
Cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba, Majalisar Dinkin Duniyar ta bakin kodinetan ayyukan jin ƙai a Najeriya, Mohammed Malick Fall, ya ce sace mutanen masu yawa, ''tunatarwa ce cewa mata da 'yan mata na daga cikin mutanen da ke ciki hatsarin harin mayaƙan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin ƙasar.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a makon da ya gabata a lokacin da 'yan gudun hijirar suka tafi neman itacen girki.
yayin da yake jajanta wa iyalan 'yan uwan waɗanda lamarin ya shafa, Mista Malik Fall ya buƙaci hukumomi su samar wa mazauna sansanonin gudun hijira sana'o'i da ayyukan yi don rage hatsarin da suke ciki.
Aƙalla mutum 40,000 ne aka kashe tare da raba fiye da miliyan biyu da muhallansu cikin fiye da shekara 10 na yakin Boko Haram.
Mazauna sansanonin 'yan gudun hijira na fama da ƙarancin abinci, Inda ake kashe su ko sace su tare da tilasta musu shiga ƙungiyoyin masu dauke da makamai idan suka yi yunƙurin zuwa gonakinsu ko neman abinci.
Haka kuma a wasu lokuta mayaƙan kan ci zarafinsu, inda suke tilasta musu auren mayaƙan.
Narendra Modi zai kai ziyara mai cike da taƙaddama zuwa yankin Kashmir
Firaministan India Narendra Modi zai kai ziyararsa ta farko yankin Kashmir, da ake takaddama a kansa, wanda Musulmi ke da rinjaye tun bayan da aka soke matsayinsa na musamman a 2019.
Mista Modi zai gabatar da jawabi a babban birnin yankin Srinagar, mako biyu kafin sanar da ranakun babban zaɓen da za a yi na Indiyar
An tsaurarar tsaro sosai yayin da ‘yantawaye na aware ke ci gaba da kai hare-hare
Rahotanni na cewa jam’iyyar Bharatiya Janata za ta gayyaci dubban mutane kan su halarci taron wanda aka tsaurara tsaro a kansa.
Tayar da ƙayar baya da fafutika da makamai da ‘yan aware masu rajin ganin yankin ya samu ‘yancin kasa sun yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a yankin tun shekarun 1980.
Soki doka ta 370 ta kundin tsarin mulkin Indiya da ta tabbatar da matsayi na musamman na yankin mai kwarya-kwaryar cin gashin kai, alkawari ne da gwamnatin Mista Modi ta yi, wanda kuma cin zaɓensa ke da wuya ya aiwatar da hakan a 2019.
Dokar ta bayar da dama mai tasiri sosai ta ‘yancin kai ga jihar Jammu da Kashmir, wadda ta haɗa da ‘yancin yin tuta ta jihar da majalisar dokokinta da kundin tsarin mulki da kuma dokoki nata.
Jihar ita ce ɗaya tilo da Musulmi ke da rinjaye. Kuma tun bayan rushe wannan doka, al’ummar jihar miliyan 12 suka rabu zuwa yankuna biyu, ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya- Jammu da Kashmir, da kuma yankin Ladakh mai tsaunuka.
An jibge dubban jami’an tsaron Indiya kafin ziyarar ta Mista Modi, abin da ya tayar da hankalin al’ummar yankin ya kuma takura su wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, amma kuma mataki ne da ya samu goyon baya daga masu goyon bayan Mista Modi.
An rufe kanana da manyan makarantu a tsohuwar jihar, an kuma umarci ‘yan yawon buɗe idanu su fice, yayin da aka dakatar da layukan waya da katse intanet.
Jagororin siyasa na yankin na yi musu ɗaurin talala- a gidajensu wasu ma kuma an kai su gidajen kurkuku a wasu sassan kasar ta Indiya.
Ziyarar ta Mista Modi ta yau Alhamis, za ta buɗe babi da yadda salon yakin neman zaɓen jam’iyyarsa ta BJP a yankin zai kasance in ji masu fashin baki.
Kotun Kolin Indiya ta amince da soke dokar ‘yancin yankin a watan Disamba, amma ta ce gwamnati ta yi alkawarin mayar da matsayin jihar ta Jammu-Kashmir kuma ta gaggauta yin hakan.
Kafin jawabin da zai gabatar ga jama’a Mista Modi zai ziyarci hedikwatar sojojin Indiya da ke Srinagar.
Kasancewar sojojin a can abu ne da ake takaddama a kansa, inda ake zargin jami’an da take hakkin dan’Adam da sauran nau’uka na gallazawa tsawon gomman shekaru.
Sallama
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.
Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya tare da kasancewa da ku a wannan lokaci domin kawo muku irin wainanr da ake toyawa a fadin duniya, musamman Najeriya da makwabtan kasashe.
Kada ku manta kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.
Ku biyo mu...