Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge
Bankwana
Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na wannan rana sai kuma gobe.
Tambuwal ya gana da Obasanjo kan ƙaruwar taɓarɓarewar tattalin arziki
Tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya gana da Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, tare da koka masa kan matsin tattlin arziƙi da ake kara fuskanta a kullum.
Ya ce "lamarin ƙara ƙazanta yake a kullum," tare da buƙatar a shawo kan kalubalen da ake fuskanta cikin gaggawa.
Tambuwal ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan ganawar da ya yi da Obasanjo a Abeokuta da ke Jihar Ogun.
Kuma a cewar sanarwar da mataimakin Obasanjo kan harkokin yaɗa labarai Kehinde Akinyemi, ya fitar a ranar Alhamis, ta ce Tambuwal ya je taya Obasanjo murnar cika shekara 87 ne a raye da ya yi a wannan makon.
Tambuwal ya yi kira ga Tinubu da ya duba halin da ƙasar ke ciki domin kai mata ɗaukin gaggawa.
'Ƙwararru sun alaƙanta sinadaran gyaran gashi da sanƙarau'
Masu bincike a cibiyar bincike ta Kenya Medicines sun gano wata guba mai haɗari da ka iya haifar da cutar daji a ƙwaƙwalwa tare da haifar da mantuwa cikin sinadaran haɗa man gyaran gashi da ake yawan amfani da shi a Kenya.
Rahoton cibiyar ya nuna aƙalla nau'ikan sinadaran gyaran gashi takwas da ke da gubar sai dai masu bincike ba su ambaci sunan kamfanoni ba cikin rahoton.
"Shida a cikinsu (kashi 75) an ƙera su a Kenya sannan biyu (kashi 25) a Uganda da Afirka ta Kudu. Biyar (kashi 62.5) an liƙa takardar da ke nuna ƙwararru ne kadai ke amfani da su', kamar yadda binciken na Kemri ya bayyana.
Sinadarai daban-daban goma sha ɗaya ne aka gano cikin wasu mayukan gashi takwas.
Binciken da cibiyar ta Kemri ta gudanar an alaƙanta shi da wani da aka yi a Amurka da Ghana, da suka gano shaidar cewa yin amfani da wasu kayan gyaran gashi kamar sinadarin sauya kalar gashi da mayuka masu sinadarai na ƙara haɗarin kamuwa da sanƙarar mama da kansar hanji.
Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar samar da lantarki a karkara
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar kula da samar da lantarki ga yankunan karkara Ahmad Salihijo tare da wasu daraktocin hukumar uku, har sai baba ta gani.
Wannan ya zo bayan, "wani sabon bincike da aka yi kan yadda aka kashe kudaden hukumar," kamar yadda sanarwar da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar an mata take da "shugaba Tinubu ya dakatar da shugaban hukumar kula da samar da wutar lantarki daga aiki da shi da tawagarsa."
Baya ga Shugaban, Tinubu ya dakatar da Olaniyi Netufo da Barka Sajou Sa’adatu Balgore.
Tinubu ya ba da umarnin a faɗaɗa bincike kan jami'an hukumar kan zargin "kashe wasu kudade da suka kai naira biliyan 1.2 cikin shekaru biyu ba bisa ƙa'ida ba, wanda tuni hukumar hana yi wa ƙasa ta'annati ta ƙwato wasu," kamar yadda sanarwar ta ce.
A gefe guda kuma Shugaba Tinubu ya amince da naɗa sabon shugaban hukumar da zai kama aiki ba tare da bata lokaci ba.
Abba Aliyu shi ne sabon shugaban, sai daraktoci uku da suka haɗa da: Ayoade Gboyega da Umar Abdullahi Umar (Abba Ganduje) da Doris Uboh da kuma Olufemi Akinyelure, duka suma za su kama aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba.
Ruwa da dusar ƙanƙara sun lullube Iran
Ma'aikatar Hasashen Yanayin Iran ta yi hasashen cewa ruwa da dusar ƙanƙara za su maimaye wasu birane a Iran daga yau zuwa ranar Litinin.
Rahoton ya ce da wannan ruwan da ake yi a Iran, a yau lardin Yammaci da Gabashin Azarbajan da lardunan Ardabil, Gilan, Mazandaran, Kurdistan, Zanjan, Kermanshah, Qazvin, Alborz, Tehran, Hamedan, Lorestan, Arewacin Ilam, Chahar Mahal da kuma Bakhtiari da kuma cikin Khuzestan, za a fuskanci ruwa da ƙanƙara da kuma wata iska mai ƙarfi da dusa a wasu sassan wurin.
Rahoton hukumar ya ce gone za a samu dusar ƙanƙara da ruwa kamar da bakin kwarya a wasu sassan arewa maso yammaci, yamma da kudu maso yammaci da yankin arewaci da ke kusa da teku da kudu sannan da Alborz da kuma Zagros.
"An gano bishiyoyi na musamman" a dajin da ya haura shekara miliyan 300
Masana kimiyya a Burtaniya sun yi amannar sun gano wani curin bishiyoyi daga wani daji da ya shafe shekara miliyan 390 a gefen teku a kudu maso yammacin Ingila.
A cewar binciken da aka yi, wanda aka wallafa a mujallar Geology and Sciences, waɗannan bishiyoyin a baya ana kiransu da "Calamaphyton" kuma tsayinsu ya kai mita huɗu.
A cewar masana kimiyyar, bishiyoyin sun daɗe, kuma ba su da ganye, maimakon ganyaye, ganyensu kauri ne da shi da tsayi tamkar reshen bishiya.
Sun kuma yi amannar a baya wannan dajin na Burtaniya ba shi da bishiyoyi masu muhimmanci kamar haka, amma da wannan bincike an gano yadda waɗannan bishiyoyi da suka daɗe a duniya suka taka rawa wajen bunƙasa da tabbatar dajin na tsawon miliyoyin shekaru.
Asali da muhimmancin ranar mata ta duniya
'Yan daba sun ƙona ofisoshin 'yansanda a Haiti
'Yandaba a Haiti da ke neman hamɓarar da Firaiminista Ariel Henry sun cinnawa ofisoshin 'yansanda wuta a Port-au-Prince babban birnin ƙasar.
Wani ofishi da ke kasuwar Salomon ita aka kai wa hari na baya-bayan nan, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na gida suka wallafa.
Hare-haren 'yandaban ya ƙaru tun bayan da Mista Henry ya bar yankin bayan kammala wani taro a makon jiya.
Rikicin ya shafi matafiya, kuma si ma ya hana shi komawa.
Mista Henry ya so ya je Port-au-Prince ranar Talata amma ƙarshe ya ƙare a wani yankin Amurka da ake kira Puerto Rico.
Ya gaza sauka a babban birnin na Haiti, saboda an rufe filin jirgin saman ƙasa da ƙasar, sojoji na kare shi daga harin masu ɗauke da makamai da ke son karɓe iko da wajen.
Mista Henry bai fitar da sanarwa ba tun bayan ziyarar Kenya, inda ya je yarjejniyar da ƙasashen Afrika da za su jagoranci sojin ƙasashen ketare yajen dawo da zaman lafiya a Haiti.
'Yan daban sun yi amfani da tafiyar da ya yi suka ƙaddamar da jerin hare-hare.
Anthony Joshua ya shirya karawa da Francis Ngannou a Saudiyya
Fursunoni 300 ne ke zaune a wani gidan yari ba tare da bayanan abin da ake tuhumarsu ba
Kwamitin da babban Sufeton 'yan Sandan Najeriya ya kafa ya gano cewa akwai fiye da mutum 300 da ke zaman jiran shari’a a wani gidan yarin jihar Kano ba tare da bayanan abubuwan da ake tuhumarsu ba.
Yayin ziyarar ba-zata da kwamitin ya kai ofisoshin ‘yan sanda da kotuna da kuma gidajen yari, ya gano abubuwa da dama da suke buƙatar a sake duba yadda ake tafiyar da su a fannin yadda ake tuhuma da gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata wani laifi.
Kwamitin ya fara aiki ne, bayan da shugaban 'yan sandan ƙasar Mista Kayode Egbetokun ya kaddamar da shirin gyara ayyukan ‘yan sanda a baya-bayan nan, sakamakon kafa wata dokar ‘yan sanda da ake kira 'Force order number 20', ta yadda aikin jami’an zai zamo dai-dai da yadda aikin dan sanda abokin kowa ke gudana a duniya.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Hussaini Muhammad Gumel shi ne shugaban kwamtin a Kano, tare da wakilcin ɓangaren shari’a da ‘yan kungiyoyi da lauyoyi da kuma masu rajin kare hakkin dan adam, ya kuma ce sun fara zuwa caji-ofi-din ‘yan sanda ne tun da farko, inda suka gano abubuwa da dama.
Kazalika, CP Hussaini Gumel, yace sun kuma ziyarci kotuna, inda suka tattauna da alkalai da masu gabatar da kara, inda ya cenan gaba za su hadu da mambobin kwamitin, inda za su tattara bayanan da suka samu wuri guda, sannan su fitar da rahoto daya kana a mika wa hukumomin da abin ya shafa don daukar mataki na gaba.
Bayanai na cewa ana-sa-rai, sauran kwamishinonin ‘yan sandan jihohin Najeriya ma, za su bi sahun jihar Kano, wajen gudanar da irin wannan bincike, da nufin gyara yadda aikin ‘yan sanda da bangaren shari’a da gidajen yari suke aiki.
A kwanakin baya ne gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shirin rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya ta hanyar biya wa masu kananan laifuka tara da yi wa wasu afuwa, sai dai kawo yanzu babu bayanin ko shirin ya ci gaba bayan da aka kaddamar da shi a jihar Kano.
Ana zargin wata uwa da garkuwa da 'yarta
Ana tuhumar mahaifiyar yarinyar nan mai shekara shida da ta ɓata a Afirka ta Kudu da laifi fatauci da garkuwa da diyarta.
An gabatar da wannan tuhuma ne a kan Kelly Smith tare da saurayinta da wasu mutane biyu a shari'ar da ta ba da mamaki a kasar.
Joslin Smith ta ɓata a wajen gidansu da ke kusa da birnin Cape Town a ranar 19 ga watan Fabarairu.
Bincike ya gano rigarta da jini a jiki, amma ba a ga yarinyar ba, duk da binciken da aka ƙaddamar na hadin-gwiwa da sojojin sama da jirage marasa matuka da karnuka.
Kafin wannan lokaci mahaifiyar yarinya ta ce ba za ta saduda ba har sai an gano diyarta ta a raye.
A cikin kowanne sa'a biyar ana samun rahotannin ɓatan yara a Afirka ta Kudu.
City za ta iya sake lashe Champions League - Guardiola
Hamas ta bar wurin da ake tattaunawa a Gaza
Wakilan Hamas sun baro inda ake tataunawa a Masar kan tsaigata wuta a Gaza.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Isra'ila na nuna turjiya wajen ganin an cimma yarjejeniya tare da watsi da sharudan tsagaita wuta, janye sojojinta da barin Falasdinawa da ke gudun hijira su koma matsugansu.
Dama dai Isra'ila ba ta aike wakilanta Alkahira ba, inda ta buƙaci a soma wallafa sunaye 'yan ƙasarta da ake riƙe da su a raye.
Hamas ta ce ba za ta saduda ba har sai an samu damar tattaunawa da cimma yarjejeniya.
'An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN'
An ci gaba da shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda aka tabbatar wa kotu cewa binciken kimiyya ya nuna cewa an yi amfani da sa hannun bogi na tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wajen cire kuɗi dala miliyan 6.2 don daukar nauyin masu sanya idanu na ƙetare a zaɓukan ƙasar.
Wani shaida da EFCC ta kira, mai suna Bamaiyi Meriga ya tabbatar wa kotu ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Hamza Muazu cewa binciken kimiyya da aka yi wa takardun - da aka sanya hannu a kansu don cire kudin - ya nuna cewa sa hannu da hatimi da aka yi amfani da su wajen cire kudin ba daidai suke da na ainihi ba.
Ya kuma tabbatar da cewa sa hannun ba na tsohon shugaban najeriya Muhammadu Buhari ba ne, kuma ba na tsohon sakataren gamnatin tarayya, Boss Mustapha ba ne.
An gabatar wa alƙalin da ke jagorantar shari'ar takardun biyu, masu ɗauke da umarnin shugaban ƙasa a matsayin shaida, sannan kuma ya amince da su.
Bayan da lauyoyin Emefiele suka nuna ƙorafinsu game da takardun, shaidar ya ce shi ba ma'aikacin EFCC ba ne kuma ba hukumar ce ke biyan sa ba.
Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa, ya nuna rashin amincewarsa da shaidar, yana mai cewa shaidar ya yaudari kotun ne don kauce wa tambayoyin da za a yi masa.
To sai dai lauyan masu shigar da ƙara, Rotimi Oyedepo, bai ji dadin kalaman lauyan wanda ake ƙarar ba.
An dai ɗage shari'ar zuwa ranar 11 ga watan Maris domin ci gaba da shari'ar.
Emefiele na fuskantar shari'a a kotun kan laifuka 20 da suka ƙunshi zargin cin hanci da haɗin baki da cin amana da amfani da sa hannun bogi wajen cire kudi har dala 6,230,000.
Ana zargin sa da sa hannun bogi na tsohon sakataren gwamnatin ƙasar Boss Mustapha wajen ciye kuɗin ta hanyar da ba ta dace ba.
Man Utd na zawarcin Southgate, Barcelona na son Arteta
'Yansanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa da mutane a Najeriya
Rundunar 'yansanda Najeriya ta ce ta kama mutum 254 cikin mako biyu da take zargi da aikata miyagun laifuka a faɗin.
Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce rundunar ta samu gagarumin cigaba a yaƙi da aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar.
''Bisa koƙarin da rundunar 'yansada ta yi ta samu nasara kama mutum 254 da take zargi da aikata laifuka ciki har da 'yan fashi 92 da masu garkuwa da mutane 153 tare da mutum tara da ake zargi da aiki da ƙungiyoyin asiri'', in ji sanarwar.
Sanarwar ta ce 'yansandan sun kuma kuɓutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato ababen hawa bakwai da aka sace.
Haka kuma 'yansandan sun kuma ce sun ƙwato bindigogi 44 tare da harsasai kusan 477 da bindigogi daban-daban.
Rundunar 'yansanda ta ce ta ƙaddamar da samamen ne a jihohin Plateau da Cross River da Taraba da kuma birnin tarayyar ƙasar Abuja.
Sojoji sun ce mutum 30 sun mutu a arangama tsakanin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Benue
Sojojin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 30 a wata arangama tsakanin wasu ƙungiyoyin 'yan tayar da ƙayar baya a yankin ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar Benue, inda sojojin suka musanta batun cewa kashe-kashen na da alaƙa da rikicin makiyaya
Babban kwamandan 'Operation Whirl Stroke' kuma shugaban kwamitin tabbatar da aiki da dokar hana kiwon sake a jihar, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba yayin da jihar ta fara aiwatar da dokar hana kiwon sake, bayan cikar wa'adin mako biyu da jihar da bayar.
Yayin da yake tabbatar da kasashe-kashen na Ukum, Manjo Igbinomwanhia ya ce aikin wanzar da zaman lafiya da sojoji ke yi a ƙaramar hukumar Kwande ya taimaka wajen daidaita al'amura a yankin bayan kashe aƙalla mutum 27 a yankin mako biyu da suka gabata.
Jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu ɗauke da makamai da ke da alaƙa da ƙabilanci da addini da rikicin manoma da makiyaya.
'Herbert Wigwe ya taimake ni bayan an sauke ni daga sarkin Kano'
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmowa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami'an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.
“Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa,'' in ji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da yake jawabi muryarsa cike da alhinin.
Ya ce tsohon jami'an bankin na Acces ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.
Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce a lokacin har jirgin sama mista Herbert ya tanadar masa don ɗaukarsa daga Kano zuwa Legas.
“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faɗa masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, ‘Herbert na san irin ƙoƙarin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san saukeni za a yi''.
“Sai ya ce mini ''mai martaba, kada ka damu. duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai. A ranar da na ji sanarwa a radiyo cewa an saukeni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas''.
“An yi sanarwar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, zuwa da rana Herbert ya tanadar mini da jirgi a filin jirgin sama na Kano, sai dai a lokacin an tsara cewa za a kaini zaman gudun hijira nashekaru masu yawa, daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas, ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otal, kafin daga baya ya sama musu muhalli, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na komo Legas don ci gaba da zama tare da iyalaina''.
Muhammdu Sanusi ll ya kuma ce mista Herbert ya yi masa alawarin ɗaukar nauyin tafiye-tafiyensa bayan komawa Legas da zama.
Australiya za ta binciki kamfanin cacar intanet na Bet365
Hukumar da ke sanya idanu kan laifukan da suka shafi kudi ta Australia ta ƙaddamar da bincike kan kamfanin cacar intanet na Bet365 na Birtaniya kan biyayya ga dokokin hukumar da suka shafi almundahanar kuɗi da yaƙi da ta'addanci
A shekarar 2022 ne Cibiyar Nazarin Hada-hadar Kudin Austarliya (Austrac), ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan kamfanin.
To sai dai kamfanin na Bet365 bai ce uffan ba game da batun, a lokacin da BBc ta tuntuɓe shi kan lamarin.
Kamfanin ya shiga cikin ƙarin matsi bayan da kamfanoni caca na intanet suka ƙara samun ƙarfi a lokacin annobar korona.
"Hada-hada ba tare da cikakkun hanyoyin lura da hatsarin da ke tattare da hakan ba,kan jefa mutane cikin hatsarin cutarwa daga ɓata-gari,'' in ji Brendan Thomas shugaban cibiyar nazarin hada-hadar kuɗaɗe ta ƙasar (Austrac).
Cibiyar Austrac kan bincike bankuna da kamfanoni da gidajen caca, don tabbatar da suna bin dokokin da cibiyar da tsara don kauce wa shigar da ɓata-gari cikin hada-hadar kuɗaɗensu.