Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara

    Al'ummar garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara sun shiga wani hali bayan sun wayi gari da labarin mutuwar limamin masallacin garin, Abubakar Hassan Mada.

    Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa an tsinci gawar limanin ne, bayan wasu sanye da kayan sabuwar rundunar tsaron jihar sun tafi da shi a ranar Talata.

    Sai dai bayan wani lokaci an tsinci gawar malamin bayan an yi masa yankan rago.

    Ɗaya daga cikin mutanen garin na Mada ya shaida wa BBC cewa "Jiya da yamma bayan sallar la'asar wasu sane sa kaya irin na asakarawa suka shigo, an ce mana daga yankin Tsafe suke, sai suka haɗu da askarawa na nan Mada, suka nuna musu gidan liman Abubakar Hassan Mada,"

    Ya ƙara da cewa "Bayan da suka fita da shi wajen gari sai suka tsaya suka yi masa yankan rago."

    Mutum na biyu da BBC ta zanta da shi wanda shi ma mazaunin garin na Mada ne ya ce: "sun zo sun tafi da shi har suna dariya suna raha, ba mu yi tunanin wani abu ne maras kyau zai faru da shi ba".

    Mun fara bincike - Kwamandan Askarawa

    Sai dai a nasu ɓangaren, rundunar Askarawar Zamfara sun bayyana wa BBC cewa suna bincike kan kisan malamin.

    A tattaunawar sa da BBC, kwamandan Askarawan Zamfara, Kanar Rabiu Ƴandoto mai murabus ya ce ya zuwa safiyar ranar Laraba hukumar ta fara bincike a kan lamrin.

    A cewarsa: "Mun sa a tattara dukkanin Askarawan yankin Mada domin yin bincike game da kisan limamin."

    Sai dai ya bayyana wa BBC cewa doka ba ta bai wa wani ba'askare damar ɗaukar doka a hannunsa ba, koda kuwa ya kama wanda ake zargi da laifi.

    Mada na cikin yankunan jihar Zamfara da suke fama da mummunar matsalar ƴan fashin daji masu kashewa tare da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

    • Yadda 'yan bindiga suka sace mutum 30 lokacin sallar asuba a Zamfara
    • Askarawan Zamfara ba za su wuce gona da iri ba - Gwamna Dauda
  2. Rikicin Sudan zai iya janyo yunwa mafi tsanani a duniya - WFP

    Hukumar abinci ta duniya (WFP) ta yi gargaɗin cewa yaƙin da ake yi a Sudan zai iya janyo fitinar yunwa mafi tsanani a duniya, muddin ba a kawo ƙarshensa ba.

    Fiye da wata 10 kenan ana gabza faɗa tsakanin ɓangarori biyu da basa ga maciji ga juna, lamarin da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 14,000.

    Haka kuma rikicin ya raba mutane miliyan takwas da muhallansu kuma mafiya yawan al'ummar ƙasar ba a san me suke ciki ba, ga kuma, ƙaruwar yunwa.

    Yayin da ake ci-gaba da faɗa, yawancin iyalai na ci-gaba da tserewa zuwa ƙasashen da ke maƙwaftaka.

    Inda su kan isa sansanoni ba tare da komai ba, cikin ja'ibar yunwa suna masu matuƙar buƙatar taimako.

    Yayin wata ziyarar da ta kai wani sansani da ke Sudan ta Kudu, shugabar hukumar abinci ta duniya, Cindy McCain, ta ce an manta da mutanen da yaƙin ya shafa.

    Ta ce akwai buƙatar a bai wa hukumomin agaji damar kai wa ga waɗanda rikicin ya keɓance don taimakawa waɗanda yunwa ta addaba.

    • 'Sai mun sayar da rai muke zuwa binne matattu a Sudan'
    • 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
  3. Ambaliyar ruwa ta kashe mutane shida a Malawi

    Hukumomi a ƙasar Malawi sun ce mutane shida sun halaka, yayin da wasu huɗu suka samu raunuka, bayan ambaliyar ruwan da aka samu a sassan tsakiyar ƙasar.

    Wata sanarwa da hukumar kai agajin gaggawa ta ƙasar ta fitar a ranar Talata ta ce ambaliyar ta makon jiya ta kuma raba wasu mutane 14,000 da muhallansu.

    Kuma mafiya yawansu a yanzu suna zaune ne a sansanoni.

    Hukumar ta ce da yawa daga cikin wuraren da ambaliyar ta shafa har yanzu ba a iya kaiwa garesu, saboda hanyoyi da sauran ababen more rayuwa sun lalace.

    Hakan ya kuma kawo tsaiko wajen kai kayan agaji, inda masu kai agajin suka fi amfani da ƙananan jiragen ruwa domin isa wuraren da ambaliyar ta shafa.

    Hukumar ta kuma yi kira ga ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni da su tallafawa yunƙurin gwamnati na samar da agaji ga waɗanda lamarin ya shafa.

    Kusan shekara guda ke nan da ɗaruruwan ƴan ƙasar ta Malawi suka mutu a sanadiyyar mahaukaciyar guguwa ta Freddy da ta ratsa kudancin Afrika.

    • Mahaukaciyar guguwa da ta shafe fiye da wata ɗaya tana ɓarna
    • 'Yadda surukata ta ɓata cikin laka bayan mahaukaciyar guguwa'
  4. Trump da Biden sun yi nasara a muhimmin zaɓen fidda gwani a Amurka

    Akwai yiwuwar sake fafatawa a tsakanin ƴantakarar shugabancin Amurka tsakanin tsohon shugaba Donald Trump da kuma wanda ke kan mulki Joe Biden, kamar yadda aka gani a shekarar 2020.

    Shugaban Biden da Trump sun samu nasara a duka zaɓen da aka yi a wasu jihohi, a wata muhimmiyar rana ta zaɓen fidda gwani da aka yi a Amurka a ranar Talata.

    Lamarin da ke ƙara nuna yiwuwar su sake karawa a babban zaben ƙsar da ke tafe a wannan shekarar ta 2024.

    Yayin da ita kuma abokiyar hamayyar Trump a jam'iyyar Republican, Nikki Haley ta samu nasara a zaɓn fidda gwanin da aka yi a Vermont kamar yadda aka yi tsammani.

    Sai dai Trump ya yi matsa zarra matuƙa, inda ake tsammanin shi zai samu nasara a zaɓukan fidda gwamni 12 na jam'iyyar ta Republican.

    • Biden da Trump sun lashe zaɓen fitar da gwani a Michigan
    • Zaɓen 2020: Biden da Trump na zaryar ƙarshe kafin zaɓen Talata
  5. Barka da warhaka!

    Masu bin mu ta wannan shafi barkan mu da safiyar Laraba - da fatan za ku kasance tare da mu har zuwa ƙarshen wannan rana inda za mu riƙa kawo muku bayani kan muhimman abubuwan da ke wakana a Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru da ma duniya baki ɗaya.

    Za ku iya tafka muhawara da faɗin ra'ayoyinku kan labaran da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta: facebook, twitter, da instagram.