Mu kwana lafiya
Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage
Jama'a a nan muke cewa Allah Ya ba mu alkhairinsa.
Da fatan kun ji daɗin labaran da muka kawo muku a yau. Sai kuma gobe cikin yardar Allah.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.
An dakatar da wani malamin wata makarantar koyar da aikin likita da ke Bangladesh, kwana biyu bayan zargin harbi tare da raunata ɗalibi a aji.
An kama Raihan Sharif jim kaɗan da faruwar lamarin amma sai a ranar Laraba aka dakatar da shi sakamakon zanga-zangar da ɗalibai suka yi a kwalejin koyar da aikin likita - wurin da lamarin ya faru.
An dai yi wa ɗalibin da aka harba tiyata kuma yana ci gaba da samun kulawa a asibiti.
Dakta Shariff kuwa yana tsare a hannun ƴansanda.
BBC ba ta iya samun sa domin jin bayani daga ɓangarensa ba har sai an ba shi lauya.
Rahoto daga kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ruwaito cewa Arafat Amin Tomal, ɗalibin mai shekara 23 sun yi sa-in-sa da Dakta Sharif yayin da yake jarabawa ranar Litinin.
Yayin jarabawar, an yi zargin Dakta Sharif ya zaro bindiga tare da nuna ta ga ɗalibin inda ya harbe shi a gwiwarsa ta dama, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Harsashin bindigar ya samu wayar ɗalibin da ke cikin aljihun wandonsa, lamarin da ya sa bai ji raunin da ke barazana ga rayuwarsa ba, a cewar jaridar Daily Star wadda kamar yadda ta ruwaito ƴansanda na faɗi.
A cewar jaridar Dhaka Tribune, akwai ɗalibai 45 da ke aji lokacin da lamarin ya faru. Sun garzaya su kai agaji inda suka kulle malamin a wani ɗaki tare da kiran ƴan sanda.
Daga bisani an kama Dakta Sharif. Wata sanarwa ta ce Dakta Sharif ya harbi ɗalibin da bindigar da aka haramta.
Ƴansanda sun ce sun ƙwace bindigar da ƙarin wata da harsasai da wuƙaƙe biyu da adduna 10 waɗanda suka ce sun gano cikin jakarsa.
Ƴansanda sun ce ana zargin Dakta Sharif da ɗaukan makamai zuwa makaranta waɗanda yake nunawa yayin da yake koyarwa.
Majalisar Dattawan Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta gana da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu kan matsalolin tsaro.
Wannan ya biyo bayan wani ƙudurin buƙatar gaggawa da Sanata Emmanuel Udende ya gabatar, kan kisan sama da mutane 50 da aka yi a kimanin ƙauyuka biyar a jihar Benue, da kuma ƙaruwar rashin tsaro da ake samu a yankin Ukum da Kwnde da kuma Katsinan-Ala.
Sanata Mohammed Adamu Aleru ɗan majalisa ne daga Jihar Kebbi, ya ce akwai rahotonnin tsaro da suka gabatarwa majalisa tun daga 2015 zuwa yau amma ba a aiki da su, kuma yanzu akwai buƙatar a ɗauko su domin aiwatar da su.
Ga ƙarin bayanin da ya yi wa Buhari Muhammad Fagge.
Mace ɗaya tilo kuma ta karshe cikin waɗanda ke kalubalantar Donald Trump a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Republican, Nikki Haley, ta janye daga takara.
Da take gabatar da jawabi daga gidanta da ke South Carolina, Ms Haley ta ce kusan a yanzu Mista Trump kaɗai ne ke takara kuma zai samu tikitin tsayawa Republican a zaɓen watan Nuwamba.
Ta ce tana masa fatan alheri, sai dai ba ta furta tana goyon-bayansa ba.
Kafin janyewarta Ms Haley ta yi rashin nasara a biyu daga cikin zaɓukan fidda gwanin da aka gudanar kawo yanzu.
Duk da cewa Nikki Haley, ta samu nasarar da aka yi mamaki a Vermont a jiya Talata - hakan bai sa ta sha gaban Mista Trump ba.
Wani harin sama da makami mai Linzami da Rasha ta kai ya faɗa a birnin Odesa na Ukraine a lokacin ziyarar firaministan Girka.
Wakilin BBC ya ce firaminista, Kyriakos Mitsotakis ya ce shugaba Zelensky na kewayawa da shi tashar odesa lokacin da suka jiyo ƙarar jiniya da fashe-fashe.
A cewar kafar yaɗa labaran Girka, makamin ya faɗa ne a wani wuri da ke da tazarar kilomita 150 daga inda shugabanni suke.
Babu dai wanda ya jikkata daga harin amma sojojin ruwan Ukraine na cewa akwai mutane biyar da suka mutu.
Rasha ita ma ta tabbatar da kai wannan hari a odesa.
Ministan ma'aikatar samar da hasken wutar lantarki a Najeriya, Bayo Adelabu ya ce yana cike da damuwa kan yadda ɓangaren samar da wuta ke ci gaba da taɓarɓarewa a faɗin ƙasar.
Ministan na lantarki ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna ɓacin ransa kan raguwar wutar lantarki da ake samu duk da irin kokari da ake yi a ɓangaren.
“Dangane da haka ne na gayyaci shugabannin kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) da kamfanin rarraba wutar lantarki na Ibadan (IBEDC), da kuma Babban Darektan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Najeriya (TCN), zuwa wani muhimmin taro,” in ji ministan.
Ya ce makasudin kiran taron shi ne tattaunawa kan taɓarɓarewar wutar lantarki a yankunansu da kuma ganin an samar da mafita mai ɗorewa kan hakan.
Mista Adelabu ya ce ma’aikatarsa ta yi ta matsa wa masu samar da wutar lantarki da su ƙara kokari a ayyukansu, abin da ya sa ma har aka ƙara karfin megawat na wuta zuwa 4000.
Ya ce duk da irin ci gaba da aka samu, wasu kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun kasa rarraba wutar lantarki da TCN ke bayarwa yadda ya kamata, yayin da ake ƙara samun masu satar da kayayyakin wutar lantarki musamman a yankuna kamar Abuja, Benin, Fatakwal, da kuma Ibadan.
Ya ce ba za su lamunci rashin samar da wuta ba daga kamfanonin da alhakin haka ya rataya a wuyansu, kuma za a ɗauki mataki mai tsanani a kansu, ciki har da soke lasisi.
Ministan ya ce ana ci gaba da tsare-tsare na ganin an warware basussukan da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarki da iskar gas, wanda hakan zai rage wahalhalun da ake fama da su.
Don haka, ya buƙaci jama’a da su ƙara hakuri yayin da ake aiki tukuru wajen magance waɗannan matsaloli da kuma samarwa ƴan Najeriya wutar lantarki yadda ya kamata.
2024 shekara ce da fiye da rabin al'ummar duniya za su fita rumfunan zaɓe domin jefa ƙuri'a a wasu manyan zaɓuka da za a yi bana.
Wannan shi ne adadi mafi girma na yawan masu zaɓe a tarihi.
Bidiyon ya nuna muhimman bayanai game da zaɓukan da za su ɗauki hankalin duniya a wannan shekarar.
Maroko ta fuskanci matsanancin zafi a wannan lokaci na sanyi, inda ta ɗora alhakin hakan kan sauyin yanayi, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Yanayin zafi a ƙasar da ke arewacin Afirka ya kai maki 37 a ma'aunin Celcius.
Kasar dai na fuskantar matsalar fari tsawon shekara shida a jere.
Farin da ake fama da shi yana ƙara sanya fargaba, musamman ma ga ɓangaren noma wanda wani muhimmin fannin tattalin arziki ne.
Shugaban sashen sadarwa na hukumar lura da yanayi ta ƙasar, Houcine Youaabed, ya shaida wa AFP cewa ƙasar ta fuskanci zafi mafi tsanani a watan Janairu.
Mista Youaabed ya ce hakan na nuni da sakamakon ɗumamar yanayi da ya shafi ƙasar.
Mayakan ƙungiyar ƴan tawayen M23 sun kwace iko da garin Nyanzale da ke gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo daga hannun sojoji.
"Yanzu muna garin Nyanzale, makiya sun tsere," kamar yadda kakakin ƴan tawayen Willy Ngoma ya shaida wa sashen BBC Great Lakes.
Kwamandan sojoji Jerome Chico Tshitambwe ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ƴan tawaye sun karɓe iko da garin.
Garin Nyanzale, wanda ke da nisan kilomita 130 daga birnin Goma da ke arewacin ƙasar, ya kasance mafaka ga ƴan gudun hijira waɗanda rikici ya ɗaiɗaita da ke yankunan da ke kewaye.
Sai dai a farkon makon nan, dubban mutane sun sake tserewa garin Nyanzale bayan wani hari da aka kai.
Mista Ngoma ya ce yanzu mutane da yawa sun koma garin.
Wani mataimaki ga gwamnan lardin da ke garin Bambo, ya ce ƴan tawayen na M23 sun yi ta harbi ko ta ina kafin su kwace garin.
Ya ce mutanen da aka kashe sun kai 15 zuwa yanzu.
Dalilai da dama ne ke janyo hauhawar farashin kaya a ƙasashen duniya da ke da nasaba da sauyin yanayi da raguwar yawan kayan da ƙasashe ke samarwa.
Irin wannan yanayin kan shafi al'ummar ƙasashen da suka tsinci kansu cikin wannan hali.
Yayin da ake tunkarar watan Ramadan da al'ummar musulmi ke azumta, ga wasu nau'ikan abinci huɗu da farashinsu ya yi tashin gwauron zabi.
Ma'aikatar Lafiya a jihar Kano ta ƙaryata wani rahoto da ake yaɗawa a kafafen yaɗa labarai da ke cewa an samu ɓarkewar cutar ƙyanda a karamar hukumar birni.
Cikin wata sanarwa da ta fito daga sashen yaɗa labarai na ma'aikatar lafiyar, daraktan sashen kula da lafiyar al'umma da yaƙi da yaɗuwar cututtuka, Dakta Imam Wada Bello ya ƙaryata labarin baki ɗayansa.
Dakta Imam ya bayyana cewa kafin a ce cuta ta ɓarke, akwai wasu hanyoyi da ake bi da wasu bayanai da ake dubawa ciki har da gwaje-gwaje da duba girman cutar da kuma yawan mutanen da suka kamu.
Ya ce game da ƙaramar hukumar birni, a cewarsa, ba a bi duka hanyoyin da za su tabbatar da cutar ɓarkewa ta yi inda kuma ya yi kira ga jama'a da su yi watsi da rahoton saboda ba shi da isassun hujjojin da suka tabbatar da ɓarkewar cutar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama aƙalla ƴansintiri 10 da ake zargi da mummunan kisan malamin addinin musulunci a jihar Zamfara.
A ranar Talata ne aka yi wa malamin Sheikh Abubakar Hassan kisan gilla inda kuma ake zargin ƴansintiri da hannu a lamarin da ya faru a ƙaramar hukumar Gusau.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa waɗanda ake zargi da hukumomi suka kama ƴansintiri ne ba askarawan jihar da aka ƙaddamar ba a baya-bayan nan.
"Gwamnatin jihar Zamfara ta samu labarin mummunan kisan da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada. Abun takaici ne da za a iya hana faruwarsa.
"Jami'an tsaro sun kama duk ƴansintirin da ake zargi da hannu a wannan ƙazamin lamari. Muna son yin ƙarin bayani cewa ƴan sintirin da ake zargi da hannu a kisan ba su da wata alaƙa da askarawan jihar Zamfara." kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Gwamnatin ta ce sakamakon binciken farko daga ƴansanda ya nuna cewa ɗaya daga cikin ƴansintirin da aka kama tsohon ɗalibin malamin da aka kashe ne. Bayanin zai taimaka wa hukumomi su fahimci lamarin tare da ɗaukan matakan da suka kamata.
A cewar gwamnatin, za ta gabatar da sakamakon binciken ƴansanda da zarar an kammala.
Ta kuma miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan malamin da kuma al'ummar garin Mada.
Gwamnatin soji da ke mulki a Sudan ta ce za ta bari a shigar da kayan agaji ta Chadi da Sudan ta Kudu.
Gwamnatin ta haramta bi da kayan agaji ta Chadi inda ta zargi haɗaɗɗiyar daular larabawa, UAE da yin amfani da jerin gwanon motocin agaji da samar da makamai ga dakarun RSF. UAE dai ta musanta zargin yin hakan.
Clementine Nkweta-Salami, jami'ar MDD a Sudan ta ce matakin abin maraba ne kuma zai taimaka wajen isar da kayan agaji zuwa mutanen da ke tsananin buƙata.
Ms Salami ta ƙara da cewa gwamnati ta amince ta buɗe hanyoyin jirgi domin isar da kayan jin ƙai a Fasher da Kadugli da El Obeid.
Dubban mutane sun mutu, kusan miliyan takwas sun ɗaiɗaita a rikicin da aka shafe fiye da wata goma ana yi tsakanin dakarun da ba sa ga muciji da juna a Sudan.
Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya, WFP ya ce yaƙin na Sudan na iya ingiza mutane da dama cikin yunwa idan har ba a tsagaita yinsa ba.
Majalisar dokokin jihar Edo da ke kudancin Najeriya sun fara wani yunƙuri na tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu.
An sanar da hakan ne a zauren majalisar a ranar Laraba, inda bayanai ke nuna cewa yunƙurin ya samu goyon bayan ƴanmajalisa 21 a cikin 24 da ke majalisar.
A ranar Talata ne aka gabatar da wani ƙorafi kan mataimakin gwamnan, inda ake zarginsa da rantsuwa kan ƙarya da kuma bayyana wasu batutuwa na sirri na gwamnatin jihar.
Kafar watsa labarai ta Channels ta ambato shugaban masu rinjaye a majalisar na cewa yawan waɗanda suka goyi bayan tsige mataimakin gwamnan sun kai kashi biyu bisa uku da ake buƙata, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Inda kakakin majalisar, Blessing Agbebaku ya bai wa magatakardar majalisar ya miƙa takardar tsige Shaibu.
Dangantaka tsakanin gwamnan jihar, Godwin Obaseki da mataimakin nasa na ƙara tsami a baya-bayan nan.
A jamhuriyar Nijar, ƴansandar ƙasar sun kaddamar da wani samame na ba sani ba sabo kan mata da ƴan mata masu yawon dare.
Ofishin hukumar ƴansanda da ke ba da kariya ga mata da ƙananan yara ƙarƙashin jagorancin kwamishiniya Zouera Hassan Hausaize ne ya ƙaddamar samamen a kan titunan Yamai.
Hukumar ta ce ta kama tarin ƴanmata masu zaman kansu da ke tsayuwa a tituna da wasu wuraren shaƙatawa a birnin.
Inda ta koka kan yadda ƴanmatan ke bijire wa iyayensu. Ko da yake acewar shugabar hukumar suna samun waɗanda ke yin nadama bisa hakan.
"Mun kama yara mata akan fitar dare suna bin tituna suna neman maza - Idan mun kama su muka kwao su wajenmu muna yi musu faɗa mu ja musu kunne, mu nuna musu cewa wayan ba wurin zuwan yaro ba ne, idan ba za su yi karatu ba to su nemi sana'ar hannu." in ji ta
Shugabar ta kuma bayyana cewa: "Iyaye ke zuwa da kukansu sune cewa yaransu basa gane musu"
Wasu iya ye a birnin na Yamai sun koka kan yadda yara masu ƙarancin shekaru ke shiga wannan rayuwa ta yawon banza.
Hukumar ƴansanda na shirya irin wannan aiki lokaci-lokaci a tsarinta na yaƙi da miyagun ɗabi'u.
Wata kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya a Amurka ta yi watsi da wata ƙara wadda ake zargin manyan kamfanonin fasaha da hannu wajen yin amfani da yara don haƙar ma'adanin colbalt a jamhuriyyar dimokradiyyar Congo.
Ƙarar wadda aka sanya wa suna Apple, Microsoft, Tesla, kamfanin fasaha na Dell da kamfanin Alphabet mai Google.
A ranar Talata kotun ta yanke shawarar cewa sayen ma'adanin da kamfanonin ke yi ba yana nufin suna da hannu a tilasta wa yara aikin ƙwadago ba ne.
Mai shari'a Neomi Rao ta ce masu shigar da ƙara sun gaza nuna cewa kamfanonin da ake zargin suna da ikon kawo ƙarshen tilastawa yara ayyukan ƙwadago a wajen haƙo ma'adanan.
A shekarar 2019 ne wata ƙungiya kare hakkin bil'adama mai kare yara ma'aikata da waɗanda suka samu raunuka da ke aiki a mahaƙar ma'adanan colbalt a Congo da iyalan yaran da suka mutu a mahaƙar ta fara shigar da ƙarar.
Sai dai wata ƙaramar kotu ta yi watsi da ƙarar a shekarar 2021, abin da yasa suka ɗaukaka.
Ƙasar ta Congo ita ke samar da kashi 60 cikin ɗari na ma'adanin colbalt a duniya, ma'adanin da ke da muhimmancn gaske wajen sarrafa kayyakin lataroni.
Kuma aƙalla yara 25,000 ne ke aiki a mahakan ma'adanan colbalt a cikin mummunan yanayi, a cewa ma'aikatar ƙwadago ta Amurka.
Hukamar yaƙi da fasa ƙwauri ta Najeriya, Kwastam, ta ce tana jiran ta samu umarni daga gwamnatin Najeriya, kafin ta buɗe iyakar ƙasar da makwabciyarta Nijar.
Wannan shi ne karo na farko a hukumance da hukumar ta fito ta bayyana haka, duk da kiraye-kirayen da jama’a ke ta yi kan a bude kan iyakar.
Hukumar ta ce nan ba da wani lokaci mai tsawo ba ne ta ke sa ran za a buɗe bakin iyakar.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta yamma, ECOWAS ko CEDEO ta bayyana ɗage takunkuman da ta ɗorawa Nijar, lamarin da ya kai ga rufe bakin iyakokin ƙasashen ƙungiyar da Nijar na tsawon watanni.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan yulin 2023 ne Najeriya ta rufe iyakokinta da Nijar lamarin da ya haifar da ƙaruwar matsin rayuwa ga ƴan Najeriyar da kuma Nijar ɗin.
A halin yanzu akwai ɗaruruwan motocin dakon kaya ɗauke da kayan abinci da na masarufi da aka hanawa shiga Najeriyar.
Ƴankasuwar Najeriyar sun yi maraba da umarnin cire takunkumin da ECOWAS ta yi, sai dai kawo yanzu ba su samu shigo da kayan ba saboda ci-gaba da kasancewar bakin iyakar a rufe.
Masu shigar da kara a Spaniya na son a yankewa kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku.
Suna zarginsa da kaucewa biyan haraji na tsawon shekaru goma.
Ana zargin dan Italiya din da zambatar hukumomin Spaniya fiye da dala miliyan daya na harajin da yake samu daga hotunansa.
Ba a saka ranar soma shari'ar ba.
Ancelotti ya samu nasarori sosai a matsayinsa na mai horas da 'yan kwallo inda ya fi kowane koci lashe gasa a nahiyar Turai.
Amurka ta ce ta jefa ƙunshin abinci 36,000 ta jiragen sama a arewacin Gaza tare da haɗin guiwar ƙasar Jordan a ranar Talata.
Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan hukumar lafiya ta duniya ta ce yara suna mutuwa saboda yunwa a arewacin zirin, inda aƙalla Falasɗinawa 300,000 ke rayuwa ba tare da isasshen abinci da ruwan sha mai tsafta ba.
Sai dai tsarin yadda ake bayar da abincin ya janyo cece-ku-ce, inda ƙungiyoyin agaji ke cewa ba zai cimma ɓuƙatar da ake da ita ba, wanda kuma ke ci-gaba da ƙaruwa.
Haka kuma wata alama ce da ke nuna cewa an gaza wajen kai agajin ta ƙasa.
Manyan motoci ɗauke da kayan agaji na shiga kudancin Gaza daga Egypt ta Rafah da kuma Kerem Shalom da ke ƙarƙashin ikon Isra'ila a lokacin da Isra'ilar ke faɗa da Hamas.
Amma arewacin Gazan, kusan an yanke shi a ciki watannin baya-bayan nan, inda nan ne sojin Isra'ila suka fara kai farmaki ta ƙasa da kuma ta sama.
A ranar 20 ga watan Fabrairun, 2024, hukumar abinci ta duniya ta ce za ta dakatar da kai kayan agaji arewaci Gaza saboda tawagarta ta masu bayar da agajin gaggawa ta fuskar lafiya, sun fuskanci "yamutsi da tashin hankali saboda rashin doka da oda" abin da ya haɗa da mummunan wawa.
An kai agaji ta hanyar jefa kaya ta saman Gaza kimanin sau 20 a ƴan makonnin da suka wuce da haɗin guiwar Faransa a Haɗɗiyar daular Larabawa da sojin Isra'ila da Masar da Amurka da Jordan.
Wani mazaunin Gaza, Ismail Mokbel, ya gaya wa sashen larabci na BBC - kayan da aka jefa ta sama a ranar Juma'a sun ƙunshi wake da gyaɗa da dangoginsu da kuma wasu kayayyakin buƙatu na mata.
Wani mutum, Abu Youssef, ya ce bai samu komai ba bayan an jefa kayan agaji ta sama a kusa da asibitin al-Shifa a ke birnin Gaza.
Wani mazaunin zirin, Mista Mokbel ya ce " Gaza na buƙatar kawo agaji ta ƙasa da ta ruwa maimakon yadda ake yi, don hakan ba zai biya buƙata ga al'umma ba."