Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Habiba Adamu, Haruna Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba and Ahmad Tijjani Bawage

  1. Kar ku baiwa jami'an Najeriya cin hanci - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shaida wa masu zuba jari na ƙasar Qatar cewa su kai masa rahoton duk wani jami'in Najeriya da ya nemi a ba shi cin hanci.

    Tinubu ya bayyana hakan ne a wajen taron kasuwanci da zuba jari tsakanin ƴankasuwan Najeriyar da masu zuba jarin na Qatar, birnin Doha a ranar Lahadi.

    Inda ya bayyana wa taron cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke neman kawo tsaiko ko kashe guiwar masu zuba jari a Najeriya.

    "Na zo nan ne domin na baku tabbacin cewa muna yin garambawul. Duk wata matsala da wasunku suka fuskanta a baya, ya riga ya wuce, ba za ku gamu da irinta ba a nan gaba," in ji Tinubu.

    Inda ya ƙara da cewa "Kada ku bai wa kowa a cikin mutane na cin hanci, idan kuma har sun nema ko sun karɓa a hannunku, ku kawo ƙararsu wurina. za ku samu ganina."

    Tinubu ya kuma bayyana musu cewa kuɗadensu za su kasance cikin aminci, yana mai cewa gwamnatinsa ta ƙarfafa batun yaƙi da cin hanci da rashawa da yaƙi da rashin tsaro.

    Ministan masana'antu da kasuwanci na Qatar, Sheikh Mohammed bin Hamad bin Qassim Al Abdullah Al Thani, ya bayyana cewa ƙasarsa na sa ran yin amfani da damar da Najeriyar ta bayar, inda Qatar ɗin za ta fi bai fifiko sun haɗa da zuba sabbin jari a shirye-shiryen da suka shafi rage iska mai gurɓata muhalli da ma'adanai, sinadaran da ake samu daga ɗanyen mai, fannin masana'antu da kuma abubuwan ci.

    • Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu
    • Abin da rahoton Oronsaye ya ƙunsa, wanda Tinubu ya bayar da umarnin aiwatarwa
  2. An tsare kanal ɗin soji a Mali bayan wallafa littafi

    An tsare wani soji mai muƙamin kanal a Mali, bayan ya wallafa wani littafi da ke zargin rundunar sojin ƙasar da take haƙƙin fararen hula.

    A cikin littafin mai shafi 400 mai taken: Ƙalubalen ta'addanci a Afrika, kanal Alpha Yaya Sangaré, ya nuni da cewa ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun rubuta cewa: "Tun shekarar 2016 rundunar sojin ƙasar FDS ke take haƙƙoƙin mutanen da ake zargi suna cikin ƙungiyoyin ƴanta'adda."

    Inda ya ƙara da cewa jami'an sojin ne suka aikata hakan "da haɗin bakin manyansu."

    An cafke Mista Sangare da yammacin ranar Asabar, amma sai ranar Lahadi aka tabbatar da kama shi.

    A ranar juma'ar da ta gabata ma'aikatar tsaron ƙasar ta musanta zarge-zargen da aka yi a littafin, tana mai cewa maganganu ne marasa tushe."

    Ƙungiyoyin ƙasashen waje masu kare haƙƙin ɗan'adam sun sha zargin dakarun Mali da kashe fararen hula a yaƙin da take yi da masu tsattsauran ra'ayin Islama.

    • Rayuwa a biranen Mali da ƴan bindiga suka yi wa ƙawanya
    • Ana murnar cikar 'yan-tara shekara daya da haihuwa a Mali
  3. Sudan ta buƙaci a mayar da ita cikin AU kafin ta amince da shiga tsakanin ƙungiyar

    Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan ya ce ƙasar za ta amince da tayin da ƙungiyar tarayyar Afrika, AU ta yi na kawo ƙarshen rikici a ƙasar idan an mayar da ita cikin ƙungiyar.

    Ƙungiyar ta AU ta dakatar da Sudan ɗin ne bayan da sojoji suka karɓe mulki a watan Oktobar 2021.

    A ranar Lahadi ne janar Burhan ya gana da tawagar da ƙungiyar AU ta kafa domin kawo ƙarshen rikin da ke faruwa a ƙasar, wadda Mohamed Ibn Chambas ke jagoranta.

    Tawagar mai mambobi uku zata shiga tsakanin wajen tattaunawa da maido da ƙasar kan turbar dimokradiyya, inda zata yi aiki da masu ruwa da tsaki ƴanSudan na cikin gida da waje domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

    A wata sanarwa da janar Burhan ya wallafa a shafinsa na Facebook ya bayyana ƙwarin guiwa kan ƙungiyar ta AU da yiwuwar kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a ƙasar, amma ya nemi a mayar da Sudan cikin AU ta zama cikakkiyar mamba.

    • 'An mayar da mata tamkar ganimar yaƙi a Sudan'
    • 'Sai mun sayar da rai muke zuwa binne matattu a Sudan'
  4. Kamala Harris ta nemi a tsagaita wuta a Gaza

    Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce mutanen Gaza "na cikin yunwa" inda ta buƙaci Isra'ila ta "ƙara yawan kayayyakin agajin da take bari a shiga da su" zirin gaza.

    Ta ce "dole a tsagaita wuta na aƙalla makonni shida" wanda a sa'ilin nan "za a iya fitar da duka ƴan Isra'ilar da ake garkuwa da su."

    Tun da farko, Isra'ila bata halarci taron tsagaita wutar da aka kira a Masar ba, tana mai cewa Hamas bata bayar da jerin sunayen waɗanda take garkuwa da su da har yanzu suke da rai ba.

    Hamas ta shaida wa BBC cewa ba ta samu damar yin hakan ba saboda ruwan bama-baman da Isra'ila.

    "A zahiri da wuya mu gane waye ke da rai har yanzu," a cewar Dr Basem Naim, wani babban jami'in ƙungiyar.

    Bayanai na nuna cewa tawagar Hamas da kuma masu shiga tsakani na Amurka da Qatar sun isa Alƙahira domin fara tattaunawa.

    Ana ƙara matsin lamba don cimma tsagaita wuta, tun bayan al'amarin da ya auku a ranar Alhamis, inda aka kashe Falasɗinawa 112 a wajen birnin Gaza ta arewaci, bayan sunyi cuncurundo domin karɓar kayan agaji, inda sojin Isra'ila suka buɗe musu wuta.

    • Biden na fuskantar ƙarin bijirewa a cikin gida kan yaƙin Isra'ila a Gaza
    • Dole a bar Falasɗinawa su zauna a Gaza - Blinken
  5. Za mu tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abinci - NEMA

    Hukumar kai ɗaukin gaggawa ta Najeiya (Nema) ta ce za ta tsaurar tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin Najeriya domin kare su daga 'ɓata-gari’

    Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan wani daga cikin rumbunanta da ke Abuja, babban birnin ƙasar a ranar Lahadi.

    Wasu matasa ne ake zargin sun kai farmaki kan rumbun wanda ke unguwar Gwagwa da ke birnin na Abuja, inda suka yi awon-gaba da kayan abinci da kuma sauran abubuwan da aka taskace a rmbun.

    Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NEMA, Manzo Ezekiel, ta ce "Shugaban hukumar na ƙasa, Mustapha Ahmed ya bayar da umarnin a tsaurara tsaro a ofososhi da kuma rumbunan ajiye kayan hukumar a faɗin Najeriya domin kauce wa kutsawa cikin su."

    Najeriya dai na fama da matsi na tattalin arziƙi, inda mutane da dama ke kokawa kan rashin abinci da tsadar kayan masarufi.

    Kafin fasa rumbun ajiye abincin a Abuja, an samu rahotannin yadda mutane suka far wa motocin dakon kayan abinci tare da yin wawason abin da suke ɗauke da shi a wasu sassan ƙasar.

    Ko a makon da ya gabata kungiyar ƙwadago ta ƙasar (NLC) ta gudanar da wata zanga-zangar yini ɗaya a ƙasar domin matsa wa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakan da suka dace wajen kawo sauƙi ga matsalar rayuwa da al'umma ke ciki.

    Gwamnatin ƙasar dai ta ce ta fito da tsarin raba kayan tallafi ga al'umma da kuma bai wa masu ƙaramin ƙarfi tallafin kuɗaɗe.

  6. Ƴar Ghana ta gaza kafa tarihin girkin abinci na Guinness

    Kundin tarihi na Guinness ya yi watsi da yunƙuri da wata ƴarƙasar Ghana ta yi na kafa wani sabon tarihi na wadda ta ɗauki lokaci mafi tsawo tana girki a duniya, a cewar tawagarta.

    A watan Janairun da ya wuce ne Failatu Abdul-Razaƙ ta nuna cewa ta kafa sabon tarihi na kwashe sa'oi 227 tana ɗora sanwa.

    Ɗaya daga cikin jami'an da ke taimaka wa Failatu, Kafui Dey, a ranar Lahadi a ce yunƙurin nata na kafa tarihi bai yi nasara ba,"ta gaza cimma wasu tsaurarn matakan da kundin ya shimfiɗa."

    "A wata sanarwar da masu lura da kundin suka fitar, ta nuna cewa matar ta karya dokokin wutu, hakan ya sa ta kasa cin nasara."

    Ƴunƙurn kafa tarihin ya jefa ƴanƙasar Ghana cikin farin ciki da annashuwa.

    iki har da ƴansiyasa, inda mataimakin shugaban ƙasar, Mahamudu Bawumia da mashahuran mutane da dakarun sojin ƙasar sun bayyana goyon bayansu a gare ta a lokacin da take girkin.

    Sai dai duk a rashin nasarar da ta yi, mai dafa abincin ta gode wa magya bayanta.

    • Hoton mai tsire a Kashmir ya lashe gasar hotunan abinci ta duniya a 2022
    • Ka san sirrin samun rayuwa mai tsawo? Cin abinci kadan
  7. Ƴansanda sun kama waɗanda suka fasa rumbun abinci a Abuja

    Rundunar ƴansanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta kama wasu mutane 15 da ake zargi da hannu wajen fasa rumbun adana abinci a birnin.

    Wasu matasa ne suka fasa rumbun ajiya kayan abincin na hukumar kai gajin gaggagawa ta ƙasar, a yankin Gwagwa.

    Bayanai sun nuna cewa matasa sun yi wa rumbun ƙarƙaf, ko da yake ƴansandan sun ce sun kwata buhu 26 na masarar da ake zargin an kwashe.

    Ƴansandan sun kuma ce sun kwato babura biyar daga mtanen da aka cafke.

    A ƙarshen mako ne wasu matasa suka daka wa wata babbar mota mai ɗauke da taliya wawa, kuma har yanzu babu rahoton kama wani.

    matalar fasa rumbun abinci ko motocin da ke ɗauke da kayn abinci, batu ne da ke c gaba da faruwa a sassan ƙasar daban-daban.

    Miliyoyin ƴanƙasar ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci, lamarin da ya jefa da dama cikin halin yunwa da ƙarancin abinci.

    Tun bayan janye tallafin mai a watn Mayun da ya gabata ne, farashin kayyayaki, musamman na abinci suka yi tashin gwauro zabi a ƙasar.

  8. Nikki Haley ta kayar da Trump a zaben fitar da gwani a Washington

    'Yar takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Republican, Nikki Haley, ta yi nasara a zaben fidda gwani, sai dai dole ta yi nasara kan daukacin wakilan jam'iyyarta a gundumar birnin Washington DC.

    Mis Haley ta ce ba ta yi mamakin zabarta da 'yan Republican suka yi ba, da watsi da tsohon shugaban kasar Donald Trump da tada kurar da ya yi.

    Har yanzu Mr Trump ne ke sahun gaba a zaben fidda gwanin jam'iyyarsu, ana kuma sa ran zai samu karin wakilan da za su mara masa baya cikin makon da sauran jihohi za su zabi gwaninsu.

  9. Barka da warhaka!

    Da fatan za ku kasance tare da mu a tsawon wannan yini inda za mu kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya.

    Kada ku manta za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, twitter da instagram.